mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Karo da juna tsakanin ka’idar dake cewa duk wanda yayi ijtihadi ya dace yanada lada guda biyu, idan kuma ya kuskure yanada lada daya da kuma hadisin imam Sadik amincin Allah ya kara tabbata gare shi.


Salamu Alaikum
Mene ne ra’ayinku kan ka’idar dake cewa:
(( من اجتهد فأصاب فله اجران ومن اخطا فله اجر واحد ))
Duk wanda yayi ijtihadi sai ya dace to yanada lada gudfa biyu, idan kuma ya kuskure yanada lada guda daya
Shin wannan ka’aida tana sabawa hadisin da ya gangaro daga Abu Basir fadinsa:

(( قلت لأبي عبد الله عليه السلام : ترد علينا أشياء ليس نعرفها في كتاب الله ولا سنة فننظر
فيها ؟ فقال : لا ، أما إنك إن أصبت لم تؤجر ، وإن أخطأت كذبت على الله عز وجل )) الكافي
na cewa baban Abdullah amincin Allah ya kara tabbata gare shi: wasu abubuwa na gangarowa garemu wadanda bamu sansu cikin littafin Allah da sunna, shin zamu yi duba cikinsu ne: sai imam yace: a’a, amma kai koda ka dace cikinsu to baka da lada, idan kuma ka kuskure to kayiwa Allah mai girma da daukaka karya. Alkafi.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Akwai banbanci tsakanin waccan ka’ida da kakawo da madaukakin hadisin Abu Basir, lallai shi wannan hadisi na karkata zuwa ga kiyasi lalatacce a mazhabarmu wato irin kiyasin Abu hanifa, sai dai cewa ka’idar tana karkata zuwa ga ijtihadi da mujtahidi wanda ke wahalar da kansa don ya tsamo hukunci daga dalilanta na filla-filla, a wannan lokacin idan ya dace to yanada lada biyu saboda ya wahalar da kansa ya kuma ya dace da abinda yake a hakika a tabbace, idan kuma ya kuskure to yana lada guda sakamakon wahalarsa, sai dai cewa ita wannan ka’ida ta samo asali ne daga Ahlus-sunna wal’jama’a sun samar da ita ne don gyara kurakuren da halifofin zalunci daga cikinsu Mu’awiya kai har da yazidu bn Mu’awiya Allah ya dawwamar da su cikin hawiya, sai dai cewa an rungumeta bisa kebanta da sharadin ijtihadin ya kasance ingantacce a kuma kan gaskiya, ka’idar daga nahiyar kubrawiyya bata da matsala kadai sabani cikinta yana nahiyar sugrawiyyat,

Ingantacciyar magana shi ne idan mujtahidin gaskiya ya dace da hukuncin Allah to yana lada idann  kuma yayi kuskure babu laifi kansa.

Allah ne masani

Tarihi: [2018/1/22]     Ziyara: [763]

Tura tambaya