sababun labare
- Labarai » Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
- Labarai » Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
- Labarai » Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
- Labarai » MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
- Labarai » Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
- Labarai » muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
- Labarai » Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
- Labarai » Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » Shahadar Fatima Azzahra A.S
- Labarai » Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
Labarun da ba tsammani
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
- Labarai » Taron sada zumunci
- Labarai » Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi kan shahadar imam Muhammad bakir amincin Allah ya tabbata gareshi
- munasabobi » BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
- Labarai » Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alawi
- Labarai » RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
- Labarai » Bayanin sayyid Adil alawi akan mujalla na dorinnajafi
- Sanarwa » Majallanna mai suna Sautil kazumai tafuto
- Labarai » An buga mujalar sautil kazimin me lamba 210/211 wacce take fitowa a wata
- Labarai » Daliban hauza na labanon sun ziyarci Sayyid Adil Alawi
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- munasabobi » TUNAWA DA HAIHUWAR IMAM ALIYU BN MUHAMMAD ALHADI A.S
- munasabobi » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
- Labarai » Litatafan da aka buga
Labarai wanda akafi karantawa
- munasabobi » Ma'asumiyya Haura'u Zainab amincin Allah ya kara tabbata gare ta tare da Alkamin-samahatus sayyid Adil Alawi
- Labarai » Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » Litatafan da aka buga
- Labarai » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi
- Labarai » juyayin wafatin sayyida zainab Alkubra
- Labarai » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amicin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- munasabobi » Soyayyar Husaini (as)ta haukatar da ni
- Labarai » Sayyid Adil Alawi ya halarci wurin karatun Al’qurani
- Labarai » jan hankali ko fadakarwa ga masu wa'azi
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- Labarai » Sakon ta'aziyya
- Labarai » An wallafa mujallar kazimain me lamba 204/205 na watan rajab da shaaban na shekaran 1437H wanda yayi dai dai da shekaran 2016
- Lacca » Fatima zahara madubin kyawun Allah girmansa ya girmama
- Labarai » Ubangiji ya gwabunta ladanmu da naku da tunawa da ranar shahadar kofar biyan bukatu imam musa alkazim(as).
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku taron muminai masoyan Husaini (as)
Bayan haka, hakika Allah ta’ala cikin littafinsa mai girma yace:
﴿وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوبِ﴾[1].
Duk wanda ya girmama ibadojin Allah lallai tana daga takawar zukata.
Mamaki ta kaka cikin jihadi da yakar yan ta’addan Salafiya (Da’ish) muna sadaukar da rayukan a zubar da jinanen mu karkashin fatawar Maraji’ai Salihai amma kuma cikin raya wasu ba’ari daga ta’aziyar Imam Husaini (as) sai mu dinga karbar fatawa daga Haura’u Zainab (as).
Hakika Assayada Zainab (as) raina fansa gareta bata laminci hakan ba, lallai ita kamar Imam Zaman Alhujja (as) ce, tana mayar da mu zuwa ga Fakihai a zamanin gaiba Kubra, sannan shi Marja’i fakihi wand aya cika sharudda shine wanda yake komawa zuwa ga Assayada Zainab (as) domin karbar hukunci daga riwaya da tarihi da hadisanta, domin ya tantance rarrauna daga ingantacce da hadisan da suke da isnadi da ababen la’akarim domin ya tantance wuraren da akai kara da juna cikinsu, kuma ya hada tsakaninsu da hadawa da kafa hujja ko jam’il tabarru’i, tana iyab yiwuwa abinda aka rawaito daga gareta da sauran Ahlil-baiti ya kasance rarrauna cikin isnadi da dalala, ko kuma ya kasance yana cin karo ba zai iya yiwuwa a warware matsalarsa ba da jam’il dalala ko na tabarru’i sai ya zama ya tilasta faduwarsa, ko kuma ya kasance yana sabawa hankali ko wani abu makamancinsa, sakamakon abinda yake kewaye da shi daga matsaloli da ishkalai na fanni wadanda masana fannin tantance hadisai da riwaya daga fakihai su ke tsinkaye a kansu(Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya daga cikinsu ya kuma kare wadanda suke rage)
Abinda yafi kamata daga kowannce mawaki da mai rera wake dama duk wani mai karanta huduba da dukkanin wanda yake raya zaman makoki da ta’aziyyar da majalisan jimami da maukibai da dukkanin wani mas’uli kai har ga zuwa matashi balagagge wanda yake hidima cikin maukibi wajibi aikinsa ya kasance ingantacce karbabbe a hankalce da shari’a domin ya samu lada kan aikin ka da ya bige da janyo kansa azaba da ukuba, ka da kuma ya zamanto ya cutar da shugaban shahidai (as) da aikinsa, domin shugaban shahidai (as) kamar mahaifinsa Sarkin muminai (as) yake cikin fadinsa amincin Allah ya kara tabbata a gare shi :
(قَصم ظهري إثنان: عالم متهتك لا يعمل بعلمه، وجاهل متنّسك يعمل بجهله ويعبد ربه عن جهل).
Mutane biyu sun karya mini gadon bayana: da malami mai keta alfarma wanda baya aiki da iliminsa, sai kuma jahili mai ibada yana aiki da jahilci yana bautawa ubangijinsa kan jahilci.
Duk wanda yake raya ta’aziyyar Husaini (as) kan jahilci da son rai, lallai shi babu shakka yana karya gadon bayan Imam Husaini (as) da kofaton kafafun dokin jahilcinsa. Yana karya gadon bayan wanzazzen yunkurin Imam yana kuma rusa gininsa na kawo gyara cikin al’umma da dukkanin mutane da aikinsa na jahilci da bata, lallai al’ummar muslunci sune mafi alherin al’ummomi da aka fito da su aka samar da su domin mutane, lallai Allah ya cika Annabta da manzanci da cikamakin Annnabawa shugaban manzanni Muhammad (s.a.w) ya aiko shi da shiriya zuwa doran kasa don tabbatar da adalci da daidaito bayan an cika kasa da zalunci da danniya.
Sannan kamar yanda muke kira zuwa ga shi’a masu wilaya da masoya Husaini (as) da dukkanin bangarorinsu da banbance-banbance harshensu ya zuwa ga taimako kan raya zaman makokinsa da dukkaninh abinda Allah ya hore musu daga karfi da nishadi da dukkanin kamala, da dukkanin abinda yake bayyanar da bakin ciki da sanya kuka, haka zalika muna jan kunnenmsu muna yi musu gargadi daga ayyukan jahilci da wauta da shirirta da hauragiya da dukkanin abinda yake bakanta fuskar mazhaba.
Lallai shi muslunci da Manzon Allah (s.a.w) kamar yanda ya kasance mai bushara a daidai wannan lokaci kuma ya kasance mai gargadi, ya kuma kasance fitila mai haskawa Manzo mai bada shaida, Allah shi ne masanin manufa.
Godiya da yabawa ga jagororin ni’ima, farin ciki ya tabbata ga masoya Husaini cikin kukansu da shashshkarsu da sadaukarwarsu cikin raya ibadojin zaman juyayi halastattu da suke dacewa da hankali, lallai suna daga ibadojin Allah, duk wanda ya raya ibadar Allah lallai hakan na daga tsoran Allah.
Daga cikin abin da ba boye yake daga dukkanin mumini da mumina shine cewa al’amarin shugaban shahidai (as) da ranar Ashura da kasar Karbala da ibadojin ta’aziyyar Husaini halastattu lallai suna daga tajallin hasken Husaini (as) da fitilarsa ta ubangiji (lallai Husaini fitilar shiriya ne kuma jirgin tsira) shi hasken Allah ne mafi girma da makiya da masu shakku kullum suke kokarin kawo shubuha da cikas kansa.
Suna ta kai kawo don bushe hasken Allah matsarkaki sai dai kuma cewa Allah zai cika haskensa da yake tajalli cikin fansar jinin shugaban shahidai amincin Allah ya kara tabbata a gareshi ko da kuwa musrikai da kafirai basa so.
Sha’a’irul husainiyya halastattu suna daga jan layi duk wanda ya kusance su ya nemi ketare su ya halaka ya lalace
Farin ciki da aljanna su tabbata ga wanda yake gaggawa cikin raya su da kafafunsa da alkalaminsa da jininsa, lallai shi shugaban shahidai tafarki ne mikakke tareda wadanda Allah yayi ni’ima kansu daga Annabawa da Siddikai da Shahidai da Saliahi sun kyautata zama abokai, karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai
اللّهم عجّل لوليك الفرج والنصر والعافية
Ya ka gaggauta bayyanar waliyinka ka bashi lafiya.
Ya Allah ka amsa ya ubangijin talikai tsira da aminci suka tabbata ga Muhammad da iyalansa tsarkaka