mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shiga yakin da ake a kasar siriya tareda banbantar ra’ayin sayyid sistani da sayyid Ali kamna’i

الجهاد
Salamu Alaikum
Ni ya kasance ina da akida cikin yakin saboda kare martabar mazhaba da kuma muslunci da sura ama, matukar dai hadafina shi ne muslunci a bayyane yayin da naga sayyid kamna’i yana goyan bayan shiga yin yaki a siriya sai na shirya tsaf don in sadaukar da kaina don kare mazhaba. Sai dai cewa na bincika wajen sayyid sistani sai ya zamanto ban samu kowanne irin goyan baya ba daga gare shi, ni dai yanzu na wayi gari bana taklidi da kowanne marja’i saboda duk sanda na nufi fita jahadi sai mutane su dinga ce mini: ai sayyid sistani bai goyi baya ba. idan nayi niyyar taklidi da sayyid kamna’i kan zuwa jahadi siriya da iraki, sai mutane suce mini sayyid sistani ya fi shi ilimi, ni yanzu duk na rikice
Ok idan sayyid sistani ne mafi ilimi to me yasa cikin fatawarsa bai bayani ko sharhi kan zuwa jahadi siriya ba, ni dai yanzu ban san wane ne mafin ilimi cikin su biyun ba da zan taklidi da shi, sakamakon sanin cewa mafi karfafar maraji’ai a wannan lokaci da za ai taklidi da su sune sayyid sistani da sayyid kamna’i

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Wannan hiyali da tunani dukkaninsu lalatattu ne, ka bincika wane ne marja’i ta hanyar da shari’a ta tanada don yin taklidi da shi kamar misalin shaidar adalai biyu, idan hakan ya tabbata kada ka batawa kanka lokacin kan wane baya fatawar zuwa jahadi wane yana fatawar zuwa jahadi, kai dai kawai kayi aiki da fatawarsa zai sauke maka nauyin da ya rataya kanka, idan fatawar ta kasance dai a hakika yanada lada biyu, idan kuma yayi kuskure yana da lada guda. Muhimmi kai dai kayi aiki da abinda ya wajabta akanka, kada ka kasance cikin gigita lallai shakka da gigita suna daga aikin shaidani da rundunarsa daga mutnae da aljannu, dukkanin maraji’a kan gaskiya suke bayan tabbatuwar halascin yin taklidi da su ma’ana wadanda suka cika sharuddan yin taklidi da su, babu banbanci kan sunyi fatawar jahadi ko kuma basu yi ba.

Allah ne abin neman taimako

 

Tarihi: [2018/1/16]     Ziyara: [711]

Tura tambaya