b na karanta ziyarar Ashura har sau 40 amma bukata bata biya ba
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

na karanta ziyarar Ashura har sau 40 amma bukata bata biya ba

Salamu Alaikum
tambaya ga Samahatus Assayid Adil-Alawi (h) ina da wata bukata tawa ta kaina na karanta ziyarar Ashura har sau Arba'in tareda yin la'ana kafa 100 salati kafa 100 don neman biya bukata ta amma kuma ban dace ba, zuwa yanzu na maimaita arba'in arba'in har sau uku amma duk da haka bukatar bata biya ba, tareda cewa ni inajin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma farin ciki yana mamayeni duk sanda na kammala karatun ziyarar.

abinda bake neman biyan bukata kansa shine ni mace ce kuma ina son auren wani mutum, sannan nayi mafarki na ganni gaban Kabarin Imam Husaini amincin Allah ya tabbata a gareshi yana rike da wata takarda sai dai ban san mene ne ke rubuce cikin taakardar ba ina dai iya tuna cewa akwai Hatimi kan takardar, sannan na maimaita irin wannan har karo biyu.

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai
Ina fawwala al'amarina zuwa ga Allah lallai shine mafi sanin halin da nake ciki, yayi kusa kuso wani abu alhalin sharri ne gareku, kuma yayi kusa ku ki wani abu alhalin alheri ne gareku, sai abinda yafi dacewa garemu shine yin addu'a da kuma fawwala al'amari ga Allah da dogara da shi, sannan da fari ya kamata himma ta kasance ta 'daga sama matuka a lokacin karatun ziyarar Ashura da sauke addu'a da Kur'ani, hakika Allah yana son al' amura masu ma'ana yana mjma kin shirma da shashanci, ya kamata ace hatmar ta kasance da niyyar neman kusancin Allah da kuma tashi tareda shugaban Shahidan Karbala bawai kawai da niyyar ina son auren wane ko wance ba, karamar bukata irin wannan yafi bukatar addu'a daga Mumina mo mumina amma hatmar زویا Ashura mai girma wacce babu wanda ya san sirrinta face Allahda masu zurfin ilimi Muhammad da iyalansa tsarkaka amincin Allah ya kara tabbata a gare su.
Wurin Allah ake neman taimako.

Tarihi: [2020/4/13]     Ziyara: [488]

Tura tambaya