b Harkokin samun abinci na da arziki na sun tsaya cak sun tabarbare me ya kamata in yi?
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Harkokin samun abinci na da arziki na sun tsaya cak sun tabarbare me ya kamata in yi?



Salamu alaikum
Na saurareka cikin daya daga muhadarorinka na bidiyo kana yin nasiha kan yin sallar neman arziki, lallai ni na lazimci wannan sallah da ka yi nasiha da yinta tun lokaci mai tsayi tsawon shekaru amma tare da babu abin da ya ce cikin tabarbarewa harkokin samun abinci na, kamar yadda lallai ni na lazimci ayyukan ibada masu tarin yawa kamar misalin ziyarar ashura da yaaita istigfari da karanta kur’ani da yin salloli kamar misalin sallar kun fayakun da sallar jafarul dayyar da sallar istigasa bil hujja cikin kowanne daren alhamis da juma’a karkashin sama kai hatta yin kuri’ar intigasa bil hujja ita ma na jarraba ta na jefa ta cikin kogi sannan dukkanin wanda na samu labaarin zai je ziyara mashad wajen imam rida (as) na kanyi masa wasiyya da ya yi mini adddu’a da sanya sunana tare da bukata ta cikin hubbaren amma duk da haka babu abin da na samu ya canja, sannan ni da kaina na ziyarci annabin Allah Muhammad almustafa (s.a.w) da fadima da imaman da suke kwance a baki’a (as) da ummul banin sannan gabanin watanni bakwai naje umara cikin watan rajab ban yi kasa agwiwa ba cikin yawaita addu’a na yi addau’a don samun canji cikin halin da nake cikia daren lailatul kadri sai dai fa duk da haka babu abin da ya sauya.
Abin da ya sanya ni rubuto maka wannan wasika lamarin ya wuce bakin iyakarsa bazan cigaba da juriya ba, sannan ina da `da da zai shiga makaranta sannan ya na bukatar kudin da zai biya makaranta da wadanda zai amfani da su sannan albashin babansa ba zai isa biyan kudaden makaranta ba da bukatun rayuwar yau da gobe saboda haka sayyid kai mini nasiha ka bani wani aiki na ibada da zan yi da zai fitar da ni daga wannan matsala da wahala ya bude mini kofar arziki na ya bayyanu cikin kusa-kusa

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

بسم الله الرحمن الرحیم

`yar`uwata mai daraja salamu alaikum wa rahamatullahi ahlil baiti wa barakatuhu ya zo cikin hadisil kudisi daga matsarkaki masani mai hikima mai ludufi mai tausayi da jin kai cewa tabbas shi ya ce: daga cikin muminai maza da muminai mata akwai wanda wadatuwa tafi zama maslaha da alheri gareshi sai nake sanya shi mawadaci domin da zai talautu da ya kafirce daga cikinsu kuma akwai wanda da talauci yafi dacewa da shi sai na sanya shi matalauci saboda soyayya ta gareshi dai zai wadatu da ya yi `dagawa ya kuma kafirce. Wannan kenan da farko na biyu kuma ya zo cikin hadisi cewa lallai Allah ya na jinkirta amsa addu’a har ya zamanto ya ji addu’ar da yawan gaske lallai shi ya na jin sautin bawansa ka da bawa ya zaci cewa bai son jin muryarsa bari ya zama dole ya yi farin ciki lokacin da ya ke Ambato na da yawan ayyuka nagari, tsakaninki da Allah da ace kin kasance cikin wadata da dukiya mai tarin yawa shin zaki dinga wadannan salloli na neman arziki tsawon wadannan shekaru da yawa da yawa haka da kuma ayyukan ibada misalin karanta ziyarar ashura da yawaita istigfari da kartun kur’ani da sallolin nafilfilu kamar yadda kika bamu labara, wannan ya na nuni kan cewa Allah ya na sonki ya na kuma kusanto da ke zuwa gareshi cikin wannan kuntatawar. Ashe bai daga cikin siffar mumini da mumina wasicci da hakuri, me ya sanya Allah ya yi miki wasicci da yin hakuri ai saboda shi hakuri rabin imani ne ita kuma godiya daya rabin ki kasance mai hakuri mia godiya ga Allah kiyi farin ciki da kasancewa haka bawai ki dinga kokawa daga gareshi, lallai yadda lamarin yake shi ne mafi yawaitar wilaya da kusanci daga cikinku shi ne mafi yawan bala’I daga cikinku, sannan daga cikin mafi girman bala’i talaucida kunci da kuntatuwa  da bakin ciki da damuwa, kadai annabawa da waliyyai da salihai ba sukai ga mukamin kusantar Allah ba face da talauci ba wai da wadatuwa ba, sannan yawancin annabwa da waliyyai da saliahi sun rayu talakawa, ki karanta rayuwar malamai da arifai don ki san yaya suka rayu cikin talauci, babban malaminmu sayyid mar’ashi najafi (k’s) wata rana ya ce mini da na kasance ina cikin azumi azumin kwadago sannan ina da aure ina kuma da `da bai da kudi sai na ke sayo gurasa da nono don iyalina sai ince ni bako ne bai halarato da tunace tunace sai in yi buda baki da ruwa sai in kaddara cewa ni bakon ssayyada Fatima ma’asuma (as) ne ya kara ce mini ya sassauya gidan haya har karo talatin da bakwai  ya ce mini shi tsawon rayuwarsa `dan haya ya rayu tarda cewa shi ya kasance ya na rike da marja’iyyar shi’a mai girma ya zama wajibi muyi koyi da wadannan bayin Allah salihai shin yanzu bayan wannan zaki cigaba da kokawa kan talauci da kuncin rayuwa ki godewa Allah ubangijin talikai kamar yadda ya cancanci godiya a kowanne hali ki yarda da arzikin da ya hukunta kanki sai dai cewa tare da haka ki lazimci arzikinki da akai miki alkawari ki roki Allah daga falalarsa, sannan kina iya komawa abin da  na rubuta cikin wannan babi cikin littafin (nurul afak fi ma;arifatul arzak) an buga shi an kuma sauke shi a ya nar gizo (internet) a adisrhin alawy.net

Allah ne abin neman taimako ku dawwama cikin alheri
Tarihi: [2017/11/2]     Ziyara: [1973]

Tura tambaya