mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin wannan riwaya ta inganta

Salamu Alaikum
Ya zo cikin riwayar Imam Kazim amincin Allah ya tabbata a gareshi cewa ya kasance a cikin Banu Isra’ila akwai wani mutumi Mumini da yake da wani Makoci Kafiri, wannan Kafiri ya kasance yana tausayi Mumini yana kyautata masa a zamantakewarsu ta duniya, lokacin da wannan Kafiri ya mutu sai Allah ya gina masa gidan tabo a cikin wuta wannan gida yana kareshi daga zafin wuta sannan arziki yana zuwa gareshi daga wajen wuta, aka ce masa wannan shine abin nan da kake baiwa makocinka.

1-    Shin wannan riwaya ingantacciya ce?

2-    Yana nufin Kenan duk wani Kafiri da yake kyautatawa Mumini ana saukaka masa azaba?!

Idan halin Kafiri ya kasance haka to yaya kuma shi Mumini ake masa azaba cikin wuta alhalin shine mafi girmama daga wancan Kafiri da aka saukaka masa.

3-    Shin shima Mumini ana saukaka masa radadin azaba har zuwa lokacin da ceto zai zo masa sabida wasu na cewa shi Mumini ana masa azaba tsawon shekaru hamsin ko kasa da haka bisa yanda ya zo dai a riwaya, ashe Mumini ba shi ne mafi girmama daga Kafiri ba to ta kaka shi Mumini zai dandani azaba a cikin wuta amma Kafiri sakamakon aikata wani dan kankani aiki na alheri zai samu saukaka azaba a wuta ?

Da sunan Mai rahama Mai jin kai

Ni bani da sani dangane da ingancin riwayar bai bincike kan riwayar ba, sai dia cewa abinda ta kunsa ya zo cikin jumla daga wasu riwayoyi da suke nuna cewa aikin alheri da wanzazzun ayyuka nagari suna zuwa wurin Mumini yayin domin dauka masa fushin Allah wani lokacin ta hanyar gafarta masa zunubansa a wani karon kuma suna daukaka darajarsa cikin aljanna, haka lamarin yake dangane da Kafiri da Nasibi lallai a na saukaka masa azabar Jahannama

Sannan shi saukaka azaba ga Kafiri na kasancewa ga wanzuwa da dawwamarsa a wuta,amma shi Mumini da ya aikata sabo to lallai shi sakamakon ayyukan alherinsa wanzazzu ana saukaka masa azaba da ma’anar fitar da shi daga wutar kacokan da kuma shigar da shi aljanna, kan wannan ne banbanci ke tabbata tsakanin saukakawa mumini da saukakawa kafiri. 

Tarihi: [2021/2/21]     Ziyara: [321]

Tura tambaya