b Tsarin yanayin zamantakewa yana bada gudummawa mai yawan gaske cikin karkatar da samari daga hanyar shiriya
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Tsarin yanayin zamantakewa yana bada gudummawa mai yawan gaske cikin karkatar da samari daga hanyar shiriya

Salam Alaikum. Sayyid kamar yanda kuka sani cikin al’ummar mu akwai kungiyoyi masu yawan gaske da suke tukewa ga karkatar da yawa-yawan matasa, al’amarin ya kai su ga shaye-shaye kayan maye da aikata munana ayyukan fasikanci (Allah ya tsaremu), muna neman su Sayyid da su bamu wata addu’a ko wata ayar kur’ani da zamu yi riko da ita ta yanda zamu iya samun damar Magana da wadannan matasa kuma su kasance masu mutumta maganar mu da kaunarmu.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Wajibi kan mu mu isar da sakon Allah zuwa ga mutane sai dai cewa tareda hakan bamu da iko kan su, kamar yanda Annabi mafi girman dara (s.a.w) yake cewa: (ni banda iko kansu) kadai taka isar da sako, cikin akwai wanda zai karbi nasiharka akwai kuma wanda ba zai karba ba, muhimmi shine kai dai kaga kayi kokarin sauke nauyin da ya hau kanka wato umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, kada kayi tsammani cewa dukkanin mutane sai sun so k aka sani mafi yawan mutane basu son gaskiya, su mutane suna kiyayya da abin da suka jahilta, idan ka himmatu kan yin tabligi isar da sako to ka karanta (ya Azizu) kafa hudu shi suna ne daga Asma’ulllahi husna sannan ka hura shi kan kirjinka zaka kasance madaukaki da daukakar Allah matsarkaki, duk wanda yake da rabon shiriya zai kaunace ka zai saurari nasiharka.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2019/4/25]     Ziyara: [610]

Tura tambaya