b Shin ya halasta gare mu mu roki Allah mahaliccin sarki mai iko ya dawo mana da dan’uwanu da ya mutu
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin ya halasta gare mu mu roki Allah mahaliccin sarki mai iko ya dawo mana da dan’uwanu da ya mutu


Salam Alaikum
Tambaya ta shi ne ni ina da yakini kan cewa Allah yana da iko kan yin komai daga ciki raya matattu lallai Allah cikin littafinsa mai girma ya ambaci labarin annabi Ayuba (a.s) da labarin annabinmu Muhammad (s.a.w) da yanda ya dawowa da Ayuba lafiyarsa da dukiyarsa da iyalansa da suka mutu da wasunsu daga kissoshi da suke da irin wannan ma’ana, shin ya halasta gare mu mu roki mahalicci mai iko ya dawo mana da dan’uwanmu mamaci a raye yana mai azurtuwa, hakika ba zan iya jure hakurin rabuwa da shi ba. Ashe Allah Azza wa Jalla cikin hadisul kudusi bai ce: (ya kai bawana ka mini da’a sai ka kasance misalina za ka cewa abu kasance take sai ya kasance) kuma ai raya matattu abu ne mai saukin gaske gurin Allah ta yanda ya bada damar yin hakan ga wasu ba’arin bayinsa da wasiyyai mafi falalarsu Muhammad da iyalansa (s.a.w) shin ni ma ya halasta gareni in yi addu’a da kamun kafa da annabawa da wasiyyai domin samun biyan wannan bukata sakamakon ni ina kyautata zato ga Allah lallai ni zan roke shi idan ya so sai ya biya mini bukata ta idan kuma bai so ba lallai shi ga kowanne abu mai iko ne.

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Kadai dai ubangijin talikai ya yi hakan ne domin bayyana mu’ujiza kan hannun annabinsa domin mutane su gasgata annabtarsa, ita mu’ujiza abu ne da ba a saba ganinsa ba, ba kuma saba da shi a al’adance ba sannan ita rayuwarmu ta yau da gobe ba kan tsarin mu’ujiza take tafiya ba kadai abu ne da ke tafiya kan tsarin al’adar da aka saba da ita yau da gobe, sannan yayin da muka yi  rashin dan’uwa Allah ya umarce mu da rungumar hakuri da kuma kowanne lokaci mu dinga fadin (Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un) maimaikon dawowar mamaci cikin wannan duniya da take cike da wahalhalu da kuma cewa idan ya dawo garemu sai kuma mu muka rigaye shi gidan gaskiya to a wannan lokaci shi ne zai shiga cikin bakin ciki ya kuma nemi Allah ya dawo da mu shi ya koma ya mutu alhalin mu muna neman haka har zuwa karshen duniya, shin wannan Magana ta dace da hankali? Ko kuma dai tafi kama da maganar masu tabin hankali, ya kamaceka ka rungumi yin addu’a ga mamacin da Allah ya yi masa gafara ya ajiye shi cikin aljanna bawai neman ya dawo ba zuwa wannan duniya mai cike da bakin ciki da damuwa, ashe baka ji daga masu huduba abin da Imam Husaini (a.s) ya fadi yayin shahadar dansa (hakika ka huta daga bakin ciki da damuwar wannan duniya) shin yana daga cikin soyayya ga mamaci neman a ga ya dawo cikin bakin ciki da damuwa ko kuma dai kawai wannan tsabar son kanka ne da son zati da cewa mamaci ya dawo me ya sameku ne yaya kuke hukunci, kamar ina ganinka daga wayayyu me ya sanya ka wannan raki ina hakurin da aka umarce mu da shi ku sani dukkanin mu fa zamu mutu (lallai kai mai mutuwa ne suma zasu mutu) bayan yan shekaru kadan ta yiwu mabasu wuce adadin yatsun hannu ba da sannu za a riskar damu da su (sukai wasicci da gaskiya sukai wasicci da hakuri) ka dinga yin istigfari tare da karanta kur’ani mai girma da addu’o’i da tawassulai da karanta ziyarori ga kanka da mamacin da kuma yawan nazarin litattafai masu amfanarwa   

 (وقل ربي زدني علماً)

Ka ce ubangiji ka kara mini ilimi.

Ka kuma riskar da ni da salihai Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2018/4/28]     Ziyara: [838]

Tura tambaya