■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Daga cikin misdakan sharri da Ashararai
Hakika mun ambaci cewa sharri da alheri kishiyoyin juna biyu ne kuma dama ana sanin abubuwa tare da kishiyoyinsu, duk wanda ya san alheri zai san sharri, sai dai cewa cikin ayoyi da riwayoyi akwai isharori kan ambaton ba'arin misdakan alheri da sharri, ina kaunar yin ishara zuwa garesu ko da atakaice ne tare da cire isnadan hadisan daga A'imma ma'asumai (a.s).
Allah ta'ala cikin littafinsa mai daraja mai girma ya ce:
1 ـ (إِنَّ شَرَّ الدَّوَابَّ عِندَ اللّهِ الصُّمُّ الْبُكْمُ الَّذِينَ لاَ يَعْقِلُونَ)[1] .
Lallai mafi sharrin cikin dabbobi a wurin Allah shi ne Kurama Bebaye wadanda basa sa aiki da hankali.
2 ـ (إِنَّ شَرَّ الدَّوَابِّ عِندَ اللّهِ الَّذِينَ كَفَرُواْ فَهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ)[2] .
Lallai mafi sharrin dabbobi a wurin Allah sune wadanda suka Kafirce alhalin su basa Imani.
Dabbobi jam'ine na Kalmar Dabba, ma'ana halittar da take tattaka kasa shi yasa ake kiran mutum da sunan lallai tattaki a doran kasa yana daga gammamiya siffarsa d atake bijira gare shi, ta yiwa an amabace da wannan suna cikin ayoyin guda biyu domin ishara zuwa ga wadanda basa aiki da hankali basa imani, su hakikaninsu hukuncinsu daya da dabbobi bari ma sunfi dabbobi bata.
Amma misdakin sharri da bayaninsa cikin hadisai masu daraja shi ne kamar yanda zai zo a kasa:
1-hakika mafi sharrin cikin mutane a wurin Allah shi ne Limami Ja'iri batacce mai batarwa. 2- da kuma wanda ya sayar da lahirarsa don duniya, mafi sharri daga gare shi shi ne wanda ya sayar da lahirarsa da duniyar waninsa. 3- da wadanda mutane suke girmama su saboda tsoron sharrinsu.4- da wanda yake zaluntar mutane.5-wanda yakewa mutane algus.6 wanda baya karbar uzuri da wanda baya zobaitar da laifi.7wanda baya damuwa da mutane su dauke shi mai munanawa aiki.8 da wanda baya godewa ni'ima baya kiyaye alfarma.9 da wanda yake kokarin hada rigima tsakanin `yan'uwa yana mantar da kyautatawa.10 da wanda ba a fatan alherinsa ba aminta daga sharrinsa.11 da wanda baya cika amana baya nesantar ha'inci.12 da wanda baya afuwa ga tuntube baya suturce tsiraici.13 da wanda baya taimakon wanda aka zalunta.14 wanda yake taimakon Azzalumai.15 da mai bibiyar aibobi min mutane amma kuma yana makanta daga aibobinsa.16 da me neman halaka ga mutane.17 wanda yake tsoran mutane cikin ubangijinsa baya tsoran ubangijinsa cikin mutane.18 da wanda baya yarda da kowa sakamakon munana zatonsa, babu wanda yake yarda da shi sabida munnanar ayyukansa 19da wanda yake gani yafi kowa 20da mai dogon buri da munana aiki 21 wanda ya sakawa alheri da mummuna. 22 mafi sharrin mutane shi ne Fasikin da ya karanta littafin Allah ya samu fahimta cikin addinin Allah, sannan ya sadaukar da kansa ga Fajiri, idan yayi nishadi sai yayi kakaci da karatunsa da tattaunawa da shi, Allah sai ya kafa hijabi kan zuciyar mai fadi da mai sauraro.23 da wanda yake kai dan'uwansa wurin Sarki dmin cutar da shi, sai ya halaka kansa da dan'uwansa ya kuma halakar da Sarki, sunansa wanda ya halakar da mutane uku. 24 amfi sharrin mutane a wurin Allah a ranar lahira shi ne mai fuska biyu Munafuki.25 da kuma lalatattun Malamai. 26 Ashararan Mutane sune Ashararan malamai cikin mutane. 27 da malamin da baya amfana da iliminsa.28 da Fajiri tsagera da yake karanta Kur'ani baya kiyaye komai daga gare shi.29 da wanda ya halakar da lahirarsa da duniyar waninsa.30 suna sayen mutane da sayar da su.31 da wanda ake kyamar zama da shi sakamakon alfasharsa.32 da wadanda idan aka ya azurta su sai suyi rowa idan kuma aka hana su sai su aibata da zagi. 33 da wanda yake da saurin fushi da jinkirin yarda.34 da Attajirai maha'inta.35 da mai yawan kage kan mutane da yi musu karya da kage.36 da mai keta iyakokin Allah. 37 mai fadin alfasha da miyagun kalamai.38 da marowaci mai ci shi kadai sakamakon munanar dabi'arsa.39 mai hana alherinsa da kyautarsa.40 mai dukan bawansa da wanda yake karkashinsa.41 mai dora hidimar iyalinsa kan waninsa, baya sauke nauyin da yake kansa daga iyalinsa.42 da masu yada annamimanci.43 da masu raba kan masoya.44 da masu neman aibobin wadanda suke barranta daga aibobi.45 mafi sharri daga sharri shi ne azabar da take bayansa, sannan mafi alheri daga alheri ladan da yake biyo bayansa. 46 mai aikata sharri yafi sharri daga sharri.47 mafi sharrin Aklak din nufus shi ne danniya da zalunci.48 mafi sharri abin da yake tatare da mutum sune: rowa mai tsoratarwa da ragwanci mai gurbatarwa.49 matattarar sharri na dunkule cikin abotaka da mugun aboki.50 da cikin ruduwa da jinkiri da dogara da aikin da kayi.51 da jayayya da yawan musu. 52 Shaidan ya gaya `yan'uwansa Shaidanu daga mutane ku rungumi nama da giya da mata, banga abin da ya tattaroi sharri ba misalinsu.53 mafi sharrin riwaya riwayar karya.54 mafi sharri al'amura kagaggunsu.55 mafi sharrin makanta itace makantar zuciya.56 mafi sharri nadama itace namadar ranar lahira.57 mafi sharrin aikin da aka tsiwirwira shi ne riya.58 mafi abinci shi ne cin dukiyar marayu da zalunci.59 fushi shi ne mabaudin dukkanin sharri.60 lallai Allah Azza wa Jallaya sanyawa sharri wasu ayyuka ya kuma sanya giya matsayin makullin dukkanin kwadon wannan ayyuka, karya ta fi giya sharri. 61 abubuwa da suke haifar da sharri sune: karya, rowa,zalunci, jahilci.
Wadannan wani adadi ne daga misdakan sharri kamar yanda ya zo a riwayoyi daga Manzon Allah (s.a.w) da mutanen gidansa tsarkaka, wani dan kanface ne daga Kogi, duk mai son saninsu baki daya to lallai sun ninninka wadannan da muka kawo. Muna rokon Allah matsarkaki da ya karemu daga sharri da Ashararan mutane da Fajirai, da sharrin kawukanmu da iyalanmu da duk wanda yake tare da mu, lallai sharri na iya zuwa daga makusanci ya gaza zuwa daga na nesa damu, wurin Allah muke kai kuka daga gare shi muke neman taimako, babu tsimi babu dabara sai da Allah madaukaki mai girma.