mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Neman fatawa kan kakaba takunkumin tattalin arziki

Salamu Alaikum

Muna da bahasi kan kakaba takunkumin tattalin arziki a muslunci meye matsayinsa yaya ake mu’amala tareda shi, muna fatan Samahatus Assayid zai bamu amsa kuma idan zai yiwu ayi mana ishara zuw aga dalili, Allah ya saka muku da alheri.

 

Salamu Alaikum

 

Muna da bahasi kan kakaba takunkumin tattalin arziki a muslunci meye matsayinsa yaya ake mu’amala tareda shi, muna fatan Samahatus Assayid zai bamu amsa kuma idan zai yiwu ayi mana ishara zuw aga dalili, Allah ya saka muku da alheri.

 

Neman fatawa dangane da takunkumin tattalin arziki.

Idan wata kasa daga cikin kasashen Kafirai ta kakabawa kasar musulmi takunkumin tattalin arziki shin yana halasta ga wata kasa ta musulmi daban ko kuma wani musulmi yin mu’amala tareda waccan kasa ta Kafirai?

 

Na biyu:shin ya halasta ga kasar musulmi ta bada hadin kai da tarayya tareda waccan Kasa ta Kafirai cikin takunkumin kan kasar musulmi?

 

Na uku: shin yana halasta ga musulmi a daulance ko kuma kungiyance da daidaikunsu su kakaba takunkumin tattalin arziki kan kasar musulmi yar`uwarsu ko kan daidaikun yan’uwansu musulmi?

 

Na hudu: idan wasu ba’arin musulmi suka yanke mu’amala da Kafirai shin wajibi ne kan sauran musulmi suma su yanke mu’amala da wacancan Kafirai?

 

Na biyar: da kasar Kafirai zata mu’amala da waa kasar ta Kafirai shin ya halasta ga Musulmi yayi tarayya tareda daya cikinsu kan kishiyantar daya?

 

Na shida: shin ya halasta a sabawa takunkumin tattalin arziki da aka da Majalisar dinkin duniya ko majalisar tsaro suka kakaba shi kan kasar musulmi ko kasar da bata musulmi ba tareda rashin rattabuwar cutuwa kan masu sabawa ma takunkumin?

 

Na bakwai: shin wajibi aikata dokokin majalisar dinkin duniya da majalisar tsaro cikin takunkumin tattalin arziki kan kasar musulmi ko wacce bata musulmi cikin halin rashin cutuwa kan sabawar?

 

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Duka ya halasta a dunkule amma da sharadin kada ya zamanto Kafirai sun samu iko da mulkin mallaka kan musulmi (Allah ba zai taba sanyawa Kafirai iko kan musulmi ba) Nisa”I 14. Majalisar musulmi da ma’abota zartarwa da gudanarwa da ministoci sune wadanda suke tantance misdakai da sugrayat din wannan Kubra,

Allah ne masani. 
Tarihi: [2020/11/23]     Ziyara: [343]

Tura tambaya