b Zantukanku da kalmominku haske ne cikin sauraron faraji
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Zantukanku da kalmominku haske ne cikin sauraron faraji


* قال رسول الله (ص): «طوبى للصابرين في غيبته، طوبى للمقيمين على محبته».
Manzon Allah (s.a.w) yace: farinciki ya tabbata ga masu hakuri cikin fakuwarsa, farinciki ya tabbata ga wadanda suke kan soyayyarsa.
* قال أمير المؤمنين (ع): «انتظروا الفرج ولا تيأسوا من روح الله، فإن أحب الأعمال إلى الله عزَّ وجلَّ انتظار الفرج ... والمنتظر للفرج كالمتشخّط بدمه في سبيل الله».

 

* قال رسول الله (ص): «طوبى للصابرين في غيبته، طوبى للمقيمين على محبته».

Manzon Allah (s.a.w) yace: farinciki ya tabbata ga masu hakuri cikin fakuwarsa, farinciki ya tabbata ga wadanda suke kan soyayyarsa.

* قال أمير المؤمنين (ع): «انتظروا الفرج ولا تيأسوا من روح الله، فإن أحب الأعمال إلى الله عزَّ وجلَّ انتظار الفرج ... والمنتظر للفرج كالمتشخّط بدمه في سبيل الله».

Sarkin muminai Ali(as) yana cewa: ku saurari yayewa kada ku debe tsammani daga ni'imar Allah, hakika mafi falalar ayyuka zuwa ga Allah shine jiran yayewa…

* قال الإمام الحسين (ع): «أما إن الصابر في غيبته على الأذى والتكذيب، بمنزلة المجاهد بالسيف بين يدي رسول الله (ص)».

Imam Husaini (as) yace: amma mai yin hakuri cikin fakuwarsa kan cutuwa da karyata shi da mutane keyi  lallai daidai yake mujahidi cikin tafarkin da takobi gaban manzon Allah (s.a.w).

* قال الإمام زين العابدين (ع): «من ثبت على ولايتنا في غيبة قائمنا، أعطاه الله أجر ألف شهيد مثل شهداء بدر وأُحد».

Imam Zainul Abidin (as) yace: duk wanda ya samu sabati kan wilayarmu cikin fakuwar Qa'im Alu Muhammad, Allah zai bashi ladan shahidi dubu daga misalin shahidan yakin Badar da Uhudu.

* قال الإمام الصادق (ع): «المنتظر للثاني عشر كالشاهر سيفه بين يدي رسول الله (ص) يذبُّ عنه».

Imam Sadik (as) yace: mai sauraron Imamul Hujja daidai yake da wanda ya zare takobinsa yana baiwa manzon Allah (s.a.w) kariya

* قال الإمام موسى الكاظم (ع): «طوبى لشيعتنا المتمسكين بحبّنا في غيبة قائمنا، الثابتين على موالاتنا والبراءة من أعدائنا أولئك منا ونحن منهم. وقد رضوا بنا أئمة ورضينا بهم شيعة. طوبى لهم ثم طوبى لهم هم والله معنا في درجتنا يوم القيامة».

Imam Kazim (as) yace: farinciki ga shi'armu masu riko da soyayyarmu cikin fakuwar Qa'im din mu, masu tabbatuwa kan wilayarmu daga makiyanmu wadannan daga garemu suke mu ma daga garesu muke, hakika sun gamsu da A'imma mu ma mun gamsu da su matsayin shi'armu, farinciki ya tabbatab garesu, wallahi suna tareda mu cikin darajarmu ranar alkiyama.

* قال الإمام الرضا (ع): «ما أحسن الصبر وانتظار الفرج».

Imam Rida (as) yana cewa: mai yafi kyawu daga hakuri da sauraron yayewa.

* قال الإمام الجواد (ع): «أفضل أعمال شيعتنا انتظار الفرج».

Imam Jawad (as) yace: mafi falalar ayyukan yan shi'armu jiran da sauraron yayewa.

* قال الإمام الهادي (ع): «لولا من يبقى بعد غيبة قائمكم من العلماء الداعين إليه والدالين عليه، والذابين عن دينه بحجيج الله، والمنقذين للضعفاء من عباد الله من شباك إبليس ومردته لما بقي أحد إلا ارتد عن دين الله. ولكنهم يمسكون أزمَّة قلوب ضعفاء الشيعة كما يمسك صاحب السفينة سكانها، أولئك هم الأفضلون عند الله عزَّ وجلَّ».

Imam Aliyul Hadi (as) yana cewa: ba da ban wadanda suke rage bayan gaibar Qa'imun dinku daga malamai masu kira zuwa gareshi masu nusantarwa kansa, masu bada kariya daga addininsa da hujjojin Allah, masu ceton raunanan bayin Allah daga tarkon Iblis da halakarsa da babu wani mutum da zai rage face yayi ridda daga addinin Allah. Sai dai cewa sun kasance suna rike da ragamar zukatan raunanab shi'a kamar yanda direban jirgi yake rike da ragamar fasinjar cikin jirgin, wadannan sune mafi fifita da falala wurin Allah azza wa jalla.

 

 


Tarihi: [2019/2/26]     Ziyara: [602]

Tura tambaya