mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ta yaya zan iya yin hadayar salla ga `yan’uwana makusantana?


Salamu alaikum

Ina da `yan’uwa guda biyu amma duka su biyun ba suyin salla `daya cikinsu inkarin sallar yake bai yi ma imani da ita ba `dayan kuma bai yin sallar hakika nayi nasiha a na farko wanda yake inkarin salla sai dai cewa ya kafe kan ra’ayinsa bai yaki sauyawa.
Menene taklifin da ya hau kaina na shari’a dangane da su.. tabas na karanta wani hadisi daga manzon Allah amincin Allah ya kara tabbata gareshi da iyalansa yana cewa : ku yiwa yahudawa da nasara sallama amma kada ku yiwa yahudawan cikin al’ummata sallama sai aka tambayi manzon Allah (saw) su wanene yahaudawan cikin al’ummarka sai yace mai barin salla.
Ku fa’idantar damu Allah ya saka muku da alheri

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya kamata ka ta maimaita yi musu nasiha da tausasa musu lafazi kamar yadda Allah ya gayawa abokin maganarsa musa (as) da ya je wajen fir’auna

 (فَقُولا لَهُ قَوْلًا لَيِّنًا لَّعَلَّهُ يَتَذَكَّرُ أَوْ يَخْشي)

Ku gaya masa zancen tausassa saransa ya tunatu ko yaji tsoro.

Sannan ka dinga motsa masa dabi’arsa ta hanya buga masa misalai., misali da ace za ai maka kyauta wata kyauta kamar misalin kyamara (injin daukar hoto) me zaka y ? da sannu zai ce maka zan gode masa sai kace masa idan kuma baka gode masa ba fa zai ce ni na zama `kasan dabba da mafi `bata daga gareta  saboda hatta kare idan akai masa kyauta da kashi lallai zai godewa wanda ya bashi kashin ta hanyar karka`da jelarsa, a wannan lokaci sai kace masa ashe ba Allah ne ya baka id oba wanda ya fi girmama daga kyamara (injin daukar hoto) lallai shi ido na daukar hoton miliyoyin hotuna masu launi-launi ya aikasu zuwa kwakwalwarka  kwakwalwarka ta ajiye su ta kiyayesu ta yaya ba zaka godewa wanda yayi maka kyauta da wannan babbar kyautar ba, da sannu zai ce maka ina gode masa da abin da na sani, kace masa kai baka san girman wanda ya yi maka kyauta ba shi ne Allah baka san yadda ya kamata kai masa godiya ba ma ‘ana godiyar data dace da shi wacce yake yarda da ita daga gareka, Allah yana sanarka da kai yadda ya kamata ka gode masa sai ya wajabta maka salla domin ka kasance mai godiya ga ni’imarsa wacce ya ni’imtaka da ita wacce ba zata kirgu kuma ba zat iyakantu ba, a wannan lokaci idan bakai salla ba shin kai kuwa mutum ne ko kuma kafi `bata daga kare daga dabbobi hanya ?  

Cikin mu’amalarka da wadannan makusanta naka da basa yin sallah ka kudurci cewa kana neman kusanci da Allah cikin shiryar da su kada ka damu da `batan da suke kai daga hanya mikakka kamar yadda wasu jahilai suka gayawa musa da isa kan addininsu, bari dai

 (وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ)

Duk wanda ke neman addini koma bayan muslunci ba za’a karba daga gareshi ba sannan shi ranar lahira yana cikin hasararru

 (یَآ أَیُّهَا الَّذِینَ ءَامَنُواْ قُواْ أَنفُسَكُمْ وَأَهْلِیكُمْ نَاراً وَقُودُهَا النَّاسُ وَ الْحِجَارَةُ عَلَیْهَا مَلاَئِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَّا یَعْصُونَ اللَّهَ مَآ أَمَرَهُمْ وَ یَفْعَلُونَ مَا یُؤْمَرُونَ)

Ya ku wadanda sukai imani ku tseratar da kanku da iyalanku daga wuta wacce makamashinta mutane da duwatsu kan akwai mala’iku masu tsanani da kausasawa basa sabawa Allah abin da ya umarce su suna aikata abin da aka umarce su da aikatawa.

Wadacananka shi ne wa’azi mai kyawu

 (ادْعُ إِلَى سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ وَجَادِلْهُمْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنْ ضَلَّ عَنْ سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ)

Ka yi kira zuwa ga hanya ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyawu kayi jayayya da su da abin da yafi kyawu tabbas ubangijinka shi ne mafi sani da wanda kaucewa hanyarsa kuma shi ne masanin shiryayyu

Allah ne abin neman taimako

 

Tarihi: [2017/11/7]     Ziyara: [853]

Tura tambaya