b Yawan wasiwasi a cikin sallah da mafita?
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Yawan wasiwasi a cikin sallah da mafita?

Yawan wasiwasi a cikin sallah da mafita?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya kamaceka ka lazimci yin addu’a da tawassali da tawakkali ga Allah da yawan neman taimako daga gareshi kan sharrin iblis da rundunarsa, lallai daga cikin rundunar iblis akwai wasiwasi.

(wanda yake wasiwasi cikin kirajen mutane) suratu nasi :5

Iradar mutum karfaffa wacce take galaba kan makiyi wanda shine shaidan.

(lallai kaidin shaidan rarrauna ne) nisa’I;76

Sai dai cewa wanda ya jarrabtu da yawan yin wasiwasi kaidin shaidan ya ninninkawa kansa ta yadda a wannan lokacin shi ke galaba kansa sai ya jarrbau da ciwon wasiwasi.

Haka ma cikin mujarrabat ya zo da zai bar wasiwasi karo uku cikin buwaya, to lallai shidan zai nesance shi kamar yadda la,arin yake cikin jifan shaidan a mina cikin ayyukan hajji cikin kwanaki uku da suke jere da juna sai shaidan ya rushe rugu-rugu cikin karfin Allah da tsiminsa.

Kamar yadda ya kamaceka da’iman ka rungumi karanta wannan addu’a musammam ma cikin alkunut

أعوّذ بالله القويّ من الشيطان الغوي ، وأعوذ بمحمّد الرضيّ من شرّ ما قُدِّر وقضى ، وأعوذ بإله الناس من شرّ الجِنَّة والناس أجمعين

Ina neman tsari da Allah mai karfi daga sharrin shaidan batacce. Ina neman tsari da muhammad yardajje daga sharrin abin aka kaddara da da hukuntawa, ina neman tsari da abin bautar mutane daga sharrin aljannu da mutane baki dayansu.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2018/2/10]     Ziyara: [1632]

Tura tambaya