b Wacce rana ce za ta kasance ranar farko ga watan Ramadan mai albarka mai zuwa na wannan shekara ta 2018?
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wacce rana ce za ta kasance ranar farko ga watan Ramadan mai albarka mai zuwa na wannan shekara ta 2018?

Salamu Alaikum
Don Allah ku sanar damu ranar farko da watan Ramadan ami albarka zai kasance cikin wannan shekara ta 2018
Muna godiya gareku kan abinda kuke sadaukarwa ga muslunci da musulmai ina kara godiya bisa bada loakcin mai tsada da kukayi wajan karanta waikar tambaya ta, Allah madaukaki ya dawwamar muku da taufiki.
Daga karshe gaisuwa ta ga samahatul Ayatollah Sayyid Adil-Alawi Allah ta’ala ya kare mana shi ya kuma sanya mana shi ajiya da taska ga musulmai da muslunci.

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai

 

Sanin ranar da zata kasance farkon ramadan mai albarka kaɗai ya rataya da sama da ganin jinjirin wata kamar yadda ya zo cikin hadisai masu daraja :

 (صم للرؤية وأفطر للرؤية)

Ka dau azumi idan anga wata ka kuma buɗa baki idan anga wata.

Saboda haka ka jira nima ina tareda ku cikin masu jira da sauraro.

Allah ne abin neman taimako

Tarihi: [2018/2/5]     Ziyara: [934]

Tura tambaya