mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ya zanyi in kuɓuta daga zunubai?

Salama Alaikum
Sayyid lallai zuciya mai yawan umarni ce da mummuna face wanda Allah ya ji ƙai.
Sayyid lallai zunubai sun mamaye ni na kasa taka musu birki kowanne lokaci ina fadin da zan tuba sai kuma daga bayan in koma kan abinda na bari.
Sayyid don alfarmar kakanka Husaini kai mini addu’a da samun shiriya da gafara da watsi da aikata sabo, lallai ni bana iya yin bacci cikin nutsuwar zuciya alhalin ni ina zakkewa zunubai.
Sayyid yanayin tattalin arziki bai bani damar yin aure ba da zan iya katange kaina da kareshi, kai mini addu’a da Allah ya bani mace ta gari
Was salam.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai

 

Ina roƙa maka Allah da ya sauƙaƙe maka al’amarin aure cikin nasara insha Allah, sannan kada ka ɗebe tsammani daga rahamar Allah matsarkaki lallai shi mai yawan gafara ne mai kuma karɓar tuba ko da kuwa ka aikata adadin zunuban mutanen farko da mutanen karshe kai da adadin digon ruwan tafkuna da taurarin sama.

Tarihi: [2018/2/5]     Ziyara: [917]

Tura tambaya