sababun labare
- Labarai » Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
- Labarai » Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
- Labarai » Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
- Labarai » MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
- Labarai » Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
- Labarai » muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
- Labarai » Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
- Labarai » Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » Shahadar Fatima Azzahra A.S
- Labarai » Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
Labarun da ba tsammani
- Labarai » Daga cikin muhimman darajojin da Fatima (as) ta kebantu da su
- Lacca » bahasul karij bahasi kan kiran sallah da ikama
- Labarai » Bikin zaman makokin na kwanaki goma daga watan Muharram mai alfarma shekara ta 1440 hijri don juyayin shahadar Imam Husaini (as)
- Labarai » Muhadarorin Samahatus Sayyid Alawi (h) na Akhlak cikin filin Husaini maxaukak
- Labarai » Sayyid adil alawi ya dawo daga tafiyarsa ta tabligi
- Labarai » maulidin imam zainul abidin
- Labarai » MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Bakir (as)
- Labarai » ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
- Labarai » Watsa muhadarar Samahatus Sayyid Adil-Alawi kai tsaye a tashar Assaklain
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » Ganawar samahatus Sayyid Adil-Alawi (h) tare da matasan kasar Labanun.
- Labarai » Bisa zagayowar ranar shahadar imam hassan mujtaba husainiyyar kazimiyya Tehran za ta raya majalisin juyayi wanda cikin wannan munasaba ayatollah sayyid adil-alawai zai hau mimbari domin gabatar da muhadara
- Labarai » ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
- Labarai » ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI KAIWA ABU ABDULLAHI HUSAIN ZIYARA A.S
Labarai wanda akafi karantawa
- munasabobi » Ma'asumiyya Haura'u Zainab amincin Allah ya kara tabbata gare ta tare da Alkamin-samahatus sayyid Adil Alawi
- Labarai » Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » Litatafan da aka buga
- Labarai » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi
- Labarai » juyayin wafatin sayyida zainab Alkubra
- Labarai » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amicin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- munasabobi » Soyayyar Husaini (as)ta haukatar da ni
- Labarai » Sayyid Adil Alawi ya halarci wurin karatun Al’qurani
- Labarai » jan hankali ko fadakarwa ga masu wa'azi
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- Labarai » Sakon ta'aziyya
- Labarai » An wallafa mujallar kazimain me lamba 204/205 na watan rajab da shaaban na shekaran 1437H wanda yayi dai dai da shekaran 2016
- Lacca » Fatima zahara madubin kyawun Allah girmansa ya girmama
- Labarai » Ubangiji ya gwabunta ladanmu da naku da tunawa da ranar shahadar kofar biyan bukatu imam musa alkazim(as).
Wasika ta uku ta karshe dangane da ra’ayoyin sayyid Kamalul haidari
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Ya ubangijina ka buda bakina da shiriya kai mini ilhama da takawa
﴿اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ﴾.
Ka shiryar damu tafarki madaidaici.
Yan’uwana maza da mata masoyana salamu Alaikum, Allah ya dawwamar daku cikin alheri da taufiki da dandagatar da kyakkyawan karshe,
Wannan itace wasikata ta uku kuma ta karshe dangane da wanda ya tsunduma ni ta hanyar tambayar da yayi mini dangane da minhajiyar sayyid Kamalul haidari, zan fadi karara da bayyanarwa da gaskiya muna rokon Allah sabati ga kowa da kowa kan wilayar sarkin muminai da iyalansa tsarkaka da wanzuwa cikin inuwar kur’ani da sahibul Asri waz’zaman Allah ya gaggauta bayyanarsa madaukakiya, lallai wilaya Alawiyya nabawiyya ita ce tafarki madaidaici siradi mikakke Allah ya azurtamu baki daya da kyakkywan karshe.
Da farko: ban kasance ina nufin suka da ishkali kan tsarin tafiyar Kamalul haidari da ra’ayoyinsa cikin wasika ta farko da ta biyu da wannan ta karshe ba, kadai dai na nufin baiwa mai tambaya labari atakaice da yanayi na gama gari da cewa lallai shi Akaramakallahu sayyid Kamnalul a yanzu fa yanada wasu bakin ra’ayoyi da suka ratse suka sabawa abinda jamhur din manya-manyan malamanmu suka tafi akai daga hauzar Najaful Ashraf da birnin qum mai tsarki, wannan ra’ayoyin nasa sun ratse daga abinda hauza ilimiya take tafiya kai da abinda magabata nagari suka tafi kai dama wanda suka zo bayansu cikin bahasosinsa da sabuwar minhajarsa, wannan wani abune wand akowa ya sani babu banbanci daga mai sabani da mai laminta, amsata ga mai tambaye ta kasance daga fuskacin bada labari daga cikin gida zuw awaje bawai kan hakikanin abun ba daga babin bayanin bayyanannun abubuwa na fili, sai dai cewa a zahiri ba’arin daga wasu yan’uwa sun karanta amsa tareda abinda ke cikin kwakwalensu daga natijar abubuwan da suka ginu kai da suka gabata daga wanda suka dace da kuma wanda suke da sabani, saboda haka wannan matsala ba daga gareni take ba kadai tana daga wasu adadi matakai nasu kansa, kamar yadda ake cewa: me yasa kake baka sukansa a ilimance ka kawo wasu maudu’ai da ishkaloli da shubuhohi maimakon bada amsa da amsa ta gama gari? to anan da farko sai ince: azurtacce shine wand aya wadatu da waninsam hakika wasu ba’ari sun daukar ma kansu sukansa da kalubalantarsa daga cikinsu akwai wanda yayi rubuta aka buga daga cikinsu kuma akwai wanda ya bi irin wannan hanyar da na bi.
Hakika mahaifina tun farko-farkon fara karatuna a hauza yayi mini ladabi da cewa in gayawa mutane kyakkyawar magana, kuma inyi kira zuwa garenbi daga daddadan nono- wannan daga babin misali kenan, kuma kada in dinga suka kan nonon da yake wurin wasu da fadin cewa tsami gareshi, lallai mutane masu hankali da kansu zasu dandana su banbance zazzakan nono daga tsatstsama Allah ne mai datarwa da damdagatar.
Sannan ya zo cikin ma’anar wani hadisi da cewa
(العاقل من يضع الأشياء في مواضعها)
Shi mai hankali shine mai ajiye abubuwa a muhallansu.
babu shakka cewa shi sayyid yana daga cikin ma’abota hankali masu daraja, sai dai cewa shi kamar yadda ta bayyanar mini (iliminsa ya zarce hankalinsa) amma ba da ma’anar nakasta shi ba, kada Allah ya tauye masa hankali, bari dai abinda ya dace gareshi shine ya ajiye iliminsa a muhallin da ya dace da shi, ya bijiro da abind ayake wurinsa daga sabo cikin bahasosi, kan fadin abokansa daga sabunta zamani da ilimi cikin nutsuwa da rusunawa, cikin girma da kyawu da yanayi da yafi dacewa ba tareda raunana hauza da yan hauza daga malamai magabata da na zamani, bari dai da dukkanin iklasi da bin tsarin hankali tareda neman taimakon Allah da kyakkyawa mai tajalli cikin taimakon hauzozi da maraji’ai da malaman addini daga wadanda suke takaicin abinda yake aikatawa, ba a gushe ba ana takaici da bakin cikin rashin mutum irinsa ba, bari daga cikinmu akwai wadanda har yanzu suke fatan kasantuwarsa nan gaba ya zama makoma mai haske da amfani ga addini da mazhaba da hauzozin ilimi da jama’a da dukkanin mutane sosai-sosai, babu tsimi babu dabara sai ga Allah madaukaki mai girma.
Ku sani hakika gabanin shekara guda mun hadu da shi mun gaisa, hakika gabanin shekara mun kasance tareda shi da dana da ma’abocin gida kan walimar abincin isha’i kan gayyatar ma’abocin gidan bisa munasabar bikin dan mai gidan wanda ya kasance daga daliban hauza, sannan zamanmu ya tsawaita fiye da awa biyu mun kuma kasan ce muna tattaunawa da juna kan batutuwa daban-daban daga abind aya ta’allaka da ra’ayoyinsa kebantattu mun yi tattaunawar cikin barkwanci na ilimi cikin nutsuwa da nishadi, lokacin da zamu yi sallama da bankwana muka rungumi juna kowanne na girmama juna ba tareda sukan juna ba, sai dai fa hakan bai nufin in bye masa in yarda da dukkanin ra’ayoyinsa in tafi kan abind aya tafi kai, lallai shi yanada ra’ayoyi daga cikinsu akwai karbabbu kyawawa hakama akwai ababen watsi da tattaunawa kansu da bahasi, sai dai cewa yana bayyanar mini Allah ne masani abinda ya bijirar daga ratsatstsan bahasi da ra’ayi daga gareshi ba zai zaunu ba nan gaba daga abinda yake fafutikarsa na habbaka hauza ilimiya da gyaranta kamar yadda yake fadi, har muslunci da shi’anci ya wayi gari karbabbe wurin wayayyun mutane daga samari yan jami’a , lallai yadda al’amarin yake shine ra’ayoyinsa na karshe-karshe basu samu karbuwa ba hatta wurin kusoshin hauza jigajiganta, to me kake tsammani kuma nan gaba kadai dai babu mai karbar wadannan ra’ayoyi nasa sai wadanda suke kan hanyar irin tasa, lallai dacewa da juna dalili ne na hadewa dda juna.
Daga karshe ma ta kai ga hatta tashoshi tauraronb dan adam na shi’a sun fara watsi da shi. Kamar yadda ta kasance a baya. Kai hatta tashar Alkausar wacce da ta kasance kasuwar bajakolin ra’ayoyinsa da tunaninsa suma sunyi watsi da shi sun ki yadda ya cigaba da bajokolin ra’ayoyinsa, lallai ni nasan abubuwan da baku sani ba babu tsimi babu dabara sai ga Allah madaukaki mai girma.
Daga cikin abin ban nishadi da dariya a wancan dare a muka hadu gidan wancan mutumi, bayan mun zauna mun gama lale da maraba da juna sai wannan mai gida Allah ya dawwamar da daukakarsa yace: lallai ni lokacin da naje hajji wasu ba’arin mahajjata da sayyid Kamalul haidari ya kasance yana birge su sun dinga tambayata gameda shi, sai cikin murmushi nace wannan ya kasance shekara nawa kenan ? sai yace: gabanin shekaru shida da suka shude suka wuce, sai sayyid Kamalul haidari ya daga murya yace: (shin wai ko ka fahimci manufar tambayar sayyid Adil Alawi? Yana son yace kadai dai hakan ya kasance a lokacin da nake kan shiriya sai dai cewa a yau......) sai muka fashe da dariya wannan shine sababin budewar kofar tattaunawa tareda sayyid muka gama tattaunawar har zuwa lokacin da sayyid kamalul haidari yake cewa: kamar yadda sayyid sistani (dm) yake d ara’ayi nima inada ra’ayina na kaina, kuna da ra’ayinku nima inada ra’yina, sai na ce masa yayi kyau mu zuba ido muga mai zai kasance nan gaba ga wanene fage zai kasance da lokaci, Allah ne mai bada kariya shine majibanci.
Sannan dana sayyid Muhammad Alawi Ya rubuta makala da alkalaminsa mai shafi 20 sai dai har zuwa yanzu lokaci yada ta bai yi sakamakon wasu yanayiyyika ta yiwu a yada ta nan gaba domin fa’idantuwa da izinin Allah.
Abu na karshe: daga wannan mimbari na gidan annabta ina aika gaisuta ga sayyid ina yi masa addu’a da kuma kaina da dukkanin mutane da shiriya da kyakkyawan karshe
(إهدنا الصراط المستقيم صراط الذين أنعمت عليهم)
Ka shiryar damu tafarki madaidaici tafarkin wadanda kai ni’ima kansu.
Daga annabawa da siddikai da salihai wadannan sun kyautata zama abokan tafiya,
Lallai ni na sauke nauyi na yafe daga wanda yaci nama ya soke da konannen harshe, sabod ayana jahilta ta yana kuma jahiltar abinda na nufa daga wasikuna lallai shi ya samu uzuri, sai dai cewa kuji tsoran Allah hakikanin tsoransa, kuji tsoran Allah cikin maraji’ai da malamai da hauzozi, amincin Allah ya tabbata gareku, karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai
18 jimada sani 1439