sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
  • Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
  • Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
  • MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
  • Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
  • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
  • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
  • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
  • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
  • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
  • Shahadar Fatima Azzahra A.S
  • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
  • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
  • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
  • sababun labare

    Labarun da ba tsammani

    SHAIDUN ASHURA (KASHI NA FARKO) {MU’ASSASAR WARISUL ANBIYA}

    SHAIDUN ASHURA (KASHI NA FARKO) {MU’ASSASAR WARISUL ANBIYA}

    Malami mai gabatar da muhadara:  samahatus Sayyid Adil-Alawi.

    Allah madaukakin sarki cikin littafinsa mai girma yana cewa

    ﴿يرفع الله الذين آمنوا منكم والذين أُوتوا العلم درجات﴾

    Allah yana daukaka darajar wadanda suka yi Imani da wadanda suke da ilimi.

    Cikin sharar fage zamu Ambato shaidu daga wurin Ahlil-baiti (as) daga nan kuma sai mu tsallaka zuw aga Imam Husaini shugaban shahidai da kuma abin da ya kasance daga shaidu cikin Karbala mai tsarki a yinin Ashura da daren ta.

    Bahasi shaidu ya ta’allaka da ilimin Irfani, saboda haka za mu yi tambaya mene ne Irfanin muslunci?

    Maganganum dangane da Irfani”

    Akwai mutanen da suke da sabawa da Irfani da sura saki babu kaidi, musammam ma cikin hauzozin ilimi da muke da su, akwai kuma wadanda suka karbe shi da sura saki babu kaidi, akwai kuma wadanda suke karbarsa tareda dabaibayin sharadi.

    Shin Irfanin muslunci yana daga cikin ilimummukan muslunci ko kuma dai yana daga ilimin da dan Adam ya samar da shi da kansa?

    Irfani a cikin isdilahi da kuma ilimance, tarihinsa yana komawa zuwa ga falsafa, sannan ita kuma falsafa tana tsohon tarihi cikin zauruka karatuttukan zamani na Rumawa da Girkawa a yammacin turai, haka wurin Fahlawiyyun da Indiyawa a gabashin duniya, hikima d afalsafa suna da tarihi mai tsaho da fadin gaske, Almajiran malami na farko ma’ana malam Arasto sun kasu zuwa sinfi uku, sinfi da yake biye d ashi yake karbo falsafa daga daga gare shi wadanda aka fi sani da suna Masha’iyyawa, da kuma sinfi na biyu cikin makaranta da filinta sun karbi falsafa daga gare shi sune wadanda suka shahara da sunan Rawwakiyun, da kuma sinfi na karshe wadanda suka kasance kamar suna kallo malaminsu ne suna karbar falsafa da hikima daga gare shi da mahangar Is’hraki, sai suka shahara da sunan  Is’hrakiyyun,

    Irfani ya samu ne daga mahaifar is’haraki, saboda haka ne ma ilimin Irfani yake komawa zuwa ga Falsafa da tarihinta, da wannan ne zai iya zama ilimin da dan Adam ya samar, ma’ana tubali na farko da aka sanya shi a matsayin isdilahi kuma kamar matsayin tadwini na ilimi kadai ya kasance daga hannun mutum, tabbas babu shakka cikin kasancewar dukkanin ilimummuka daga Allah matsarkaki suke daga kuma annabawan sa suke- wannan shi ne abin da muka yin Imani a kai- sai dai cewa a matsayin rubutaccen ilimi da sanyawar ilimi kadai sun kasance daga hannun dan Adam, sannan daga cikin ilimummuka akwai wadanda suka kasance a hannun Allah kamar yand aya zo cikin madaukakin hadisi:

    «إنّما العلم آية محكمة، أو سنّة قائمة، أو فريضة عادلة»،

    Shi ilimi kadai dai ay ace bayyananniya, ko kuma sunna tsayayya, ko farilla adala.

    Ma’ana ilimummukan muslunci uku n: ilimin sanin Akida, da ilimin Akhlak da ilimin fikihu.

    Maganganu dangane da mutumin da assasa ilimin Irfani:

    Akwai sabani cikin musulmai kan wane ne ya assasa ilimin irfani? Shin wai shi wannan ilimi na irfani yana daga cikin jerin ilimummukan muslunci ko kuma dai kirkirar dan Adam ce? Daga cikin manya masana- musammam ma daga masanan gabashin turain akwai wanda ya tafoi kan cewa irfani ilimin irfanin muslunci lallai fa ba daga musluncin ya samo asali ba, bari dai wani abu ne da aka cudanyo shi daga wajen muslunci aka shigar da shi cikin muslunci, ance: daga malaman kiristanci yake, wasu kuma sunce: daga sufancin Indiyawa da Budawa ya samo asali, Irfani ya shigo cikin muslunci ne daga budanci, daga cikin su kuma akwai wanda ya mayar da shi zuwa ga Yahudawa, akwai kuma wanda ya komar da shi zuwa ga falsafa, masana falsafa da hikima sun sassaba kan haka, sai dai cewa mu abin da muke Imani da shi shi ne cewa ilimin Irfani muslunci kadai dai shi daga muslunci yake, muslunci ne ya samar da shi, domin cewa shi yana iya sabawa ta fuskanin maudu’i da kuma fuskanin dokoki da hanyoyi, kamar yanda kuka sani shi sassabawar ilimummuka kadai dai yana kasancewa cikin maudu’i, cikin maudu’i da mahmuli da agraz ilimummuka sashen su ka iya sabawa daga sashe, maudu’in ilimin irfani yana sabawa da sauran ilimummuka, sannan shi irfanin muslunci ya kasu zuwa makaranta biyu: makarantar sunna da makarantar shi’a, adadi mai yawan gaske daga malamai sun tafi kan cewa lallai fa shi irfani nan ba wani abu bane face sufanci, dama fuskar sufanci ta biyu shi ne irfani, daga manyan masana da suka tafi kan wannan ra’ayi akwai Shahid Mudahharai (a.r) ta yanda dangane da irfanin muslunci ya bayyana cewa: lallai shi irfani da hankalin nazari kadai shi ne irfani, sai dai kuma cewa ta hanyar hankalin ilimi kadai dai shi ba wani abu bane da ya wuce sufanci, ma’ana dai Arifi shi ne Sufi, sannan zaka samu akwai wadanda suka zare takobin yakar irfani da wadanda ake kira da Araifai sakamakon sun fassara irfani da sufanci, shi kuma sufanci abin wurgi ne a makarantar Ahlil-baiti (as) muna da hadisai masu tarin yawa daga Ahlil-baiti (as) kan cewa dukkanin wanda ya taimakawa Sufi daidai yake da wanda ya taimaki Yazidu bn Mu’awiya kan kisan Imam Husaini, sannan cikin wannan zamani da muke ciki- musammam ma bayan samun nasarar juyin-juya halin muslunci a Iran da jagorancin Imam Komaini (rd) zamu ga cewa na bude kofa dangane ilimin irfani, saboda wajibi mu zage dantse mu san ingantaccen irafni lafiyayye, wanda ya ginu kan kur’ani da Ahlil-baiti, ma’ana muna karbar irfanin muslunci wanda maudu’in sa ya doru kan tubalin sairi da suluki zuwa ga Allah matsarkaki, sannan baki dayan  dokokin sa da mas’alolin sa ana karbo su daga kur’ani mai girma da Ahlil-baiti tsarkaka.     

    Babu shakka kan cewa daukakar mutum da girman sa kadai suna kasancewa ta hanyar hankalin sa da zuciyar sa, sakamakon Allah ya halicci mutum cikin mafi kyawun tsari da zubi, ya rakkaba shi da turbaya daga kasa domin ya kasance mai tawali’u, kamar yand aya rakkaba shi da Mala’ika daga samaniya da ruhu daga gare shi domin ya daukaka, lallai a wannan lokaci yana kasancewa tsakankanin baka biyu bakan nuzuli da na su’udi, lallai shi yana sauka daga madaukaka cikin bakan nuzuli ya zuwa kasancewa cikin gidan duniya makaskanciya, sannan bayan haka daga wannan gida na duniya daga turbaya da kasa da mala’ikantaka yana tsallakawa ya hau zuwa malakutul A’ala, ya zuwa subuhiyya da kuddusiyya ta Allah, sai ya kasance cikin hallarar Allah madaukaki, domin cewa ita duniya hallarar Allah ce saboda haka ka da ka sake ka aikata sabo cikin hallarar sa, ya daga zuwa bakan su’udi, cikin wadannan baka guda biyu bakan su’udi da nuzuli kadai anan irfani yake kasantuwa, irfani a dunkule kadai yana tajalli cikin fadin sa madaukaki: 

    ﴿إنّا لله وإنّا إليه راجعون﴾،

    Daga Allah mu ke gare shi za mu koma.

    Ingantaccen irfanin muslunci karkashin hasken kur’ani da Ahlil-baiti kadai yana kasancewa igiya mai sadar da bawa da ubangijin sa, Allah matsarkaki ya halicci mutum yayi huri cikin sa daga ruhin sa- shi ruhin wani Mala’ika mafi mafi girma daga Jibrilu (as) ya dnaganta shi zuwa gare shi domin daukaka shi, mutum da sabuwar tsiruwar sa yana cikin mafi kyawun tsari, albarku sun tabbata ga Allah mafi kyawun masu halitta.

    Bana nufin kiran sa da sunan irfanin shi’anci, babu banbanci cikin kasantuwar mai Imani da dan shi’a ne ko dan sunna, domin akwai wadanda suke karbar irfani daga Ahlil-baiti (as) kamar misalin Sufaye; domin cewa sun kasance tsakankanin irfani da sufanci kamar yand ana ambata, akwai mas’aloli da yawan gaske da suke da kamanceceniya da juna, sai dai cewa akwai mihwari jigo da yake banbance tsakanin irfani na asali da kuma sufanci da yake gwamutse cikin makarantunsa, muna da makarantun sufanci fiye da dari uku da suke raya sufancin su  daga kyallen su suna karba daga murshidin su da shehin su, shi kuma shaik yana karbowa daga shehin sa, silsilar sufanci tana tukewa da karkarewa zuwa ga Albarki sannan kuma ta tsallaka zuwa ga Imam Rida (as) sannan zuwa Sarkin muminai Ali (as) makarantun sufancin sunna da na shi’a baki dayan su tarihin sufancin su yana komawa zuwa ga Sarkin muminai kan cewa shi ne waliyin dukkanin waliyyaim da kuma daga gare shi aka karbi kyallen, tabbas Sarkin muminai ya karbo kyallen daga Manzon Allah sannan shi kuma Manzon Allah (s.a.w) ya karbo daga Allah matsarkaki madaukaki, da wannan zaka ga akwai fuskar kamanceceniya da juna mai yawan gaske tsakanin irfani na asali da muke Imani da shi da sufanci, daga nan zaka kiya samun dan sunna da yake kan irin irfani da muke Imani da shi, hakan na kasantuwa karkashin kur’ani mai girma da Ahlil-baiti tsarkaka, saboda hakan a kowanne lokaci muke mai da hankali kan cewa mu irfanin da muke Imani da shi wanda kofofin sa suke ga bude ga gobe mai zuwa da sasanni sababbi insha Allah, lallai an samu masu tahkiki cikin wannan fage, ma’ana irfanin da ya ginu kan kur’ani mai girma da tsatso tsarkaka, da zmu koma tarihin irfanin muslunci za mu samu cewa shi yana daga cikin daya daga ilimummukan muslunci, lallai irfani yana danganewa da dayan biyun sinfofi daga ilimummuka

    Na farko: ko dai ya dangane zuwa ga sinfin ilimummukan assasar su wadanda muslunc ya shuka irin su kamar sauran ilimummuka, misalin fikihu da ilimin tafsiri da hadisi da abin da ya yi kama da haka.

    Na biyu:  ko kuma ya dangane zuw aga sinfin ilimummukan da mutane suka assasa su wadanda mutum ya shuka irin su ya kuma ba da gudummawa cikin habbaka su da tace su, sannan muslunci da musulmai ya kara musu cigaba kamar misalin ilimin likitanci da physics da falsafa da abin da ya yi kama da haka.

    Nayi Imani cewa muslunci kammalallen addini ne

     ﴿اليوم أكملت لكم دينكم﴾، ﴿ومن يبتغِ غير الإسلام ديناً فلن يُقبل منه﴾،

    Yau ne na cika muku addininku. Duk wanda ya nemi wani addini koma bayan muslunci ba za a karba daga gare shi ba.

    Hakika ilimin mutanen farko da na karshe da dukkanin abin da yak e ingantacce cikin dukkanin ilimummuka da fannoni kadai dai daga littafin muslunci yake ma’ana cikin kur’ani mai girma, yana tsono hasken imgantaccen ilimin irfanin muslunci daga Assaklaini-littafin Allah da tsasto tsarkaka, saboda haka tushe na farko uwa ga ilimin irfanin muslunci shi ne littafin Allah da sunna tsarkakka da hanyar A’imma tsarkaka.

     

    Alamomi da kudud ba farko-farko da rukunai tushe na ilmin ingantacen irfanin muslunci sun ginu kan wadadannan tubalai da zasu zo kamar haka:

    Na farko: dayantacciyar fidira, ta yanda za mu ga Allah ya halicci mutum kan tsarin halitta dayantacciya katangaggiya, kamar misalin kur'ani mai girma da wahayi, da maganganun ma'asumai (as).

     

    Na biyu: hankali wanda yake a matsayin fitila  mai haskakaw, ta hanyarsa mutum yake banbantuwa da sauran halittu marasa magana

    Na uku: zuciya, matsayinta na cibiyar dukkanin soyayya da tausasawa da dukkanin ihsasin mutum, da kuma juzu'i da yake karbar ishrakat da fadaka da ilimin Allah.

    Na hudu: irada da zabi, wadannan abubuwa biyu  ne da suke misalta mana yancin mutum da cin gashin kansa cikin aikatawa da bar, idna ya so zai yayi idan ya so ya bari,

    Na biyar: lamiri da dabi'ar mutum, wadannan abubuwa biyu ne da suke bayyana dokar Akhlak da taka tsantsan cikin zurfafar dan Adam, wadanda ake bayyana su cikin isdilahin kur'ani da nafsul lawwama (nafsu mai yawan zargi)

    Na shida: soye-soyen rai da karfin nafsu, da mafi fadada daga kasantuwar ta mai kyawu ko mara kyawu, wato sune karfin fushi da sha'awa ma'ana karfi mai jawontowa da karfi mai tunkudewa, wadannan karfin nafsu da karfi soye-soyen rai kadai su karfi ne da yake cikin samuwar mutum kamar misalin karfin wutar lantarki, mutum zai iya amfani da wannan karfi  na sinadarin makamashin nukiliya kamar misalin nakiyar nukiliya da bata barin komai, sannan kuma yana iya amfani da cikin manufofi masu kyawu na zaman lafiya kamar misalin samar da wutar lantarki, soye-soyen rai idan suka kasance jagoran hankali da soyayya da ihsasi wanda cibiyar su zuciya, to fa lallai hakan zai kai mutum zuwa ga hasara a wannan lokaci ya wayi gari batacce mai batarwa, amma idan suka kasance karkashin jagorancin hankali to a wannan lokaci mutum sai ya kasance cikin farin ciki.

    Daga banbance-banbance tsakanin ingantaccen irfanin muslunci da sufanci shi ne wannan gaba da mahalli, sufaye suna cewa: wajibi kanmu mu yaki soye-soyen rai mu kore su daga nafsu din mu ta hanyar kauracewa mutane, da kauracewa duk wani jin dadi, da sanya kausassan tufafi da abin da yayi kama da haka. domin har sukai ga korar wannan soye-soyen ran da wannan karfi na nafsu daga nafsu din s, sai dia cewa shi imgantaccen irfanin muslunci yana cewa lamarin bah aka yake ba, da farko dai dole ne a tabiyantar da nafsu da tsarkaketa da kuma nemarwa wadannan soye-soye rai fuskar da zasu iya kasancewa na halas a shari'ance, domin wannan karfi yana da motsarwa, sha'awa da fushi kadai su karfi ne mai motsarwa, saboda haka babu makawa daga garesu.

    Wannan kenan, sannan kuma shi ingantaccen irfanin muslunci ko kuma muslunci da sura mafi gamewa kadai shi yana tsarkake mana wannan krafi na nafsu, daga nan ne zai bayyana cewa lallai mutum yana riska da Aklul nazari sannan yayi aiki da abin da ya riska da Aklul amali.

    Allah matsarkaki ya halicci mutum ya rakkaba shi da wannan majmu'a ta ruhi da gangar jiki, ya sanya tsarin halite da zuciya da hankali da soyayya cikin ruhin sa, a wannan lokaci ne idan hankali yayi galaba kan karfin soye-soyen rai sai mutum ya wayi gari Arifi ma'abocin hikima , amma idan soye-soyen rai sukai galaba kan hankali to a wannan lokaci sai mutum yayi hasara ya gaza cin riba.

    Kadai hankali na kasancewa fitila ga sanin hanya, sakamkon bayyanarwarsa ga hany-da zurfafa tunani da karatu da koyarwa da yawan neman ilim, ma'ana cikin kaziyoyin hankali mutum yana bukatar malami da kuma karanta lamarin da kuma koy, shi ilimi a yarinta kamar misalin rubutu ne kan dutse, amma ilimi lokacin da aka rigaya aka girma kamar misalin rubutu ne kan kogi, lallai cewa:

     ﴿ومَن نعمّره ننكّسه في الخلق﴾،

    Dukkanin wanda muka raya shi zamu tauye halittarsa.

    Daga karshe ta yiwu mutum ya rasa wannan ilimi wanda ya same shi da hankalin sa. Da yawan lokuta mutum na samun matsalar raunanar karfin hankali ta fuskar riskar ilimummukan hankali, zaka same shi lokacin samartakar sa yana tsananin jin dadin yin kaatu, sai dai cewa lokacin tsufan sa abin takaici sai ka same shi yana kasala da nauyin jiki cikin hakan, ilimummukan hankali kadai suna kasancewa karkashin dalilan mandiki ma'ana sugra da kubra da natija, kadai su zasu kasance hujja, saboda a wajen mu akwai hujja akwai kuma ilimibn hankali, wannan yana kasancewa da tunani da zurfafawa da lura da kuma karantawa sosai, muna da zuciya, ita zuciya itace mazubin kuma madubi mabayyana ga yaye hakika, kamar yanda hankali yake fitila ga yaye hakika, ma'ana hankali yana yaye mana tabbatattun abubuwa, zuciya ma tana yaye mana su, sai dai cewa shi hankali yana yaye mana su karakshin hujja, amma ita zuciya tana yaye su karkashin kashafi da shuhudi, anan ne banbanci yake bayyana tsakanin falsafa da irfani, da kuma sabanin da yake tsakanin masana hikima da masana falsafa, tama iya yiwuwa kowanne daya daga cikin su yake kore abokin rigimar sa ba tare da cewa ya san rigimar da take tsakanin su banbanci ne na lafazi kawai kamar yadda aka fada, ba banbanci ne na tushe ba..

    Yayin da muka tsinkayi hakikar lamari, da sannu za mu mu samu cewa babu banbanci tsakanin falsafa da irfani, dukkanin suna kwarar kan makwarara guda daya, sai dai cewa su suna sassabawa ta fuskar hanyar kowanne daya cikin su da kuma uslubi, ta yanda zaka samu cewa shi irfani yana kasantuwa ta hanyar kashafin shuhudi, sai dai cewa ita kuma falsafa tana kasantuwa daga kafuwar hujja, a wannan lokaci ya zama dole mu tsinkayi wannan hakika mu ganota, ita zuciya tana kaiwa zuwa ga mukamin kashafi da shuhudi da bayyanuwar tabbatattun abubuwa karkashin tsaftatuwarta da tacewa, da kuma karkashin zikiri da tak'wa da wa'azi, sannan su kuma ilimummukan hankali suna tabbatuwa karkashin zurfafa tunani da karatu, shi ko ilimin da ake samunsa ta hanya zuciya bay a kasanuwa da yawan karat, kamar yanda ya zo a hadisin unwanu basari daga Imam Sadik (as)

    «إنّما هو نورٌ يقذفه الله في قلب مَن يشاء أن يهديه»،

    Kadai shi ilimi wani haske da Allah yake sanya shi cikin zuciyar wanda ya so shiryar da shi.

     

    Wannan ilimi na zuciya na ilhama shi ne tushe kuma shi ne asasin irfanin muslunci ingantacce, duk wnada ya kai  zuwa ga wannan mukami da sannu zai kasance Arifi masanin Allah matsarkaki madaukaki, kuma da sannu tabbatattun abubauwa za su yaye gare shi, zaka same shi yana magana da harshen ma'arifa duk da cewa yana kafa hujja da harshen hankali, ma'ana baya wadatuwa da hankali sabod yare da yake amfani da shi cikin isar da abind ayayi kashafi da shuhudinsa kadai dai yana kasancewa  da hankali, saboda ba zai yiwu ya wadatu da ga hankali ba, wanda yake kaiwa ga mukamin irfani kadai dai yana kaiwa ga hakan ta hanyar zikirin zuciya da hallara, domin shi zikiri shi ne hallarar abin Ambato ga mai Ambato, sabanin ziyara wadda take hallarar mai ziyara ga abin ziyara, Allah matsarkaki dangane da mu yafi kusa daga jijiyar wuya bari dai shi ne mai shiga tsakanin mutum da zuciyar sa, sai dai cewa hijban haske, cikin bakan suudi yah au zuwa ga ubangijin sa-yana tsakanin baka biyu ko kuma mafi kusa daga haka, idan yak eta wadannan hijabai, kuma cikin bakan sa su'udi a wannan zai zama ana kimsa masa ilimin ladunni ilhami, wannnan shi ne irfani, natijar irfani iliminsa da idarakinsa za su kasance daga idarakin ilhma, tabbatattun abubuwa na shari'a da halittazasu dinga yayewa gareshi, alal misali yayin da ake Ambato asraran ibada da asraran hajji dana sallah, kadai dai ana ambaton su daga wannan mafara, daga kashafi da shuhudi, jigo cikin wannan kashafi da shuhudi lallai baya kasancewa sai bayan Akidu sun kasance lafiyayyu ingantattu, dabi'u su kasance  kyawawa, bayan kammala marhaloli da matakai akidu ma'ana bayan  kammaluwar akidu da dabi'u, saboda wannan kofa da mukami kowanne mutum yana begen yin da'awar sa, da yawan mutane lamarin ya cukurkude masa da sa hannun shaidani sai ka same sun da'awar abin da babu shi cikin sa.

    A wannan lokaci irfani yake bayyana a wannan lokaci mutum yake kasantuwa cikin dayin san a masaukan sa na irfani da mukaman sa da halayen sa da suke gagngara kan sa, babu banbanci cikin kasancewa masauki dubu ko dari uku ko guda dari, kamar yanda hakan yake sananne shahararre cikin littafin (Manazilul Akirin) na littafin Kajo Abdullahi Ansari, lallai shi kadai zai isa ga irfani na hakika na gaskiya bayan kammaluwar akidu da kasantuwar su lafiyayyu.

    Da yawan manyan malumma sun tafi kan cewa tushen da sasin irfanul nazari kadai dai an dauko shi daga Muhuyul dini Ibn Arabi, amma ni a ra'ayina hakan ba inganta ba, saboda Arifi shi ne wanda tabbatattun abubuwa suke bayyana gareshi kamar yanda suke a hakika, bawai yayi da'awar kashafin hakika ba.