b Mutumin da ya gano cewa matarsa tana cin amanarsa
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Mutumin da ya gano cewa matarsa tana cin amanarsa

Salam Alaikum
Zuwa ga sayyid Adil-Alawi Allah ya tsawaita rayuwarsa ya sanya shi daga bayinsa masu iklasi, Sayyid ni ina dag cikin masoyanka, mas’alar shine mutum ne ya ganio cewa matarsa tana ha’intarsa ba tareda wani dalili sannan da aka matsa mata sai da kanta tayi ikirari cewa eh ta ci amanarsa, bayan wnai lokaci sai ijinta ya tambayeta me ya sanyata ha’intarsa sai tace: na tsinci kaina na kadaita da wani namiji na to shine shaidan ya zama ukun mu shine abinda ya faru ya faru, sai dai cewa mijin ya tambayeta tambayoyi da yawa da ta gaza amsa su, shi yanzu yana cikin shakka cewa abinda ya faru ya faru fiye da karo daya sannan shi kuma yana masifar son matarsa, kuma ta ce masa lallai ta tuba, sai dia cewa mijin yana cikin dimauta ya rasa me zai yi sakamakon akwai `ya`ya tsakaninsu wadda daya takai shekaru goma, kuma ita matarsa tsa marainiya ce bata uwa bata uba, wacce shawara kuke bashi lallai ku malamai muna godiya da gudummawarku.
Mijin bai da wata hujja kan abinda yake zarginta face ikirarin da ta yi.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Amma batun marainiya baima taso ba sakamakon maraici yana tsayawa iya kan yan shekaru 9 bayan haura shekaru babu batun maraici.

Sannan batun cewa mai zai yi wannan mataki ya kamata ya dauka wannan wani abu ne yake hannunsa ta yiwu wasunsa yayinda suka san gasgatuwar tubanta da rashin komawarta kan abinda ta aikata a baya za su yafe mata saboda kaunar da suke mata da kuma kare `ya`yansu don gudun kada su kasance ba tareda mahaifiyarsu ba, sannan kuma daga cikin mutum akwia wand aba zia yarda da hakan ba kuma zai iya kara rayuwa tareda it aba ko da gwargwadon awa guda bari ma dai sanannan lamari cikin larabawa a lokacin jahiliya da ta gabata idan suka gano hakan to zasu kashe ta ko kuma su korata gidansu su saketa, wannan batu ne da ya danganta da kowanne mutum da yadda yake daukar mataki.

Allah ne abin neman taimako
Tarihi: [2018/12/11]     Ziyara: [721]

Tura tambaya