sababun labare
- Labarai » Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
- Labarai » Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
- Labarai » Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
- Labarai » MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
- Labarai » Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
- Labarai » muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
- Labarai » Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
- Labarai » Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » Shahadar Fatima Azzahra A.S
- Labarai » Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
Labarun da ba tsammani
- Labarai » Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
- Labarai » FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
- Labarai » Samahatus Sayyid Adil-Alawi (h) ya tarbi maziyarta yan asalin kasar lubnan da suke zaune a kasas siwidin (Sweden
- Labarai » juyayin wafatin sayyida zainab Alkubra
- Labarai » Kalmar munasabar mauludin Fatima zahara ga samahatus Sayyid Adil-Alawi (h)
- Labarai » Watsa muhadarar Samahatus Sayyid Adil-Alawi kai tsaye a tashar Assaklain
- Lacca » bahasul karij bahasi kan kiran sallah da ikama
- munasabobi » Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
- Labarai » Sayyid Adil-Alawi zai hau minbari don yin lacca kan Munasabar tunadawa rasuwar mawakin Ahlil-baiti Sayyid Muhammad Bakir Alawi
- Labarai » Mu’assasar warisul Anbiya’i ta tarbi Samahatus Sayyid Adil-Alawi (h)
- Labarai » Cikin yardar Allah samahatus Sayyid Adil-Alawi zai haskaku da ziyartar shugabansa abin koyinsa Imam Abu Abdullahi Husaini A.S
- Labarai » Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
- Labarai » Insha’ Allah sayyid adil-alawi zai fara bada darasin bahasul karijul fikihu daga ranar litinin 1 ga watan rabi’ul awwal 1439
- Labarai » Samahatu Assayid Adil-Alawi ya kai ziyara mu’assasatul Dalili a birnin Qum wacce ta ke karkashin hubbaren Imam Husaini (as)
Labarai wanda akafi karantawa
- munasabobi » Ma'asumiyya Haura'u Zainab amincin Allah ya kara tabbata gare ta tare da Alkamin-samahatus sayyid Adil Alawi
- Labarai » Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » juyayin wafatin sayyida zainab Alkubra
- Labarai » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi
- Labarai » Litatafan da aka buga
- Labarai » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amicin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- munasabobi » Soyayyar Husaini (as)ta haukatar da ni
- Labarai » Sayyid Adil Alawi ya halarci wurin karatun Al’qurani
- Labarai » jan hankali ko fadakarwa ga masu wa'azi
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- Labarai » Sakon ta'aziyya
- Labarai » An wallafa mujallar kazimain me lamba 204/205 na watan rajab da shaaban na shekaran 1437H wanda yayi dai dai da shekaran 2016
- Lacca » Fatima zahara madubin kyawun Allah girmansa ya girmama
- Labarai » Sakon ta'aziyya
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Assalamu Alaikum yaku taron muminai masoya Husaini (as).
Bayan haka: hakika Allah ta’ala mai hikima cikin littafinsa mabayyani mai girma ya ce:
﴿وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوبِ﴾[1].
duk wanda ya girmama ibadojin Allah lallai tana daga takawar zukata.
Babu shakka da kokwanto cikin dukkanin mutumin da ya kasance mai tsoran Allah tabbas zai kasance mutum mai girmama ibadojin Allah girmansa ya girmama da abubuwan da suke raya ambaton waliyinsa masoyinsa fansarsa shugaban shahidai Imam Husaini (as) wanda aka rubuta shi a Al’arshi (Husaini fitilar shiriya ne jirgin tsira).
Babu shakka kan cewa ma’abota takawa suna cikin lambunan aljanna da koramu, suna cikin matsugunin gaskiya gurin sarki mai ikon yi.
Kadai dai ana raya ibadojin Allah da sha’a’irun husainiyya cikin neman yardar ubangiji ba da biyewa son rai ba kuma da abin da ya ginu kan jahilci ba, ana raya su ana tsayar da su kan ma’aunan shari’a.
Kadai dia ana raya ta’aziyyar Husaini (as) ta hanyar aiki da abin da kur’ani da sunna da ijma’ai da hankali suka tafi akai, wannan shi ne abin da masana fatawa suka tafi akai daga Fakihanmu masu daraja daga wadanda suka kasance sun cika sharuddan fatawa.
Wannan shi ne asali da aka doru a kansa a zamanin Gaiba Kubra, idan ya kasance halascin ibadojin Allah suna tabbatuwa da dalilai na filla-filla daga littafin Allah da sunna da ijma’i da hankali a wurin malaman ilimin Usul daga mabiya Mazhabar Ahlil-baiti (as) to haka zalika ta’aziyyar da zaman juyayin Husaini (as) wanda yake daga furu’a daga wancan asali da kuma kasancewa daga tajallin ibadojin Allah matsarkaki.
Idan ya kasance ibadojin Allah suna matsayin asalin bishiya da jijiyoyinta, to lallai daga cikin reshen wannan bishiya da kayan marmarinta shi ne sha’a’irul husainiyya, a bayyane yake cewa yana gudana cikin rassan furu’a abin da yake gudana daga asali, wannan shi ne abin da hujja da kur’ani Irfani ya doru a kai, ma’ana dalilin hankali da na nakali da shuhudi zauki, abin da yake gudana cikin sanin yardar Allah da neman ta cikin tsololuwar girmama sha’a’ir da ibadojin Allah da dalilin hankali da na nakali, haka zalika yana gudana cikin raya girmama ta’aziyyar husainiyya, kamar yanda yake a tabbace cikin makarantar malaman ilimin Usul a Mazhabar Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata a garesu.
Ya zama dole ayi tsarkake niyya a tabbatar a na yini domin neman yardar Allah da yardar shugaban shahidai amincin Allah ya kara tabbata a gareshi, ka d amu sake mu dinga biyewa son rai sa sha’awe-sha’awe daga amawa da sunan raya ta’aziyarsa, lallai zahirinta ana yi don shi ne amma kuma wasu a badini suna yi domin kansu neda son zatinsu da jahilci, daidai yake da wanda yake bugun jikinsa domin Husaini (as) sai dai cewa kuma shi tareda haka zaka same shi yana raira wakokin wargi na haramun yana rawa yana Shewa da wakokin da basu halasta ba.
Ya zama tilas a hankalce da shari’ance duk mutumin d azai raya ta’aziyyar Husaini (as) ya nemi yardar Allah da yardar shugaban shahidai, kadai zai iya sanin haka cikin jumlar abin da ya tabbata a zamanin Gaiba Kubra ta hanyar sikeli da ma’aunan shari’a ta hanyar komawa wurin Maraji’an taklidi masu daraja Salihai, kamar yanda muka karbi fatawa daga garesu cikin yakar makiyanmu yan ta’addan salafiyya, haka zalika dole mu nemi fatawa cikin dukkanin wani abu na raya ta’aziyyar Husaini (as), Allah ya tsare kada mu je mu kasance daga cikin wadanda suke karya gadon bayan Sarkin muminai Ali da shugaban shahidai (as) bari dai muslunci da kur’ani da addini mabayyani sun rigaya sun bayyana a fili, lallai shi yana cewa: (mutane guda biyu sun karya bayana: maami da baya aiki da iliminsa da mai ibada da jahilci cikin jahilci) sau da yawa zaka samu jahili yana nemanh yardarm Allah da raya ta’aziyyar Husaini (as) cikin jahilci ba tareda ya koma wurin Maraji’ai ya nemi fatawa ba, bai san cewa yin hakan zai iya kai shi da karya gadon bayan Husaini mai daraja ba, ya zama ya tattake shi da kofutan dokin jahilcinsa a ranar goma ga muharram mai alfarma, sau da yawa mai karanta kur’ani yana karanta shi amma kur’ani na tsine masa, sau da yawa mai karanta hudubako mawaki ko mai rera waken wasu mawaka da kasidun Imam Husaini (as) amma Imam yana la’antarsa, nawa ne daga mai huduba a kan mimbari yake fadin abin da yake rusa addini da bakanta alfarmar shari’a tsarkakka, mawakin nawa ya fadi abin da ya fada daga cikinsa abin da akwai fushin Allah a cikinsa da Manzonsa da shugaban shahidai (as) cikin misalin abin da suke rerawa da yake kunshe da gullanci da shari’a take kyamarsa ta ke wurgi da shi daga abin da yake jawo la’ana kan mai fadinsa kan harshen Annabi da iyalansa amincin Allah ya tabbata a garesu.
Saboda haka kowa da kowa ya sani zai iya ta’aziya a zahirinta ta kasance daga ta’aziyar Husaini (as) daga wanda yake da’awarta sai dai cewa kuma a wurin masana da dandake ilimi ta zamanto an kirga daga ta’aziyar Yazidu (L) sakamakon ta ginu a kan jahilci da jahiliya kamar yanda Yazidu Ibn Mu’awita (L) ya jikkantu da ita.
Bayan haka ya zama dole a samar da wata lujuna karkashin kulawar Maraji’ai Salihai da zasu dinga yin bayanin hukuncin abin da ake dangantawa zuwa ga ta’aziyar Husaini (as).
Wurin Allah muke neman dacewa da damdagatar karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, ya Allah ka gaggauta bayyanar waliyinka ka bashi lafiya da nasara
(السلام عليك يا أبا عبد الله، وعلى الأرواح التي حلّت بفنائك، عليك مني سلام الله أبداً ما بقيتُ وبقي الليل والنهار، ولاجعله الله آخر العهد مني لزيارتكم، السّلام على الحسين وعلى علي بن الحسين وعلى أولاد الحسين وعلى أصحاب الحسين) الذي بذلوا مهجهم دون الحسين عليه السلام ورحمة الله وبركاته.
Amincin Allah ya tabbata a gareka ya baban Abdullah da dukkanin rayukan da suka halasci filin dagarka, amincin Allah ya tabbata a gareka daga gareni har abada tsahon raina da wanzuwar dare da rana, ka da Allah ya sanya wannan ziyara itace karshen alkawari gareka, amincin Allah ya tabbata ga Husani da Aliyu Ibn Husaini da `ya`yan Husaini da Sahabban Husaini wadanda suka sadaukar da rayukansu don baiwa Husaini kariya da rahamar Allah da albarkokinsa