b Shin zai yiwu mutum ya rarraba taklidi cikin mas’alar auren mutu’a idan ya kasance wanda yake taklidi da shi ya sanya sharadin neman izinin matarsa cikin halin auren mutu’a da wacce ba musulma
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin zai yiwu mutum ya rarraba taklidi cikin mas’alar auren mutu’a idan ya kasance wanda yake taklidi da shi ya sanya sharadin neman izinin matarsa cikin halin auren mutu’a da wacce ba musulma

Salamu alaikum ni ina daga cikin masu yin taklidi da sayyid Ali Sistani (dz) kuma ina da aure sannan mata ta yi imani da takaitawarta da gazawarta musammam cikin saduwa da juna sannan ni ban samu dacewa samun mace musulma da zan yi auren mutu’a da ita ba, sannan na samu damar yin auren mutu’a da kirista sai dai cewa lokacin da na duba fatawowin sayyid Sistani sai naga ya shardanta neman izinin mata ta musulma, sannan ni ina da yakini idan nayi ganganci sanar da ita da neman izininta to rayuwar aurena da ita ta zo karshe, Allah ne shaida cewa ni tsahon shekaru goma ina cikin wannan matsala sannan ban samu dacewa da auren mutu’a da musulma ba, shin cikin wannan mas’alar ya halasta in yi taklidi da wani marja’in

 

Nasiha ta gareka shi ne ka roki Allah cikin kowanne lokaci cikin alkunut sallolinka da ya sanya sha’awarka cikin soyayyarsa da zikirinsa, tabbas duk wanda ya debe haso da Allah zai samu rashin nutsuwa da mutane kamar yadda ya zo cikin riwaya daga imam hassan askari amincin Allah ya kara tabbata gare shi. Cikin kowanne lokaci ka dinga fadin:

 (اللهم اجعل شهوتي في حبك وذکرك وتلاوة کتابك وعبادتك)

Ya Allah ka sanya sha’awa ta cikin soyayyarka da zikirinka da karatun alkur’ani da ibadarka.

A wannan lokaci zaka tsira daga yawan sha’awar mata da yawan tunani kansu hakan shi ne mafi girma daga al’aurarka da farjin mata ka dinga yawan tunani cikin mutumtakarka, da cewa lallai kai ta wacce hanya zaka kasance halifan Allah cikin kyawawan sunayensa da madaukakan siffofinsa, lallai shi mumini sha’awarsa a mace take har ta lokacin da yake saduwa da matarsa bai saduwa da ita don bukatar kansa sai don bukatarta da gamsar da ita sai ya zama ya samu yardar Allah da hakan   

Tarihi: [2017/12/20]     Ziyara: [953]

Tura tambaya