Taambayoyin karshe
- Hanyar tsarkake zuciya » Ni Dalibar ilimin addini ina fuskanta matsaloli masu tarin yawa da suke bijirowa kan hanya ta
- Hanyar tsarkake zuciya » Shin akwai wata `yar gajeriya kaifiyya la’ana da sallama cikin ziyarar Ashura
- Hanyar tsarkake zuciya » Bani da Malami ina kuma gashi ina son in yi suluki cikin hanyar irfani na bincika sosai amma ban samu abin da zai taimakani zuwa ga wusuli ba
- Hukunce-hukunce daban-daban » Wanne ayyuka ne da ayoyi ne zasu taimaka mini kan kubuta daga sihiri
- Hukunce-hukunce daban-daban » Barin karatun Hauza
- Hanyar tsarkake zuciya » ina fama da rauni himma da irada cikin al’amurra masu yawan gaske
- Hukunce-hukunce » Ko zaku iya gaya mana malamai da suka tafi kan juzu’iyyar shahada ta uku cikin kiran sallah
- Hukunce-hukunce » Mene ne hukuncin wanda yake rafkanwa cikin zikirin ruku’u da sujjada sai ya karanta na farko a muhallin na biyu ya karanta na biyu a muhallin na farko
- Hukunce-hukunce » Ladani yayi kiran sallah alhalin ina cikin jirgin sama lokacin da na isa garina zan rama sallah Kenan ko zan sauketa a kan lokacinta Kenan
- Aqa'id » Mene ne hukuncin limanci wanda bai tabbatar da cewa shi Adali bane tareda sanin cewa su masu binsa sallah suna Imani da adalcinsa
- Hukunce-hukunce » . Shin ya halasta a gareni na fara yin sujudush shukuri daga baya sai na yi sujudus Sahawu
- Aqa'id » Yanzu muna karshen zamani Kenan
- Hukunce-hukunce » Ya halasta mu kira Sarkin Muminai Aliyu bn Abu Talib (.AS) da lakabin shugaban Sufanci
- Aqa'id » shin soyayyar Ahlil-baiti tana kasancewa daga bangare daya
- Aqa'id » Wani ne yake cewa wai shi yana haduwa da Imam Mahadi A.F
Wasu daga cikin tambayoyi
- Hukunce-hukunce » Shin yin tattoo haramunne?
- Hukunce-hukunce » furucin kalmomin larabci a sallah
- Hukunce-hukunce » Tambaya atakaice: me yasa a musulunci akwai wurare da aka bada dama dukan yaro karami?
- Hukunce-hukunce » Shin yana halasta a yi taklidi da matacce
- Hukunce-hukunce » Idan wani mutum ya karbo sallar kwadago (sallar da ake biyanka don ka sauke bashin sallar wani mamaci da ake binsa bashinta) sai kuma ya bayar da ita ga wani domin yayi, idan wanda ya bawa yayi shin ta isar, idan ya saba ya biya wanda ya baiwa kasa da far
- Hukunce-hukunce daban-daban » Wadanne ayoyi wamda idan manzon Allah (s.a.w) ya ji ana karanta su sai ya fashe da kuka
- Hukunce-hukunce daban-daban » suka ga marja;iyya
- Hanyar tsarkake zuciya » Shin akwai wasu wuridai ayyanannu domin aurar da budurwa wacce ta samu jinkirin aure?
- Hanyar tsarkake zuciya » WANNE AIKI NE ZAI TAIMAKENI KAN KIYAYE FARILLA DA KAURACEWA HARAMUN
- Hukunce-hukunce » Shin rashin amincewar mahaifiya cikin aure yana zama sabawa iyaye
- Hukunce-hukunce » Shin ya halasta a gareni in sallah cikin masallacin Annabi da yin sujjada kan abinda baya halasta ayi sujjad a kansa
- Hukunce-hukunce » Shin komawa zuwa ga shaik wahidul Kurasani cikin mas’alolin ihtiyaɗi wujubi na sauke nauyin taklifi?
- Aqa'id » Wurida da suke kai mutum zuwa ga mukamin Arifai
- Hanyar tsarkake zuciya » Ina da `da mai tsananin fusata
- Aqa'id » Menene ma'anar fikra (tunani) cikin hadisi
Tambayoyin da akafi karantawa
- Hukunce-hukunce » Hukuncin istimna’i (yin wasa da al’aura) lokacin larura ga mata
- Hukunce-hukunce » Wadannan abubuwa ne ke zama alamun balaga ga `ya mace da namiji?
- Hadisi da Qur'an » ?menene fasarar suratul kausar
- Hukunce-hukunce daban-daban » Shin akwai wasu aiyuka da wuridi da mutum zaiyi domin samun aiki ko
- Hukunce-hukunce daban-daban » na fake da Allah da yawan istigfari da addu’o’i na kuma yi sallar neman arziki sai dai cewa abin bakin cikin tare da haka ban iya cimma muradina ba
- Hukunce-hukunce » Shin ya halasta mace ta hana mijinta ya sadu da ita a matsayin sa na wanda baya ruko da addini?
- Hanyar tsarkake zuciya » Shin akwai wani zikiri ko wani aiki da zai mini maganin yawan ciwon damuwa
- Hukunce-hukunce » MAI BARIN SALLAH
- Hukunce-hukunce daban-daban » Aslm Menene ma'anar Buriji
- Hukunce-hukunce » Wasiwasi kan alwala da wanka da kuma sallah
- Hukunce-hukunce daban-daban » Addu’ar gane barawo
- Hanyar tsarkake zuciya » Naso neman Karin bayani daga gareka kan azkar wanda kayi ishararsu cikin littafin ulumul garbiyya
- Aqa'id » MENENE ILLA CIKIN AUREN ALI DA FATIMA (AS) SHIN UMARNIN UBANGIJI NE
- Hanyar tsarkake zuciya » Gwajajjiyar addu’a da aka gwada domin samun daukar ciki da samun zuriya.
- Hukunce-hukunce daban-daban » Tambaya atakaice: ni da matata munyi jima'I muna dauke da azumi saboda haka menene hukuncin mu?.
salamu alaikum
da sannu zanyi maka bayani filla filla domin ka kewayu da ilimi da dukkanin abinda nake son kai mini bayani kai, ya shaik ina da wata tambaya da ta shafi makomar rayuwata da nake neman shawara kanta sannan dukkanin fatana yana gareku da ku taimaka mini da nusantarwa ga bangarorin batun domin in samu damar dogaro da shawarwarinku, sannan zanyi bakin kokarina zan kuma roki Allah madaukaki da ya sanya albarka cikin lokutanku domin darajar zahara(as).
An haifeni a shekara ta 1985 hijra miladiya inada mata guda daya da `ya`ya uku sannan ina aiki da matsayin injiniya cikin daya daga cikin kamfononi hako man fetur masu zaman kansu a kasar iraki sannan inada tsananin kwadayin karatun hauza a jamhuriyar muslunci ta iran a makarantar jami`atul Mustafa sannan matata batada wata matsala kan hakan bari ma dai tana karfafani kan karatun addini. Sannan kwadayin cikin karatun hauza ya kasance sakamakon wasu manyan dalilai guda hudu:
1- gyara kan kaina da abinda ilimi ke zama sanadin gyaruwarsa daga sanin wasu abubuwa da zama da malamai da daliban ilimin addini da rayuwa cikin duniyarsu koda ko zuwa wani gwargwado.
2- neman lada.
3 sanya iyalina su rayu cikin duniyar kishin addini domin ita kanta matata tana da kwadayi da shaukin neman ilimin addini sanna ita ma injiniya ce amma duk da hakan tanada kwadayin karatun hauza sannan babbar niyyata da izinin Allah shi ne samar da iyalin masu kishin addini bisa zabinsu ba wai da tilasawa ba kawai dai ta hanyar samar da yanayin da zai taimaka musu cikin wayar gari iyali masu lazimtuwa da addini da izinin Allah nima ina kwadayin zama mai bada darasi a cibiyoyin addini.
4- lalle inada tsananin shauki da kwadayin wannan ilimi saraina hakan ya kasance makomar wanda zan koyar ya zamanto mai kawo gyara cikin al`umma da amfanar da ita.
Manufata cikin fara wannan karatu bayan shekaru hudu kusa kusa da izinin Allah sannan cikin wannan shekaru hudu zan yi aiki in tara kudade domin idan nazo iran in ajiye kudaden a bankuna don inyi amfani da su a bukatuna na yau da kullum don nesanta daga kudaden taimako da maraji`ai ke baiwa dalibai a kowanne wata ba waida don ina kyamar taimakonba a a sai don in barwa mabukata su amfana domin su wadannan kudade na imam zaman (as) ne.
Sai dai kuma wani abokina ya bani shawara da in aje wannan tunani na karatun addini maimakon hakan kamata yayi in ciagaba da karatuna na zamani iran in dora kan zuwa digiri na biyu har zuwa digiri na uku (doktora) da wannan kudade da nake tunani amfani da su a karatun addini bayan shekaru hudu yana mai kafa mini dalili kan ra`ayinsa da cewa shekaruna sun ja na girma sosai sannan zan iya amfani da zamana a iran wajen yin nazarin littafan addini in kara samun ilimi da wayewa kan ilimin addini ba tareda na zauna a hauza ba domin ita hanya alheri da gyara ba ta takaitu da karatu a hauza ba kadai wanda na karkata zuwa gareshi, sakamakon wannan tunani na abokina sai na tsinci kai na cikin shakka da kokwanto kan wadanan abubuwa guda biyu wato kodai cigaba da karatun boko ko kuma karatun hauza, lalle cikin shawarwarin wannan abokina nawa akwai abubuwa masu kyawu akwai kuma akasin haka.
cikin tsayawa in kamala karatuna na boko ban iya tabbatar da wata fa`ida ta hakika ba tayiwu kawai bai wuce la`akari da ina da shaidar digiri kan injiniya ba domin a kasar dana nake ta iraki amfani karatun injiniyanci ina yake ina fa`idarsa take da zan iya hidimtawa jama`ata da shi a matsayin dokta wane kai idan ma akwai wata fa`idar to ba za a taba kwatanta da fa`idar da take cikin karatun addini ba, ta wannan fuskar Kenan, sannan ta wata fuskar ina tsorarma kaina cudanya da mata cikin zaurukan karatu a jami`o`in zamani a matsayin na dalibin da yake yunkurin kamala karatun ko kuma wanda ke shirin wayar gari malamin jami`a saboda ina da rauni gameda sha`anin mata(lalle shi mutum yana kan basira gameda kankin kansa)
saboda haka da mai zaku mini nasiha. Allah ya baku gwagwgwaban lada ina godiya..
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Ya kai wannan `dana nawa mai daraja kamar yadda ka sano kowanne aiki na da bangare mai kyawu da kuma kishiyarsa shi dukkkanin ma hankali da farko ya na kallon bangare mai kyawu sai ya dauki abinda ke cikinsa idan kuma babu a sai ya duba Tsakani yaga wane ciknsu yafi saukakar sharri, wannan Kenan bisa lissafin hankali da dalili sannan hukunci ya rage gareka domin kai kasan yadda kake rayuwa da abinda yafi dacewa ga rayuwarka lalle zamnani da wurin da kake rayuwa tushe ne wajen canja hukunci da kuduri da niyya sannan su mutane ba bai daya suke kowa da yadda yake cikin hukuncisa da tsare tsarensa.
Saboda haka shawara shine ka fara darasin batun daga dukkanin bangarorinsa da nahiyoyinsa lalle karatu a hauza kamar fure ne da ke dauke da kayoyi masu tarin yawa ta yiwu idan ka hango shi daga nesa ka ganshi tsurar fure sai dai cewa yayinda ka kusanto ka nemi tsinka mai yiwuwa kayarta ta sokeka harma ka fara tunanin hakura daga tsinkar furen, bari tayiwu ka munana zato ga wannan fure, gaskiya magana wannan shi ne abinda yake faruwa ga wanda ya shigo hauza lalle zaka same shi a farko farko yana cikin tsananin shaukinta sai dai kuma sakamakon cin karonsa da wasu ba`arin kayoyi suna iya kaishi ga `debe tsammani da bakantuwa da munana zato ga hauza da mutanenta da malaman cikinta daga maraji`ai, ba dukkanin wanda ya shiga hauza ya kutsa tafkinta ke tsira ba cikin iyo da yin nusto don fito da gwalagwalanta da ilimanta ba bari ma dai da yawa yawa sun nutse sun halaka, sannan haka al`amrin yake dangane da karatu a jami`a yana bangare mai kyawu da kuma akasinsa kishiyarsa.
Sai dai cewa ni abinda nayi Imani da shi cikin hauza da karatunta ta fuksar gamewa lalle ita hauza ita hanyace zuwa ga azurta duniya da lahira saboda haka ne ma na sanya `ya`yana guda hudu dukkaninsu cikin ahlin ilimi suka kuma zamanto `ya`ya ga hauza haka dukkanin surukaina daga hauza suke hakan bag a komai yake nuni ba face imanina ga ingancin hanyar da lamuninta ga farin ciki da azurtuwa koma bayan aiki da sana`a da wasu karatukan sabanin na hauza lalle su babu tabbas cikin gobensu ta yiwu su lamuntar da farin ciki da azurtuwa ko kuma akasinsa.
Daga ka karshe dai ina kara maimaici gareka da ka karanta yanayin sosai kada kayi gaggawa hakama kayi shiri na ruhi da ilimi kai da iyalinka saboda lallai ita hanyar hauza akwai tsanani da wahalhalu da surutai masu tarin yawa a kan hanyarta wadanda suke bukatar ketaresu takansu musammam a cikin kasar muslunci ta iran sakamakon banbancin wayewa da al`adu ta yiwu wata rana wani jahilin ba`iraniye ya nuna maka kabilanci wanda haka zai iya yi maka tasiri a mahangarka ta muslunci da rikonka ga juyin juya hali da jagoransa da imam komaini(ks) da wanda ke kan tafrakinsa.
Daga karshe idan ka yanke shawara tsakanin dayan biyun ma`ana tsakanin hauza da jami`a to ka dogara ga Allah lalle shine abin neman taimako dukkanin godiya ta tabbat ga Allah ubangijin talikai.
Daga cikin tambayoyin wanna sashin (Hanyar tsarkake zuciya)
- ME AKE NUFI DA ARWAHUL SAZIJA
- Harkokin samun abinci na da arziki na sun tsaya cak sun tabarbare me ya kamata in yi?
- neman izinin zikirin yunusa?
- Idan na nufi tafiya aiki Hajji shin wajibi ne kaina in ziyarci makusantana
- NA AIKATA WANI LAIFI DA NAKE JIN TUBANA DA ISTIGFARINA BA ZASU KARBU BA
- na karanta ziyarar Ashura har sau 40 amma bukata bata biya ba
- SHIN TASIRIN ZIKIRIN TAUHIDI YANA DAGA ABINDA AKA JARRABA SHI AKA GANSHI
- Mene ne asalin Du’a’u Sirril Mustauda’i fiha
- RASHIN SAMUN DACEWA A RAYUWAR DUNIYA
- Wasiyyah zuwa ga me neman isa ga Irfani