b SHIN ANA IYA GANIN TASIRIN TAUHIDI A ZAHIRI
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

SHIN ANA IYA GANIN TASIRIN TAUHIDI A ZAHIRI


Salam Alaikum
A cikin bayananku mun je kun yi wasicci da wani kebantaccen Azkaru yayin fitowa daga gida shine karanta Suratul Tauhid a kowacce kusurwar gidan guda shida, lallai yin hakan yana da fa’idoji masu tarin yawa, sai dai cewa sakamakon rashin rubuta abinda kuka yi wasicci da shi sai ya zama mun manta cikakken bayani, da Allah ku taimaka mana da yanzu da kara bayani kan falalar aikin da tasirinsa, sannan ana ganin tasirin sa shin yana daga abinda Annabawa da Wasiyyai suka taba gwadawa suka ga nasara ciki ko kuma dai yana daga riwaya ne kadai

 

Salam Alaikum

A cikin bayananku mun je kun yi wasicci da wani kebantaccen Azkaru yayin fitowa daga gida shine karanta Suratul Tauhid a kowacce kusurwar gidan guda shida, lallai yin hakan yana da fa’idoji masu tarin yawa, sai dai cewa sakamakon rashin rubuta abinda kuka yi wasicci da shi sai ya zama mun manta cikakken bayani, da Allah ku taimaka mana da yanzu da kara bayani kan falalar aikin da tasirinsa, sannan ana ganin tasirin sa shin yana daga abinda Annabawa da Wasiyyai suka taba gwadawa suka ga nasara ciki ko kuma dai yana daga riwaya ne kadai.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya isar maka cikin tasirin wannan aiki zaka kasance cikin shinge da katamga daga wasiwasin Shaidan daga dukkanin kusurwowin guda shida, ma’ana zaka kasance cikin kariyar Allah da tsarkakar badini daga tauhidi shin akwai wani tasiri da yafi wannan?! Sannan aikin ya zo daga abinda aka jarraba aka ga nasara haka kuma ya zo a riwaya mai daraja.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2019/10/14]     Ziyara: [579]

Tura tambaya