■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Kulli tashkiki shi ne abin da yake sassabawa cikin mikar martabobinsa da fadinsu cikin karfi da rauni, ko kuma cikin cancantuwa , ko gabata da jinkirta, kamar samuwa da haske, shi haske da ke iya gani shi ne mai bayyanar da kansa da waninsa, sannan sassabawar martabobi cikin karfi da rauni, nisan rata da martaba nawa ne tsakanin hasken rana da hasken kyandir? Haka tsakanin alheri da sharri.
قال رسول الله 6لمعاذ: «ألا أُنبّئک بشر النّاس؟! قال : بلى . قال : من أكل وحده ، ومنع رفده ، وسافر وحده ، وضرب عبده ، ألا أُنبّئک بشر من هذا؟!: من يبغض النّاس ويبغضونه ، ألا أُنبّئک بشر من هذا؟!: من يُخشى شرّه ولا يُرجى خيره ، الا أُنبّئک بشر من هذا؟!: من باع آخرته بدنيا غيره . ألا أُنبّئک بشرٍ من هذا؟!: من أكل الدنيا بالدين».
وفي خبر آخر: «لا يقيل عثرة ، ولا يقبل معذرة ، ولا يغفر ذنباً، ثمّ قال : ألا أُنبّئكم بشر من هذا؟ قالوا: بلى يا رسول الله، قال : من لا يؤمن شرّه ولا يُرجى خيره».
Manzon Allah (s.a.w) ya cewa Mu'azu: bana baka labarin mafi sharrin mutane ba?! Ya ce: ka bani labari. Ya ce: shi ne wanda ya ci shi kadai yayi rowar kyautarsa, yayi tafiya shi kadai, ya bugi bawansa, kana son ian baka labarin wanda yafi wannan sharri?! Shi ne wanda yake gaba da mutane suma suke gaba da shi, yanzu bana baka labarin wanda yafi wannan sharri ba?! Shi ne wanda ya sayar da lahirarsa da duniyar waninsa. Kana so na baka labarin wanda yafi wannan sharri?! Shi ne wanda ya ci duniya da addini.
Ya zo a wani hadisin daban: shi ne wanda baya zobaitar da tuntube, baya karbar uzuri, baya yafe laifi, sannan ya ce:kuna son na baku labarin wanda yafi shi sharri?! Sukace eh muna so ya Manzon Allah. Ya ce shi ne wanda ba a amintuwa daga sharrinsa ba a fatan alherinsa.
Daga cikin hadisai masu daraja da jan hankali wadanda suka tattaro magana cikin sanin sharri:
1 ـ قال رسول الله 6: «من وقي شر ثلاث ، فقد وقي الشرّ كلّه : لقلقه وقبقبه وذبذبه . فلقلقه لسانه ، وقبقبه بطنه ، وذبذبه فرجه».
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk mutumin da ya tsira daga sharrin abubuwa uku hakika ya tsira daga dukkanin sharri: lakalakarsa da kabkabarsa da zabzabarsa, daga sautin da yake fita daga harshensa daga magana, da kuma kugin cikinsa, daga dawurwrurar farjinsa.
2 ـ وقال 6: «ان كان الشرّ في شيء، ففي اللّسان».
Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: idan ma sharri ya kasance a cikin wani abu to tabbas cikin harshe ne.
3 ـ قال أمير المؤمنين 7: «أخّر الشرّ، فإنّک إذا شئت تعجّلته».
Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: ka jinkirta sharri lallai idan da kaso zaka gaggauta shi.
4 ـ وقال 6: «من أضمر الشرّ لغيره ، فقد بدأ به نفسه ـ أي يبدأ بالشرّ بنفسه أوّلاً، لانّ إضمار الشرّ شرّ».
A wani wajen ya ce: duk wanda ya boye sharrin waninsa, hakika ya fara da sharrin kansa, sabida boye sharri shima sharri ne.
5 ـ وقال 6: «إيّاک وملابسة الشرّ، فإنّک تنيله نفسک قبل عدوک .
Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: kada ka rigantu da sharri, lallai zaka fara da kanka ne kafin makiyinka, wannan duka cikin makiyi fa kenan ya yake cikin aboki zaka halaka addininka da shi gabanin kai shi ga waninka, ma'ana kada kayi fatan sharri hatta a kan makiyanka.
6 ـ قال 6: «متقى الشرّ ـ أي يمتنع عن الشرّ بتقيّة ـ كفاعل الشرّ».
Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: mai gudun sharri daidai yake da mai aikata shi.
7 ـ وقال 6: «رُدّوا الحجر من حيث جاء، فإنّ الشرّ لا يدفعه إلّا الشرّ
Aminci ya tabbata a gare shi ya ce: ka mayar da dutse daga inda ya zo, lallai shi sharri babu abin da yake tunkude shi sai sharri.
8 ـ قال الإمام الحسين 6: «مجالسة أهل الدناءة شرّ ـ فلا تجالس من كان دني النفس ، وكان من الأراذل والأوباش فانّ في معاشرتهم ومجالستهم يصيبک الشرّ وينقص من شأنک».
Imam Husaini (a.s) ya ce: zama da ma'abota kazanta sharri ne-kada ka zauna da wanda yake mutumin banza da ya kasance daga `yan tasha lallai zama da misalinsu zai jawo maka sharri da zubar mutuncinka.
9 ـ قال الإمام الباقر 6: «كن خيراً لا شرّ معه ، ورقاً لا شوک معه ، ولا تكن شوكاً لا ورق معه وشرّاً لا خير فيه».
Imam Bakir (a.s) ya ce: ka zama alherin da babu sharri cikinsa, ka zama taushi da babu kayar da take tare da shi, kada ka kasance kayar da babu taushi tare da ita sharri da babu alheri cikinsa.
Wannan duka kadan ne daga ciki Kogi cikin sanin sharri da misdakansa haka alheri da misdakansa, muna fatan ya kasance taku na farko da farwa cikin tafiya mai nisan Mil dubu cikin wannan al'amari mai hatsari maudu'i mai wahala.
Zan hattama maganata da fadin Annabinmu mai ceton zunubanmu likitan zukatanmu Manzon Allah masoyinsa Muhammad (s.a.w) hakika ya ce:
«أطلبوا الخير دهركم واهربوا من النّار جهدكم فإنّ الجنّة لا ينام طالبها، وان النّار لا ينام هاربها».
Ku nemi alherin zamaninku ku gujewa wuta bakin ikonku lallai mai bacci baya samun Aljanna, lallai mai gudun wuta baya bacci.
Allah matsarkaki ya ce:
(فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْراً يَرَهُ * وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرّاً يَرَهُ)[1] .
Duk
wanda yayi wani aiki daga alheri gwargwadon kwayar zarra zai ganshi* duk wanda
yayi aiki daga sharri gwargwadon kwayar zarra zai ganshi.