b Ya za ai da macen da tayi watsi da yin aure saboda fakewa da wani dalili
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ya za ai da macen da tayi watsi da yin aure saboda fakewa da wani dalili


Ina da wata `yar’uwa wacce takai shekaru 27 tana aiki matsayan mai koyarwa a daya daga cikin ma’aikatun daula, kuma ita mai riko da addini ce da dukkanin ma’anar riko da addini, sai dai cewa ta ki yarda tayi aure da fakewa da hujja cewa ita kwata-kwata ba ta ma tunanin aure yanzu ta yanda al’amarin ya kai ga ba ma ta son sanin sunan wanda ya zo baiko da neman aurenta, ina fatan sayyid Adil-Alawi zai bani wata nasiha da zan mata da zatai mata tasiri a zuciyarta da abin da ta ke rayawa sakamakon kasantuwarta yarinya ma’abociyar riko da addini

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya isar a wannan mukami mu zo da wasu ba’arin hadisai daga Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata gare su sai su zama su ne amsa gareka da yar’uwarka mai girma

 

عن الرضا عليه السلام قال :( إن إمرأةَ سألت أبا جعفر عليه السلام فقالت :أصلحك الله إني متبتلة فقال لها : وما التبتل عندك؟ قالت لااريد التزويج أبداَ ، قال: ولم.؟ قالت: ألتمس في ذلك الفضل

An karbo daga imam rida amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: wata mata ta tambayi Abu Jafar amincin Allah ya kara tabbata gare shi sai tace: Allah ya yi maka gyara lallai ni mace ce wacce ta yanke zuwa ga Allah sai ya ce mata: menene yankewa a wajenki? Sai tace: bana son yin aure har abada, ya ce: maene ne ya sanya haka? Sai tace ina neman falala da yin hakan.

 فقال : انصرفي فلو كان في ذلك فضل لكانت فاطمة عليها السلام  أحق به منكِ ،إنه ليس أحد يسبقها الى الفضل).  فكما أن  امير المؤمنين عليه السلام  ميزان الاعمال وبه تقاس أعمالنا ، كذلك  فاطمة الزهراء عليها السلام  فهي ميزان الاعمال والافعال ، فإنها كفؤ امير المؤمنين عليه السلام ، فالعزوبة والتبتل لايوجبا الفضل والكمال.

Sai ya ce: tafi ki bawa mutane wuri da ace akwai wata falala cikin hakan da Fatima ta kasance mafi cancanta da yin hakan daga gareki, lallai yadda al’amarin yake shi ne babu wani wanda ya gabace ta cikin falala, kamar yadda lallai ya kasance sarkin muminai Ali (as) shi ne ma’aunin ayyuka lallai ita Fatima ita ce tsarar sarkin muminai Ali (as). gwauranci da yankewa bai kawo falala da kamala.

 وقال (صلى الله عليه وآله وسلم) : النكاح سنتي فمن رغب عن سنتي فليس مني .وعنه ايضا: (من تزوج فقد اُعطي نصف العبادة). وقال (صلى الله عليه وآله وسلم): (ما بني في الاسىلام بناء أحب الى الله عز وجل أعز من التزويج).

Ya ce: aure sunnata ne duk wanda ya kyamaci sunnata bai daga gare ni, haka ma an karbo daga gare shi: duk wanda ya yi aure hakika an bashi rabin ibada. ya ce; ba a gina wani abu a muslunci mafi soyuwa wajen Allah mai girma da daukaka ba daga aure.

Da wasu da yawa yawan riwayoyi da suka gangaro cikin wannan mukami daga karshe muna rokon Allah ya azurtaku da taufiki   

 

 

Tarihi: [2017/12/30]     Ziyara: [917]

Tura tambaya