■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Hakika zantukan Sarkin Muminai lallai jagaban zantuka ne, lallai yana daga faifaice zance, me yafi yawan hikomomi da ma'arifofi cikin zantukan Sarkin Muminaiu Ali (a.s) cikin zanensa mai cike da balaga da kalamansa na fasaha, hakan ya sanya ni na kaunaci kwankwasa kofofin Nahajul Blaga domin mu yi kiwo mu dan shakata cikin lambunansa masu yalwa, mu tsinka daga kayan marmarin cikinsu ababen dasa daga alheri da sharri, zan takaita da kawo misalai da samfuri da shaidu ba tare da yin sharhi ba da bayani ko ta'aliki, ina mai mayar da hakan zuwa ga mai karatu da wayewarsa da basirarsa cikin iliminsa.
قال 7: «إمّا داعي الله فما عند الله خير له . ولسان الصدق يجعله الله للمرء في النّاس خير له من المال يرثه غيره»[1] .
Sarkin Muminai (a.s) ya ce: ko dai mai kiran Allah lallai abin da yake wurin Allah shi ne mafi alheri gare shi, lallai harshe mai fadi gaskiya da Allah yake sanya shi ga mutum cikin mutane shi ne mafi alheri gare shi daga dukiyar da yake gadonta daga waninsa.
Hakika mutane suna gadar da dukiya ga yayansu kamar suke gadar da kyawawan ambatonsu ga mutane da alheri daga abin da suka aikata daga alheri cikin rayuwarsu kuma daga addu'ar Ibrahim (ka sanya mini harshe mai gaskiya cikin sauran mutane) ma'ana mutane bayan mutuwata da fakuwata su dinga ambatona da gaskiya da alheri da yabo, wannan shi ne mafi alherin gado lallai shi ne mafi falala ba zaq a a iya hada shi da dukiya ba wacce waninsa yake gada daga gare shi.
وقال 7: «ملكتني عيني وأنا جالس ، فسنح لي رسول الله 6، فقلت : يا رسول الله، ماذا لقيت من أُمّتک من الأود واللّدد؟ فقال : ادع عليهم ، فقلت : أبدلني الله بهم خيراً منهم ، وأبدلهم بي شرّاً لهم منّي»[2] .
A wani wajen ya ce: bacci ya daukeni idan zaune, sai nayi mafarki da Manzon Allah (s.a.w) na ce masa ya Manzon Allah, me nake haduwa da shi daga al'ummarka daga karkacewa da jayayya? Sai ya ce ka yi addu'a a kansu, sai nace Allah ya canja mini da mafi alheri daga garesu, Allah ya canja musu daga mafi sharri daga gareni a kansu.
وقال 7: «فاتقوا شرار النّساء، وكونوا من خيارهن على حذر»[3] .
Kuji tsoran mafi sharrin mata, kuma ku kasance cikin taka tsantsan daga na kirkinsu.
«أمّا ـ وشرّ القول الكذب ـ انه ليقول فيكذب ، ويعد فيخلف»[4] .
Amma-mafi sharri zance shi ne karya, lallai shi ne yana magana sai ya fadi karya, yayi alkawari ya saba
وقال : «لا يدع للخير غاية إلّا أُمّها»[5] .
Ya ce: babu mai addu'a ga alheri matukar addu'a sai mahaifiyarsa.
«فاستودعهم في أفضل مستودع ، وأقرّهم في خير مستقر، تناسختهم عترته خيرُ العِتر، أُسرته خير الأُسر، وشجرته خير الشجر»[6] .
Sai ya bada ajiyarsu cikin mafi falalar ma'ajiya, ya tabbatar da su cikin mafi alherin matabbata, sannan mafi alherin tsatsonsa suka bibiye su da danginsa mafi alherin dangi, da bishiyarsa mafi alherin bishiya.
«اللّهم اقسم له قسماً من عدلک ، واجزه مضعّفات الخير من فضلک»[7] .
Allah ka kaddara masa wani yanki daga adalcinka, ka saka masa da ninki ba ninki alheri daga falalarka.
«ثمّ أنتم شرار النّاس ، ومن رمى به الشيطان مراميه ، وضرب به تيهه ، وسيهلک فيّ صنفان : محبّ مفرط يذهب به الحبّ إلى غير الحق ، ومبغض مفرط يذهب به البغض إلى غير الحق ، وخير النّاس فيّ حالاً النمط الأوسط فألزموه ، والزموا السّواد الأعظم ، فإنّ يد الله مع الجماعة وإيّاكم والفرقة»[8] .
Sannan kune mafi sharrin mutane, wadanda Shaidani yayi jifa da su zuwa karan bararsa, yayi bugu da shi cikin dimautarsa, lallai mutane biyu zasu halaka cikina: masoyi mai wuce iyaka soyayya tana fitar da shi daga gaskiya, da kuma Makiyi mai wuce iyaka cikin kiyayya tana kai shi wajen gaskiya, mafi kyawun hali cikin mutane shi ne tsakatsaki ku lazimce shi, ku lazimci gayya mafi yawa, lallai hannun Allah yana tare da jama'a ku guji rarrabuwar kai
«وقد
أصبحتم في زمن لا يزداد الخير فيه إلّا أدباراً، ولا الشرّ فيه إلّا
إقبالاً أين أخياركم وصلحا 9.
Hakika kun wayi gari cikin wani zamani alheri bai karuw ada komai sai ci baya, sharri yana ta karuwa yana fuskantowa ina mutanen kirkin cikinku da Salihai.
Ina cewa: Shugabana majibanci lamarina idan har a zamaninka haka lamarin ya kasance?! To yaya zamaninmu kenan?! Sai dai cewa abin yake ragewa wutar zafi shi ne kara samun fatan jiran yayewa da daular `danku Mahadi mai kawo gyara cikin baki dayan duniya da hukumarsa ta adalci cikin fadin duniya zai zo ya cika duniya da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya, ya Allah ka gaggauta bayyanarsa da zuwansa cikin nasara da lafiya, da bayyanar al'amari sannan ka sanya mu daga masu tsarkin niyyar cikin mabiyansa da mataimakansa wadanda zasu samu shahada ta hanyarsa.
«وليس لواضع المعروف في غير حقّه ، وعند غير أهله ، من الحظ فيما أتى إلّا محمدةَ اللئام وثناء الأشرار»[10] .
Wanda ya ajiye kyautata a muhallin da bana ta ba wurin mutanen da ba Ahalinta ba lallai bai da komai cikin abin da yayi sai godiya daga mutanen banza da yabawar Ashararai.
Wannan na daga cikin kyawawan hadisai masu daraja lallai idan ka ajiyae kyautatawarka da alherinka a wurin mutanen da ba Ahalinsa ba zaka girbi mummunan sakamako, lallai mutum mai hankali mai hikima Adali yana ajiye komai a muhallin da ya dace da shi.
وقال 7: «ان الله يبتلي عباده عند الأعمال السيئة بنقص الثمرات ، وحبس البركات ، وإغلاق خزائن الخيرات ، ليتوب تائب ، ويقلع مقلع ، ويتذكّر متذكّر، ويزدجر مزدجر»[11] .
Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: hakika Allah yana jarrabbar bawansa da miyagun ayyuka da tawayar kayan marmari, da daure albarkoki, da rufe taskokin alherai, domin mai tuba ya tuba, mai kwabuwa ya kwabu, mai tunatuwa ya tunatu, mai hanuwa ya hanu.
«شر الإخوان من تُكلّف له »[12] .
Mafi sharrin yan'uwa wanda ya zama nauyi kan mutane.
«لا خير من شيء من أزوادها إلّا التقوى »[13] .
Babu alheri daga wani daga guzurinta face tsoran Allah
فإنّ خير الزاد في الدنيا والآخرة التقوى .
Hakika mafi alherin guzuri a duniya da lahira shi ne tsoran Allah.
Tsira da amincin Allah ya tabbata a gareka ya shugabana ya Sarkin Muminai har Abadan abiding.