b Idan na nufi tafiya aiki Hajji shin wajibi ne kaina in ziyarci makusantana
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Idan na nufi tafiya aiki Hajji shin wajibi ne kaina in ziyarci makusantana

Assalamu Alaikum Sayyidna Fadil Jalil
tamabaya shine idan na tafi hajji ya zama wajibi kaina in ziyarci makusantana da neman yafewa juna tareda su

Assalamu Alaikum Sayyidna Fadil Jalil
tamabaya shine idan na tafi hajji ya zama wajibi kaina in ziyarci makusantana da neman yafewa juna tareda su? 

Idan ya kasance daya daga cikin makusanta da ya fito daga ɓangaren mijina da suka yanke zumunci dani, sannan suka nemi mijina ya hana ni ziyartarsu cikin bayyanannen harafi da suka kamar haka(mu bama zumunci da matarka kuma bama kaunar matarka tayi zumunci damu) har ta kai ga sun sanar da kananan 'ya' yana sun ce musu ko da kun girma kunyi aureba zamu yi zumunci daku baba kuma zamu halarci daurin aurenku ba. 
sannan sun tilasta mijina da ya yanke alakarsa dani da dangina, tsawon shekaru mijina baya ziyartar dangina nima bana ziyartar nasa, wannan shine abinda suka nema daga gareshi, Allah ne shaida ni ban aikata musu wani kuskure ko laifi ba, a kowanne lokaci sune suke ta sabbaba mini matsaloli nice kuma nake zuwa ina afuwa daga gare su in nemi yardar daga gare su, dai dai cewa lamarin ya kai gaba sun tsayu kan wulakanta ni da kaskantar dani, wani daga cikinsu yana zuwa wurin mijina yana mini barazana da ya sakeni ba don komai sai don 'yar' uwarsa ta fadi magana a kaina, Akaramakallahu lamarin ya kai ga dan'uwan mijina yana neman aikata lalata dani amma dai Alhamdulillahi Allah ya tseratar dani, sai dai kuma tareda haka mijina ya kame bakinsa yayi shiru bai dau mataki ba sabida wai sune yan' uwansa da suka rage a raye, amma tareda haka ni ban hanashi zumunci da su kai hatta 'ya' yana suna ziyartar su, su kowanne lokaci burinsu rabani da mijina, idan yayana suka ziyarce su suna cutar dasu da nuna musu kyama da kiyayya ta domin sauya tunanin mijina kan yayana.
ni yanzu yaya zanyi kenan ta kaka zan je ziyarar su alhali basa kaunata sun koreni daga cikinsu, duk sanda na sassauto sai su kara wulakantani. 
Menene mafita? 
da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai 
Mustahabbi ne cigaba da kokarinki na rayar da zumunci dasu, mafita shine hakuri da neman taimakon Allah ta hanyar sallarda tawakkali kan Allah, ki zama kamar rana da take ludufinta ga Fasiki da Mumini kamar yanda ya zo cikin hadisi mai daraja. 
Tarihi: [2020/5/5]     Ziyara: [458]

Tura tambaya