Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci - CIKIN HALLARAR ALHERI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci

Daga cikin ingantattun hadisai kyawawa cikin bayanin hakikanin hankali da yaya aka halicce shi akwai abin da ya zo cikin hadisi daga Imam Musa Alkazim (a.s) lokacin d ayake bayanin hankali da ma'abotansa cikin wani hadisi da yayi bayani filla-filla tare da Hisham da yake daga Sahabbansa yana mai cewa:

Hisham ka fara sanin hankali da rundunoninsa ka san jahilci da rundunoninsa zaka kasance daga masu shiriya, Hisham ya ce sai nace: babu abin da muka sani sai abin da ka sanar damu, sai ya ce: ya Hisham hakika Allah ya halicci hankali shi ne farkon abin da ya halitta daga Ruhaniyyun ma'ana abubuwa marasa jiki daga fadinsa kasance sai ya kasance lallai shi yana daga duniyar umarni daga bangaren daman Al'arshi daga haskensa  lallai Allah matsarkaki shi ne hasken sammai da kassai misalin haskensa kamar misalin Alkuki cikinta an ajiye fitila, sai Allah ya cewa da hankali juya baya sai ya juya sannan ya ce masa taho sai ya taho, hankali ya kasance mai biyayya cikin umarni da hani cikin gabata da juyawa, sai Allah Azza wa Jalla ya ce: na halicceka wata halitta mai girma na girmamaka kan dukkanin halittuna-lallai Allah ya girmama dan Adam sakamakon abin da yake tare da shi daga wannan hankali mai girma.

Shi aiki da hankali na daga girmamawar Allah matsarkaki, sannan Allah ya halicci jahilci daga tafkin duhu, ya ce masa: juya sai ya juya sannan ya ce masa gabato sai yaki gabatowa, sai ya ce: shin kayi girman kai ne? sai Allah ya la'ance shi ya koreshi daga rahamarsa da jin kansa kebantacce ga Muminai masu kyautata masu biyayya musulmai masu sallamawa cikin gabata da juyawa sune ma'abota hankali da gaske, lallai shi hankali shi ne abin da aka bautawa Allah da shi da aka samu Aljanna da shi.

Sannan ya sanyawa hankali sojoji 75, lokacin da jahilci ya ga girmamawa da aka baiwa hankali sai ya fara kullatarsa da kiyayya-daga nan kiyayya tsakanin hankali da jahilci ta fara lallai su mutane suna kiyayya da abin da suka jahilta, adawa tsakanin Shaidan da mutum ta kullu, kishiyantar juna tsakanin haske da duhu da kullu,  hakama tsakanin gaskiya da karya da tsakanin alheri da sharri, sai jahilci ya ce: ya ubangiji ai wannan shima halitta ce misalina ka halicceshi da karrama shi ka karfafa shi, ni ina kishiyarsa ne bani da karfi kansa, nima ka bani daga Sojoji misalin abin da ka bashi mana, sai Allah matsarkaki madaukaki ya ce: na'am-sabida Allah matsarkaki Adali ne daga cikin adalcinsa sai ya baiwa jahilci abin da ya bawa hankali sai dai cewa ya sanya masa sharadi ya ce: idan ka saba mini bayan haka zan fitar da kai da sojojinka daga kusa dani daga rahamata, sai ya ce: na yarda, sai aka yi yarjejeniya tsakanin ubangiji da jahilci da ji da kai da cewa shi yana kusa da ubangijinsa da cikin rahamarsa sai dai cewa sojojin hankali sun rigaye shi shiga ciki.

Wannan na nuni kan halittar mutum lafiyayya da cewa ita fa tana karkata zuwa ga hankali da rundunarsa zuwa ga dayanta Allah matsarkaki, sai dai cewa muhallin da mutanen da mutum yake rayuwa cikinsu da gurbatacciyar tarbiyar da yake samu daga iyaye da makaranta da Abokai suna karkatar da shi da canja masa hanya da zabar hanyar sharri da jahilci da rundunarsa, koma dai ya ta kasance, lallai Allah ya baiwa hankali rundunar sojoji 75 kamar yanda shima jahilci ya bashi wannan adadi domin karfi ya zo daidaita tsakaninsu cikin gwabzawa domin adalcin Allah yayi tajalli, sannan shi kowanne Sarki yana da waziri shi ne wanda yake daukar nauyin umarni hankali da zartar da shi kamar yanda wannan shi ne al'adar sarakuna da waziransu, sai Allah ya sanya alheri wazirin hankali, wannan na nufin mukami na biyu cikin hukumar hankali shi ne alheri shi ne wanda yake jibantar lura da rundunar hankali, duk wand ayake da alheri ana fatan daula ta kasance daga gare shi a hannun rundunar hankali sai a samu kyawawan dabi'u da falolinsu suna jan ragamar jama'a, kamar yanda sharri yake wazirin jahilci, lallai jahilci yana samun taimako daga rundunarsa cikin gwabzawarsa da hankali, sai amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: daga cikin abin da aka baiwa hankali daga runduna mai dauke da sojoji 75, alheri shi ne wazirinsa , sannan sharri shi ne wazirin jahilci.