b Shekara nawa ake rainon yara a shari’ance
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shekara nawa ake rainon yara a shari’ance

Ina da wani da sunansa Aliyu yana da shekara hudu da rabi yana hannun mahaifiyarsa dana sake ta aurenmu ya kare, sannan kotu ta kebance mini awanni hutu cikin kowanne wata domin samun damar ganin sa daga hannun ta

 

Ina da wani da sunansa Aliyu yana da shekara hudu da rabi yana hannun mahaifiyarsa dana sake ta aurenmu ya kare, sannan kotu ta kebance mini awanni hutu cikin kowanne wata domin samun damar ganin sa daga hannun ta.

da sunan Allah mai rahama mai jin kai

wannan yana ta’allaku da daidaitawa tsakanin miji da mata, sai dia cewa rainon yaro a hannun mahaifiyarsa a shari’ance shekaru biyu ne idan kuma yarinya ce shekara bakwai, saboda haka yaro idan ya haura shekaru biyu to rainon sa yana komawa hannun mahaifinsa sai dai idan rashin cancantuwarsa ta tabbatu wajen Hakimul Shar’i, kamar misali ace yanada matsalar tabuwar hankali ko wauta ko dia abin da yayi kama da haka, saboda haka dole ne akomawa Hakimul shar’i gabanin komawa ga dokoki zamani da suke sabawa tsarkakakkiyar shari’a, lallai yanda lamarin yake duk wanda basa yin hukunci da abin da Allah ya saukar lallai wadannan sune fasikai kafirai azzalumai da bayanin Kur’ani karara.

Allah ne mafi sani

Tarihi: [2018/8/2]     Ziyara: [696]

Tura tambaya