mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wadanne ayyuka ne suke kawo albarka

Shin kunna sautin karatun kur’ani mai girma a cikin gida yana saukar da albarka cikin gidan?

Wadanne ayyuka ne suke janyo albarkoki cikin gida. Kuma suke korar Shaidan suke kuma saukar da Mala’iku?

Shin kunna sautin karatun kur’ani mai girma a cikin gida yana saukar da albarka cikin gidan?

Wadanne ayyuka ne suke janyo albarkoki cikin gida. Kuma suke korar Shaidan suke kuma saukar da Mala’iku?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Abin da ya fi shine ku karanta da kanku duk da dai babu laifi cikin jin sautin bisa la’akari da shi matsayin kur’ani bawai da la’akari da abin da ake karantawa domin nawa ne daga masu karanta kur’ani amma sai ya zamanto kur’anin yana la’antarsu kamar misalin makiya Ahlil-baiti, lallai da zasu karanta kur’ani da ya la’ance su domin basa yin aiki da ayoyin sa wadanda suke shiryar da zuw aga riko da Ahlil-baiti, sai suka ki suka yi riko da Zaidu da Amru kamar yanda aka fada, suka bata suka batar , basu kasance daga wadanda Allah ya ni’imta ba daga suka yi `da’a ga Allah da manzonsa (s.a.w).

Amma dangane da ayyukan da suke kawo albarka daga cikin su akawai yawan karatun kur’ani da salla da yin addu’o’I da tawassulai da munajati da kyawunta dabi’a da karanta ba’arin wasu ayoyi wadanda daga cikinsu akwai:

(رب أنزلني مُنزلاً مباركاً وأنت خير المنزلين)

Ya ubangiji ka saukar da ni masauki mai albarka kai ne mafi alherin masu saukarwa.

Da kuma yawan yin salatin manzon Allah (s.a.w) da iyalan sa tsarkaka da yin istigfari da yin kiran sallah a cikin da da sauti mai karfi. Na yi bayani dalla-dalla kan sabubban arziki cikin littafin (Hasken sasanni cikin sanin arziki) an sauke shi a sayit din Alawy.net  

Tarihi: [2019/5/6]     Ziyara: [538]

Tura tambaya