mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

MUNA BARAR WANI AIKI KO WURIDI DOMIN SAMUN `DA NAMIJI SALIHI

Salamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu
Ina da `ya`ya mata guda uku kuma yanzu haka mata ta tana da cikin tana cikin wata na biyu muna fata da burin Allah ya azurta mu da `da namiji Salihi, shin akwai wani aiki na ibada da zamu yi domin samun biyan wannan bukata.
Allah ya saka da alheri.

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Ya zo a hadisi mai daraja kuma a kankin kaina na jarraba haka, matukar ba ta shiga wata na hudu da duakar ciki ba to ka dauki hannunka ka dora a kan cikinta daga bangaren damanta ka karanta ayatul kursiyu  sannan kace na sanya masa suna Muhammad, lokacin da ta haife shi ka kira shi da Muhammad idan kana son canja masa suna to ka bari sai bayan `yan kwanaki sai ka canja masa sunan.

A wurin Allah ake neman taimako.

Tarihi: [2019/10/28]     Ziyara: [456]

Tura tambaya