b Shin akwai wasu wuridai ayyanannu domin aurar da budurwa wacce ta samu jinkirin aure?
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin akwai wasu wuridai ayyanannu domin aurar da budurwa wacce ta samu jinkirin aure?

Salamu alaikum
Shin akwai wasu wuridai ayyanannu da za a iya yiwa budurwar da ta samu jinkirin aure?
Haka ma neman haihuwa da neman aikin y?
Alhamdulillah ni na fara yin sallar neman arziƙi wacce ku kayi wasicci da ita na kuma ga tasirinta mai kyawun gaske a yanzu kam abubuwa masu yawa sun saukaka gareni godiya gereku daga karshe muna rokon addu’arku.

 

da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai

an aiya yin dukkanin zikiri tare da iklasi kai musammam ma zikirin (Allahu) tabbas shi yana daga ismul a’azam lallai shi yana buɗewa kullallun abubuwa lallai yadda lamarin yake shi ne zunuban mu suka kulle mana kofofin sammai har ya zama an tsare addu’a kamar yadda ya zo cikin du’au kumail

 (واغفر لي الذنوب التي تحبس الدعاء وتنزل البلاء وتغير النعم وتنزل النّقم و.. )

Ka gafarta mini zubai wadanda suke tsare addu’a suke saukar da bala’i suke canja ni’ima suke saukar da ukuba.

Mafificin makullin shi ne tuba da neman gafara ba da yawaita addu’a, duk wanda ya kwankwasa kofa yayi kuma naci zai shiga

Ka da kayi kasala da sanyin jiki cikin neman rahamar ubangijinka da ni’imarsa tabbas yayewa yana kusa-kusa, ashe asuba ba kusa take ba, Allah zai yassare maka lamurra ka aurar da budurwar da kyakkyawan namiji mutumin kirki salihi kuma Allah ya azurta su da zuriya saliha da izininsa madaukaki.

 

Tarihi: [2017/11/8]     Ziyara: [1585]

Tura tambaya