b Idan wani mutum ya karbo sallar kwadago (sallar da ake biyanka don ka sauke bashin sallar wani mamaci da ake binsa bashinta) sai kuma ya bayar da ita ga wani domin yayi, idan wanda ya bawa yayi shin ta isar, idan ya saba ya biya wanda ya baiwa kasa da far
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Idan wani mutum ya karbo sallar kwadago (sallar da ake biyanka don ka sauke bashin sallar wani mamaci da ake binsa bashinta) sai kuma ya bayar da ita ga wani domin yayi, idan wanda ya bawa yayi shin ta isar, idan ya saba ya biya wanda ya baiwa kasa da far

Ina da tambaya gameda sallar kwadago, idan kwadagon ya kasance da sharadin cewa shine wanda aka fara bawa ne zai yi da kansa amma tareda haka sai ya mika sallar ga wanin mutum daban don yayi sannan shi mutum ya yi shin tana isarwa ko da kuwa ya saba ya biya shi kasan da farashin da ya karbo sallar kwadagon tun fari tareda cewa ya san ta kebance shi ne kadai bai halasta ya baiwa wani yayi amma kuma ya saba ya bayar, to mene ne hukuncin sallar shin tana isarwa idan aka samu tabbacin anyita?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Idan kwadagon an bada da yanayin kebantuwa, to bai inganta ya baiwa wani daban face da izinin wanda ya bashi kwadagon sallar, idan kuma ta kasance da yanayi rashin sharadi da kebanci, to ya halasta ya baiwa wani ya yi ko da kuwa da kasa da farashin aka biya shi tun fari, alal misali sai ya fara yi ta tsahon sati guda sannan ya baiwa wani ya cigaba koda kuwa da kasa da farashinsa.

Allah ne masani.

Tarihi: [2018/1/21]     Ziyara: [1072]

Tura tambaya