Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Yaya ake rama salloli mahaifa daga uwa da una bayan mutuwarsu .
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Yaya ake rama salloli mahaifa daga uwa da una bayan mutuwarsu .

Salamu Alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
Wasu malamai suna fatawa kan wajabcin rama sallolin uwa da uba kan baban dansu bayan mutuwarsu, sannan waus kuma suna cewa iya uba kadai zai ramawa, me yasa suke fadin haka alhalin sallolin farilla duk day aske kan dukkanin musulmi.

Salamu Alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Wasu malamai suna fatawa kan wajabcin rama sallolin uwa da uba kan baban dansu bayan mutuwarsu, sannan waus kuma suna cewa iya uba kadai zai ramawa, me yasa suke fadin haka alhalin sallolin farilla duk day aske kan dukkanin musulmi.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Allah ne kadai masanin hikimar abinda ya zo cikin risalarsa da taklifinsa, kadai wajibi ne kanmu a zamanin Gaiba Kubra mu komawa gurin Maraji’ai kowa ya koma ga Marja’insa yayi aiki kan hasken fatwarsa, maksudi shine ibada da tsantsar sallamawa ga hukuncin Allah matsarkaki kamar yanda ya zo cikin hadisi daya daga cikin Marawaita ya cewa Imam Sadik (A.S) idan kace rabin abin marmarin nan halas ne daya rabin nasa haramun  zanci halal zan bar haram b azan tambayi komai ba, sai Imam (A.S) yace: addini ba komai bane face sallamawa, amma tareda haka a ba’arin wasu wurare Imam Amincin Allah ya tabbata a gareshi yana Ambato illoli da hikimomi da dalilai kamar yand aya zo cikin littafin Ilalul Sharayi na Shaik Saduk Allah ya yi masa rahama , tana iya yiwuwa hikima ciki shi da namiji yana ramawa babansa banda babarsa saboda shi uba shine asalin samuwarsa shi ya samar da digon halittarsa ita uwa ita kwaryar da ta karbi halittarsa ce ta kuma raine shi, ta yiwu cikin misalin wannan sallah ta ramuwata kasance ga uba kadai ya kebantu da ita duk da cewa cikin wasu wuraren uwa itace a kan gaba shi uba share fage yake gareta kamar misali cikin sadar da zumunci (da farko mahaifiyarka mahaifiyarka sai kuma babanka)

Allah ne masani.  

Tarihi: [2021/4/22]     Ziyara: [301]

Tura tambaya