b Ta wace hanya zan bi na isah ga malaman tarbiyya?
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ta wace hanya zan bi na isah ga malaman tarbiyya?

Assalamu alai kum
Ina rayuwa a kasar turai, sannan kamar yadda kuke da masaniya akwai hanyoyin shaidan da yawa awurin, ni kuma ina da alaqa da tsarkake zuciyata gashi bani da wani malami da zai taimakamin , sai dai nakan yawaita karanta littattafai daga internet amma hakan baya isa na, ina neman shawarar ku, wacce hanya ce zan bi na sami malami da zai taimakamin a wurin da nake rayuwa?

Da sunan Allah me rahama me jin kai

Fadin annabi Muhammad (saww) ma kawai ya isheka da yake cewa

أدبني ربي فأحسن تأديبي وأدبت علياً عليه السلام وعلي مؤدب شيعته

 wato Allah ya tarbiyyantar da ni ni kuma na kyautata tarbiyya ta, na tarbiyayantar da Ali (as) shi kuma shine me tarbiyyantar da shi’ar sa. Malami na farko  shine Allah madaukakin sarki sannan sai annabin sa, sai kuma amiral muminina Ali (as), don haka anemi taimako daga Allah ta hanyar addu’o’I sannan ayi tawakkali da shi, domin Allah shine Majibincin wadan da sukayi Imani, zai fitar da su daga duhu zuwa haske. Wato zai fidda su daga duhun duniya me gushewa, da son zuciya, da shaidanu da kuma Aljanu da mutane, sannan zai shigar da su cikin hasken rahama da kuma hasken irfani ta gaskiya sannan zai daura su ahanyar da zasu isah gare shi.

(فَمَنْ كَانَ يَرْجُوا لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا)

والله المستعان

Tarihi: [2016/11/18]     Ziyara: [1109]

Tura tambaya