mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Dangane da hadisin: bawana ba zai gushe ba yana samun

Dangane da hadisin: bawana ba zai gushe ba yana samun kusanci dani da nafiloli

Salamu Alaikum ya Sayyid tambayar mu dangane da hadisin da yake cewa: bawana bazai gushe ba yana samun kusanci da ni ta hanyar yin nafiloli har sai na so shi, to dangane da mu da muke mai’aikatan gwamnati bangaren lafiya bamu samun lokacin yin nafila sakamakon dukkanin lokacin da muke da shi ya kare cikin hidimar marasa lafiya wadanda muke daukar su bayin Allah tambaya a nan shine shin wannan hadisi ya takaitu iya cikin sallar nafila ko kuma ya tattaro dukkanin ayyukan alheri da mutum zai aikata shi cikin soyayyar Allah shine ake kira da nafila?

Wacce nasiha zaku yi mana musammam kan aikin mu na hidimtawa marasa lafiya da biyan bukatun su?

Saboda mu samu guzurin da zamu je da shi lahira domin mu ma mu samu soyayyar ubangiji da rabauta da haduwa da shi

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya halasta mutum yayi sallar nafila yana halin tafiya ta hanyar motsa kansa lokacin yin ruku’u da sujjada kage Kenan zaku samu damar hada aiki biyu hidimtawa marasa lafiya da kuma ribatar nafila a wannan lokaci kamar yanda mace tana iya hada yin girki da yin nafila a lokaci guda hakama matukin mota, kaga Kenan mumini a kowanne hali zai iya sallatar nafila wannan wata babbar ni’ima ce babu masu yin wannan sallah sai wadanda suka narke cikin soyayyar ubangiji, lallai yanda al’amarin yake shine duk wanda yake son wani abu to yana kaunar ambaton sa (ya Allah ka sanya harshena mai motsa ambatonka ka zuciya ta mai maraici da kaunarka) ma’ana in zama mai yankewa baki daya zuwa gareka , daga babin (ya Allah ka bani kamalar yankewa zuwa gareka) kula da mara lafiya tareda sallatar nafila ibada ce cikin ibadame yafi kyawu daga wannan kula da mara lafiya wanda cikin sa akwai gaggautar samun waraka da yardarm Allah, me yafi kyawu daga wannan nafila!ya Allah ka azurtamu da kasancewa haka kamar yanda kake so kake yarda, sannan ita nafila ta tattaro dukkanin ayyukan alheri da ake neman kusancin ubangiji da su

Tarihi: [2019/5/28]     Ziyara: [550]

Tura tambaya