mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Akwai wani biki da aka gayyace ni daga makusantana amma akwai cudanyar maza da mata shin zan iya zuwa bikin sanye da hijabina?


Ni mace ce mai kiyaye sanya hijabi to shine danginmu suka gayyace ni biki sai dai cewa a bikin akwai cakuduwar maza da mata, shin zan iya zuwa da hijabina ko kuma a’a, muna jiran amsa daga gareku kune ahalin ilimi Allah ya saka muku da alheri.

 

 Da sunan  Allah mai rahama mai jin kai

Shi hijabi wajibi a kowanne hali cikin wadanda ba muharramanki ba, babu banbanci cikin kasantuwa a biki ko waninsa kai hatta cikin gida idan kina tareda da wand aba muharraminki ba kamar misalin dan baffanki ko dan gwaggonki daga danginki wadanda ake kirga su a shari’ance matsayin bare duk da kasantuwarsa daga danginki amma a hukunci hijabi wajibi kan mace baliga ta lullube jikinta daga garesu dama sauran ire-iresnu.

Allah ne masani.

Tarihi: [2018/12/24]     Ziyara: [620]

Tura tambaya