b Ina jin rauni lokutan sallah da addu’a kai kace akwai wani hijabi da shinge da suka katange zuciyata daga riskar debe haso da jin dadi daga garesu
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ina jin rauni lokutan sallah da addu’a kai kace akwai wani hijabi da shinge da suka katange zuciyata daga riskar debe haso da jin dadi daga garesu


Assalamu Alaikum
Allah ya daukaka ku hakikata ni inada karancin azama da himma ina kuma da yin sako-sako da sakaci matuka da al’amuran ibada, al’amarin na damu matuka duk sanda na yunkura na yi kokari cikin sauyawa da samun azama da himma bana samun nasara kan hakan.
Al’amari na biyu kuma shine ina jin rauni da nauyin jiki lokacin sallah da addu’a kai kace a kan zuciyata akwai wani hijabi ko shinge da suke katangeni daga barin samun debe haso da jin dadin ibada.
Ina fatan addu’a daga samahatus sayyid Adil-Alawi (h).

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Babu kokwanto cikin kasantuwar dukkanin wani ma’aluli yana da illa haka dukkanin wani sababi yanada musabbabi cikakke shine samuwar muktazi (abinda ke hukunta samuwarsa) da kuma rashin samuwar shinge hijabi da zai hana afkuwarsa, lallai azama kan neman ilimi abu ne mai amfanarwa sannan aiki nagari da jin dadin cikinsa yana dogaro ne kan samuwar muktazi ga azama wanda shine soyayyar Allah da kaunar samun kusanci zuwa gareshi da ganin kyawunsa da girmamarsa cikin littafinsa da halittunsa da cikin zababbunsa Muhammad da iyalansa amincin Allah yak ara tabbata garesu, sannan share fagen soyayya na cikin watsi da aikata zunubai da halaye marasa nagarta wanda wannan na hannun mutum wanda yake da cikakken zabi, daga nan kuma sai kasance cewa lallai shingaye da hijabai daga azama sakamakon zunubai ne da sabo da halaye marasa nagarta dukkanin wanda ke cin naman dan’uwansa zuciyarsa ke mutuwa  ko kuma yake gaza kunnuwansa da  saurarren gulma zai kasance laifinsa yafi girma ta kaka zai samu azama tareda wannan halaye ta kaka zai riski zakin ibada ya yi shauki zuwa gareta yaji yana kaunar ibada kamar yadda salmanu muhammadi Allah ya kara masa yard aya kasance yana kaunar ibada ya karkade zuciyarsa da samuwarsa don ibada, bai taba ruduwa daga ibadar ubangijinsa ba ya kasance yana kwankwasa kofarsa dare da rana ba yankewa, sannan ya kamaceka ka karanta munajatin muridin da munajatin muhibbin bari dai ka karanta dukkanin munajatoti guda goma sha biyar har ka san ta yaya zaka samu azama, sannan ya zama wajibinka ka dinga karanta wannan yanki daga addu’ar Abu Hamzatu simali :    

 (مالي كلما أقول قد صلحت سريرتي)

Me ya same ni ne duk sanda nace tabbas zuciyata ta gyaru.

Imam Zainul Abidin yana ambato dalilai da illoli da sabubba goma sha hudu da suke sabbaba faduwar azama da gushewarta

Allah ne mai taimako da karewa.
Tarihi: [2018/2/26]     Ziyara: [873]

Tura tambaya