b Menene ceto? Menene iya haddinsa? Wanene ya cancanci ceto?
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Menene ceto? Menene iya haddinsa? Wanene ya cancanci ceto?


Menene ceto? Menene iyakokinsa? Wanene ya cancance shi? Daga karshe muna barar addu’a da ziyararku.

 

Menene ceto? Menene iya haddinsa? Wanene ya cancanci ceto?

ماهي الشفاعه ؟ وماهي حدودها ؟ ومن يستحق الشفاعه ؟ نسألكم الدعاء والزياره

Menene ceto? Menene iyakokinsa? Wanene ya cancance shi? Daga karshe muna barar addu’a da ziyararku.

 

Bismillahi rahmanir rahim

Shafa’atu  asalin Kalmar daga shaf’u ta ke kishiyar witru, shi witru yana da ma’anar abu guda daya kamar misalin sallar wutiri daga sallolin dare, shaf’au kuma da ma’anar biyu kamar misalin raka’a biyu ta cikin shafa’i, shafa’atu isdilahin kur’ani ne da riwaya kamar yadda yake wajen manya-manyan malaman mu tana da ma’anar taimakon ma’asumi da cetonsa ko kuma ceton wanda akaiwa izinin yin ceton tun daga waliyyai da salihai dangane da waninsu, idan ya zamanto ya yi kasa agwiwa ya takaita ya gaza cikin akinsa, misalinsa kamar misalin wanda yake hawa dutse, ya zama tilas ya hau sai dai cewa zai sha wahala zai iya tuntube da kafafunsa yaji ciwo ya fado, sai wani mutum ya zo ya tallafa masa kan mikewa da tabbata ko kuma ya tunkuda shi gaba, misalin wannan mutum da ya bashi tallafi ana kiransa da maceci, aikinsa da ya mike kansa kuma ana kiransa da ceto, to ranar alkiyama duk wanda ya takaita cikin aikinsa a duniya kamar misalin wanda ya zakkewa aikata zunubai ko ya takaita cikin wajiban da suka hau kansa da ibada, idan cto ya riske shi kamar ceton annabawa da wasiyyai da salihan da muminai maza da mata da izinin Allah matsarkaki madaukaki tabbas shi zai kasance sanadin tsiransa da kubutarsa daga kufaifayin zunubai  kamar shiga da tsananta azaba da tsayinta da makamantansu.
ranar kiyama kowa na jira da tsimayin ceton annabi mai girma, kai hatta annabawa suna fatan ceton manzon Allah mafi grima Muhammad mai ceton zunuban mu amincin Allah ya kara tabbata gareshi, hakika ya zo cikin madukakin hadisi

 (إدّخرت شفاعتي لأهل الكبائر من أمّتي)

Na ajiye cetona don masu aikata manya-manyan zunubai.

Wannan ludufi ne kebantacce ga al’ummar da ka jilanta, zahiri lallai shi ceto jin kai ne daga Allah matsarkaki ba wanda don cancanta ba, duk wanda ceto yah ado da shi ta hado da shi ne da ludufi da tausayi daga Allah bawai don cancantarsa ga hakan ba. Sau da yawa wasu karababbun ayyuka  kamar misalin ziyarartar imamai tsarkaka (as) na janyo cancantar samun ceto kamar yadda ya zo cikin zahirin hadisai haka ma kamar yadda ya zo cikin ziyarar maulana rida (as)

قال: (من زارني علی بُعد داري کنت أنا وآبائي شفعاءه یوم القیامة)

Duk wanda ya ziyarce ni daga nesa daga gidana ni da iyayena zamu kasance masu ctonsa ranar kiyama.

Hakika manya-manayan malamai daga jamhur din musulmai sun yi rubutu kan wannan janibi, kana iya komawa maktabatul islamiyya, ko maktabatul ahlul baiti daga intanet sakar yanar gizo da sannu zaka samu abin da zai kara maka abin da ka sani a baya gameda ceto, ta hanyar akwo maka ayoyi da riwayoyi da bahasussuka da darasussuka.

Wurin Allah ake neman dacewa da damdakatar.

 

Tarihi: [2017/8/23]     Ziyara: [1509]

Tura tambaya