b Wani al’amari ya faru dani a cikin Haramin Imam Ali (as)
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wani al’amari ya faru dani a cikin Haramin Imam Ali (as)

Salamu Alaikum.

Sayyid wani al’amari ne ya faru gareni a Haramin Imam Ali (as) hakika na ga wani Sharifi kan sanye da rawani cikin kwarjini da haiba haske na ta kyalkyala daura da shi, a zuciya sai naji cewa shine Imamul Hujja (Af), wannan al’amari ya afku ne gabanin hudowar rana shi ya kasance daga bangaren wajen farfajiyar haramin ni kuma na kasance ina zaune kusa da Kabarin mai tsarki, yayin da ya yin bankwana ya juya zai tafi sai ya waiwayo ya kalleni daidai lokaicn da haibarsa ta mamayeni sai nag a fuskarsa kamar yanda aka siffanta ta cikin riwayoyi, naga idanuwansa sun yi jajawur saboda yawan kuka har lokacin da ya tafoi ya bace na daina ganinsa, sannan na mike domin inje in yi bankwana da Imam Ali (as).
 
Tambaya anan shine shin zata iya yiwuwa wancan sharifi dana gani ya kasance Imamul Hujja.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Idan kina da’awa kan haka to hakika ya zo a hadisi cewa duk wanda yayi da’awar lallai ya ga Imamul Hujja to ku karyata shi, ta yiwu ya kasance daga boyayyun mutane kirki , Allah ne masani, sannan koma yaya ta kasance to kiyi kokarin ganin kin kasance daga mutane kirki da suke ganinsa, sannan nima ina rokon kiyi mini addu’a in kasance daga cikinsu, lallai ni ina kaunar mutane nagargaru salihai sai dai cewa bana daga cikinsu ta yiwu albarkacin addu’arki in kasance daga cikinsu, lallai na je wajen mai karamci ba tareda guzuri daga kyawawan ayyuka da lafiyayyar zuciya wacce babu komai cikinta sai Allah.

Ya Alolah ka azurtani da soyayyarka da soyayyar wanda yake sonka, da dukkanin aikin da zai isar da ni zuwa gareka

Tarihi: [2019/2/27]     Ziyara: [587]

Tura tambaya