b Wasiyyah zuwa ga me neman isa ga Irfani
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Wasiyyah zuwa ga me neman isa ga Irfani

Assalamu laikum
Ina neman isah ga hanyar irifani amma bani da wani masaniya akan ta kuma bani da wanda zai nuna min, ko zaku iya nunamin wasu ziki ko hanyoyi na shiga wannan hanya
?

Dan sunan Allah me rahama me jin kai

Wannan hanya ba kawai yawan zikiri da wuridi da kuma addu’o’I bane, damin yazo a hadisi cewa.

الدّاعي بلا عمل كالرامي بلا وتر wato me adduan da ba ya aiki kamar  me jifa ne da bashi da dutse.

Don haka dole ake hadawa da dabi’u da kuma ayyuka na gari kamar irin su hidima ga aluma musamman iyaye da kuma yan uwa da abokai, da kuma sa hannu cikin ayyukan alheri da ziyarar wuraren ibadu.

Da kuma halartar wuraren koya da koyarwa sannan da yin ayyukan tsarkake zuciya, da kuma tsaida dare irin su sallolin dare da yawaita yin ayyukan mustahabbi da barin makaruhi, da guje wa son zuciya tare da jahadil akbar da makamancin su.

Da wuce matakan irfani daban daban wanda sun kai matakai dari, mataki na farkon shine اليقظة والطلب da kuma jajircewa juriya da hakuri alokacin da ake bibyan wannan matakai, domin ba me iya jurewa sai mumini wanda Allah ya jarabci zuciyarsa.

والله المستعان
Tarihi: [2016/11/20]     Ziyara: [1050]

Tura tambaya