Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Shin akwai wani aiki na ibada da zai kai mutum ya zuwa samun wata daraja da cimma muradi
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin akwai wani aiki na ibada da zai kai mutum ya zuwa samun wata daraja da cimma muradi

Salamu alaikum
Fiye da shekaru goma na haramtu daga samun mukamin aiki an farlanta wasu sharudda wadanda sukai kamada abinda dama ya fi karfin ikon bil adama shin ko akwai wasu ayyukan ibada da zasu isar dani zuwa ga samun daraja da cimma burina kebantacce tabbas haramtuwarmu daga samun Karin matsayi da daraja ya haifar mana da haramtuwa Karin albashi aiki.
Allah ya saka muku da alheri alfarmar kakarku fadima (as) kada kuyi mana rowar falalar da Allah ya kwarara muku.

بسم الله الرحمن الرحیم

`dan’uwana mai girma wane ne ya gaya maka cewa karin mukami da Karin albashi shi ne maslaharka lallai Allah matsarkaki shi ne cikin maslaharka sau da yawan lokuta mumini talauci yakan fi zama maslaha da alheri gareshi da zai wadatu da ya yi dagawa ya kuma kasancewa daga hasararru, na wane daga cikin muminai da suka samu kudade da Karin albashi da alfarma da mukami sai gashi sun kasance sun canja sun sauya wadanda da suna halartar sallah cikin jam’i cikin kowacce rana  sai gashi sun dawo basu halarta sai sati-sati  kai bari sai wata-wata  har ta kai ga sai shekara-shekara  shin dukiyar ta amfanar da su da Karin mukamin aiki, me ya sanya ba zaku fawwala lamarinka ga Allah ba me ya sanya ba zaka sallamawa hukuncin Allah ba da kaddararsa, na’am ku roki Allah falalarsa

     

وقل ما يعبأ بكم ربكم لولا دعائكم

Ka ce ubangijinku bai damu da ku ba don addu’o’inku ba.

Sai dai cewa sa’ailin da ka ke nema fiye da shekaru goma me haka ke nufi me yasa baka nemi  ziyarar dakin Allah mai alfarma ba aikin hajji tsawon shekaru goma da saduwa da shugabanmu sahibul asri waz’ zaman  amincin Allah ya kara tabbata gareshi, me ya sanya tsawon shekaru goma baka nemi kasantuwa daga waliyyan Allah ba matsarkaki sai darajar imaninka da iliminka wajen Allah matsarkaki su daukaka, matsarkakin sarki cikin littafinsa ya na cewa

 (يرفع الله الذين آمنوا والذين اوتوا العلم درجات)

Allah ya na daukaka darajojin wadanda sukai imani da wadanda akai baiwa ilimi.

me ya sanya baka tunanin daukakar darajarka ta ilimi wannan ilimi da ke yardar da ubangijinka ya yardar da annabinka ya yardar da ahlil baiti ya yardar sahibus zaman (as) tare da haka ka lazimci yin zikiri kowanne lokaci tabbas shi kowanne lokaci yana tasiri cikin halin da kake ciki na zahiri da badini da izinin Allah madaukaki  

 (حسبنا الله ونِعَم الوكيل نعَم المولى ونعم النصير).

Allah ya isar mana madalla da wakili madalla da majibanci madalla da mai taimako

(أفوض أمري إلى الله أن الله بصير بالعباد)

Ina fawwala lamari na ga Allah lallai Allah masanin bayi ne

Allah ne abin neman taimako
Tarihi: [2017/11/2]     Ziyara: [881]

Tura tambaya