b Koda yaushe ina cikin kunci
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Koda yaushe ina cikin kunci

Salamu Alaikum:
na kasance cikin kuncin rayuwa a koda yaushe shin akwai wata addu'a ko wani wurudi da zai taimaka mini.

Koda yaushe ina cikin kunci
Salamu Alaikum:
na kasance cikin kuncin rayuwa a koda yaushe shin akwai wata addu'a ko wani wurudi da zai taimaka mini. 
Allah ya saka muku da alheri. 
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

عن محمد بن الرّيان قال: كتبت إلى أبي الحسن الثالث عليه السلام أسأله أن يعلّمني دعاء للشدائد والنوازل والمهمات وأن يخصّني كما خص آباؤه مواليه، فكتب إليّ: 
الزم الإستغفار (البحار: 93: 383 الحديث 30).
an karbo daga Muhammad Ibn Rayyan yace:na rubuta wasika zuwa Abu Hassan na uku amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ina rokonsa ya sanar dani wata addu'a don fita daga tsanani da musibu masu sauka da kuma ya kebanceni da kamar yadda ya kebance iyayensa da masoyansa, sai ya rubuto mini amsa da cewa ka lazimci yin istigfari.
وعن إسماعيل بن سهيل قال: قلت لأبي الحسن الرضا عليه السلام: علَمني دعاء إذا أنا قلته كنت معكم في   الدنيا والآخرة، فكتب: أكثر تلاوة (إنّا أنزلناه) وأرطب 
   شفتيك بالإستغفار (البحار 93: 284 الحديث 30) 

daga  Isma'il Obn Suhailu yace: na cewa Abu Hassan Arrida amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ka sanar dani wata addu'a idan na karantata da zan kasance tareda ku a duniya da lahira, sai ya rubuta cewa : ka yawaita karatin Inna Anzalnahu sannan ka jika labbanka da istigfari. 
Imam Kazim amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya kasance a kowace rana yana yin istigfari 5000 tareda cewa shi Imami ne baya aikata sabo da zunubi, ta yaya mu kuma masu aikata zunubi me yasa ba zamu yawaita tuba da istigfari ba, sannan ka duba  suratu Nuhu aya ta 10-11-12 a ciki akwai amsarka. 
Tarihi: [2020/4/20]     Ziyara: [468]

Tura tambaya