sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
  • Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
  • Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
  • MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
  • Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
  • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
  • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
  • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
  • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
  • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
  • Shahadar Fatima Azzahra A.S
  • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
  • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
  • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
  • sababun labare

    Labarun da ba tsammani

    Muna taya ku murnar zagayowar shekarar haihuwar imam Rida (AS)

    Da sunan Allah me rahama me jin kai 

    Tsarkakakkiyar zuciya cikin sirrin ziyarar imam irida- da Alqalamin  sayyid adil alawi. 

    Haramin imam irada gonace daga gonannakin Aljannan 

    Aljannan gidan hutune ga dukkanin muminai maza da mata bayan tashin alqiyama, rai takan samu dukkanin abun da take bukata, ba me shiganta sai wanda ke da wadatan zuci (وَأمَّا الَّذِينَ سعدُوا فَفِي الجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا)

    Allah subahanahu wata’ala cikin ludufin sa da kuma karamcin sa ya sanya gona cikin duniyannan daga cikin gonannakin Aljannan wanda an yi alkawarin ta ga masu taqawa. Da Allah zai bude idanun mutane da sunga cewa wannan gona daga Aljannan take, sai dai kuma zunubai da sabo sun kasance Katanga da suke hana dan adam gani da kuma idrakin hakan.

    waccann gonar da take duniya ta ma’ana ita gonace daga cikin gonannakin Allah, wanda ta kasane tsakanin kabarin annabi Muhammad da kuma minbarin sa, ya zo a hadisin annabi wanda dukkanin ban gorori na sunann da na shi’a sunyi ittifaqi akan hadisin Annabi na cewa tsakanin gidana da min barina gonace daga gonannakin Aljanna

    kafi anyi isnadinsa ga abi Abdullah na cewa: manzon Allah yace tsakanin gidana da min barina gonace daga gonannakin Aljannah, mimbarina kuma hanyace daga cikin hanyoyin Aljannah, matakalar minbarina kuma matakin daraja ce a Aljannah

    sai nace: kuna nufin wannan hamaramin da muke dashi a yau ne gonar?

    yace eh da zaa yaye hijabin da kun gani.

    Duk wanda ya kasance daga cikin masu saar ganin haqiqanir abu, toh kuwa ba shakka zai ga wancan Alannan da kuma maanar ta, dakuma yaya zai kasance acikin ta, zai dan dani dadinta tako wace hanya, cikin ta rai takan sami abubuwan da take so wanda baya cutar da dan adam,

     Domin gidan Aljannah wuri ne da dan mumini zai sami hutu na har abada na ruhi da kuma na jiki, kuma gida ce da me imanin yake samu sabida ladan aiki na kwarai da yayi, acikin ta akwai darajoji da kuma matakai daban daban, akwai wanda zai kasan ce a mataki na farko, akwai wanda zaiyi makwabtaka da annabi bisa darajar hasken da take fuskar mutu.

    Akwai Aljannoni kamar Firdausi, da Darussalam, da kuma ma’awa da sauran su wanda kuma ta fi kasance a kololuwarsu itace Aljannar Allah, itace Aljannan suna da kuma sifa, an ke bantar da ita ce kawai ga waliyan Allah , wanda zasu iya shigan ta sune mutanen da suka kasance suna nafsil mutumainna wanda zata koma ga Allah cikin yarda da yarjewa.

    Duk wanda ya ziyarci dakin ka’aba da haramin Annabi  (tsakanin gidan sa da mimbarinsa) da kuma haramin imamai zai sami wata gamsuwa na ruhi da kuma na zuciya, zai ji kamar yana aljannah ne.

    Mala’iku suna dawafi akan sa da tulun zinariya da kuma na azurfa

    Tare da kofuna na lu'u-lu'u da murjani, ba bakin ciki ko ciwo face har sai ya manta kansa, kuma zai mance damuwar duniya da duk wani masifu da wahalhalun ta, zai ji kamar yana rayuwa ne cikin wata duniya ta daban, cikin annashuwa da kuma kwanciyar hankali, nanne zai ke darkin siffofi na Aljannah da aka Ambato acikin ayoyi da hadisai, duk wannan saboda Albarkan annabi ne da kuma iyalan gidan sa, da kuma karbabbiyar ziyarar su da akeyi, domin akwai wasu daga cikin masu ziyarar su da aka basu ikon ganin zahirin abubuwa da kuma ji na hakika, don haka zai ke jin amsa sallamar da yayi wa imam, ruwa cikin cokali ya ishi me hankali wanka.

    Ita wannan sassa ta Aljannah wato haramin maasumai, Allah ya daga darajar ta kuma ya karrama mutuncin ta kuma ya Albarkaci gefe da gefenta da ilimi me amfanarwa da kuma Imani na gari, hasken Allah na haskaka dukkanin kasarta, kuma wurine na saukar mala’iku da rahama da kuma albarka.

    Biharul anwar, an yi isnadin sa ga abi Alhassan Arrida na cewa Khurasan wata sassace akwai zamanin da zai zo zai kasance wurin zaman mala’iku daban daban ,

    Sai akace masa: ya kai dan Annabi wace sassace haka?

    Sai yace itace kasar tus (طوس) wallahi ita gonace daga gonannakin Aljannah, duk wanda ya ziyarceni a wannan wuri kamar ya ziyarci annabi muhammad ne kuma Allah zai rubuta masa ladan haji dubu

    Da kuma ladan karbabbiyar umara dubu, kuma a ranar gobe qiyama ni da iyaye na za mu ceceshi

    Akwai wani hadisin da yayi kama da wannan wanda anyi istidlali da shi akan imamancin imamai, kuma daga cikin ruwayar gaibu ce, saboda kafin yayi shahada ya fadi wurin da za’a bissine shi, kuma wurin zai kasance wurin ziyarar masoyansa da kuma masu wilayar sa har ranar Alqiyama, mala’iku suna saukowa a wurin akai akai daga sama, me yafi haka girma?, me yasa ziyarar kabarin su ba zai yi daidai da ziyaran kabarin annabi ba? Meyasa duk wanda ya ziyarce su ba zaa ba shi ladar ziyarar hajji dubu da umara dubu ba?, me zai hana ba zai sami ceton a’imma a ranar qiyama ba? Me zai hana wannan sashe me albarka baza ta kasance tana da hukuncin haramin Allah ba? Duk wanda ya shigeta zai aminta daga zunubai da kuma tsoro a ranar qiyama.

    An rawaito daga abi hashim alja’afari na cewa: yaji Aba ja’afar nacewa: tsakanin duwatsun tus akwai wani yanki, wannan yanki daga Aljannah yake, duk wanda ya shigeta zai aminta daga da wuta a ranar Alqiyam.

    Me zai hana Allah ba zai daga darajar wannan wuri me tsarki ba ? 

    An rawaito daga imam sadiq (as) cewa akwai wasu wuri guda hudu wanda suke da daukaka agurin Allah: Baitil Ma’amur, Najafil Ashraf, Karbala da kuma Tus 

    Kaburburan ku kamar sauran kaburbura ne, sai dai ku Allah ya  darajanta ku kuma ya mutunta ku sannan ya daukaka maqamin ku, lallai haramin ku gonace daga Aljannatul Firdausi, ba me shiganta sai wanda ya taki sa’a kuma yazo da tsarkakkiyar zuciya.