lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Sai nayi na so abu kaza, sai muka so abu kaza niyya, sai ubangiji ya nufi abu kaza

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

(أَمَّا السَّفِينَةُ فَكَانَتْ لِمَساكِينَ يَعْمَلُونَ فِي الْبَحْرِ فَأَرَدتُّ أَنْ أَعِيبَها وَكانَ وَرَاءهُم مَّلِكٌ يَأْخُذُ كُلَّ سَفينَةٍ غَصْبًا).

Amma jirgin ruwa hakika ya kasance mallakar wasu talakawa da suke aiki a teku sai na yi niyyar lalalata jirgin akwai wani Sarki da ya kasance bayansu da yake kwace dukkanin jirgi

 

(وَأَمّا الْغُلَامُ فَكَانَ أَبَواهُ مُؤْمِنَيْنِ فَخَشِينا أَن يُرْهِقَهُما طُغْيَانًا وَكُفْرًا * فَأَرَدْنَا أَن يُبْدِلَهُمَا رَبُّهُمَا خَيْرًا مِنْهُ زَكوةً وَأَقْرَبَ رُحْمًا).

Amma yaron mahaifansa sun kasance muminai sai muka jhi tsoran kada ya shafa musu dagawa da kafirci*sai muka yi nufim ubangijinsu ya canja musu da wanda ya fishi kasancewa alheri da tsarkakuwa da kasancewa mafi kusa da rahama.

 

وَأَمَّا الْجِدارُ فَكَانَ لِغُلَامَيْنِ يَتِيمَيْنِ فِي الْمَدِينَةِ وَكَانَ تَحْتَهُ كَنزٌ لَهُما وَكَانَ أَبُوهُما صالِحًا فَأَرَادَ رَبُّكَ أَنْ يَبْلُغا أَشُدَّهُمَا وَيَسْتَخْرِجا كَنزَهُما رَحْمَةً مِن رَبِّكَ وَمَا فَعَلْتُهُ عَنْ أَمْرِي ذَلِكَ تَأْوِيلُ مَا لَمْ تَسطِع عَلَيْهِ صَبْرًا

Amma bangon ya kasance mallakar wasu yara guda biyu marayu a cikin birnin karkashin bangon akwai taska da ta kasance mallakinsu babansu ya kasance mutumin kirki  sai ubangiji ya nufi su cika karfinsu su fito da taskarsu sakamakon kasantuwarsa rahama ne daga ubangijinka ban aikata shi daga umarni na ba wancan shine tawilin abinda ka kasa yin hakuri a kansa.

 

Hakika cikin kissar Kidir da Musa (as) da kuma cikin fadinsa ta’ala (sai na nufi) da (sai muka nufi) da (sai ubangijinka ya yi nufi) cikin ma’anar irada nufi, ta kaka a wani lokacin aka danganta ta ga Musa wani karon kuma ga ubangiji da Kidir a wani sa’ilin kuma sai ta kebantu da Allah shi kadai, akwai tsammani da maganganu dalla-dalla kan hakan kamar yanda ya zo a riwayoyi da tafsirai dole mu koma garesu, sai dai cewa a takaice Allah ne mafi sani, daga cikin maganganun akwai: lallai jumlolin sun sassaba sakamakon wasu dalilai na balaga cikin zahirin kur’ani mai girma da abinda ya ta’allaka da siyakin ayoyin da abinda suka kunsa daga abubuwan da suka faru.

Sannan daga cikin fuskoki akwai: hakika irada da nufi na farko ta rataya da wata kaziya da cikinta akwai aibu na zahiri da barna cikin zahiri saboda hakane ma Kidir (as) ya danganta nufin zuwa ga kansa sabida ladabi, sannan irada nufi na biyu cikinta akwai alheri da sharri, da ifsadi ta fuskanin aiki da ni’imtarwa ta hanyar sauyawa sabida haka ne ya danganta ta ga Allah da kuma kansa, amma ta uku ita alheri da n’ima tsantsa ne kadai cikinta sabanin ta farko da ta biyu sabida hakane aka danganta ta da Allah matsarkaki.

Sannan daga cikin shine cewa cikin irada ta farko Kidir (as) yayi aiki da iliminsa da hankalinsa sabida kasantuwar lamarin na zahiri baya bukatar wahayi daga ubangiji, amma cikin irada ta biyu da farko ya sani ne sannan kuma Allah yayi masa wahayi, sakamakon cikinsa akwai bangaren zahiri wanda shine kafircin yaron da janibin wahayi wanda shine yiwuwar kafircewar iyayen yaron anan gaba, wannan yana daga cikin bada labarin abinda zai faru nan gaba wanda yake bukatuwa zuwa ga wahayi, amma lamari na uku shi tsantsar wahayi ne kadai saboda shi yana daga ilimin gaibu kuma Kidir bai san shi ba bai kewaya da shi face da umarnin Allah da wahayinsa.

Daga cikin fuskokin akwai yiwuwar wadannan jumloli da kalmomi su kasance daga nunar tunanin Kidir (as) ma’ana ta farko yace nayi nufin sai akai masa ilhama da cewa ba ta kasance daga iradarka ba mai cin gashin kanta ba tareda cudanya da iradar Allah ba, shi ya sanya ma a karo na biyu yace sai muka nufi sai dai aka kara yi masa ilhama kario na biyu da cewa iradarka ba zata kasance kishiyar iradar Allah ba, saboda hakane cikin ta uku ya isa zuwa ga Attaudidul Af’ali (dayanta Allah cikin ayyuka) yace sai Allah ya nufa hakan ya kasance daga babin  

.

 (وَمَا رَمَيْتَ إِذْ رَمَيْتَ وَلَٰكِنَّ اللَّهَ رَمَىٰ)

Ba jefa ba yayin da kayi jifa sai dai cewa Allah yayi jifa.

 

Daga cikin fuskokin akwai: yiwuwar wadannan martabobi su kasance cikin iradar da take bayanin martabobi uku cikin dayantuwar samuwa tareda Allah, Kidir (as) cikin ta farko yana cewa: nayi nufi saboda tsakaninsa da tsakanin ubangiji an samu wani hijabi ya kasantu wanda ake kiransa da mukamin Ainul Jam’i, a cikin martaba ta biyu sai yace: mun yi nufi, domin yayi ishara zuwa ga mukamin Nuzuli da nesanta daga mukamin Allah.

 

Daga cikin fuskokin akwai abinda Samahatus Assayid Adil-Alawi yayi bayani: cewa tana bayyanar da halayen daban-daban tsakanin bawa da ubangijinsa, ta farko marhalar wadatuwa tsantsa ga bawa da izinin ubangijinsa, shine da ma’anar cewa komai na bawa ne kamar yanda Allah yake cewa:

 (مَنْ ذَا الَّذِي يُقْرِضُ اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا)

Wane ne zai baiwa Allah rance mai kyawu.

Cikin rance da bashi kuddaden na kasancewa ga wanda nemi rancen shi kuma wanda ya bayar ya zama ya tawaya daga garesu, saboda haka ne ma Kidir yake cewa: na nufi wannan cikin zahiri sai dai cewa badininsa kadai na kasancewa da iradar Allah da yardarsa, sannan marhala ta biyu cikin igiya da tsanin tsakanin bawa da ubangijinsa Allah yana cewa bawanda kana da shi ina da shi zo muyi cinikayyam sayar mini da kanka in baka aljanna

 (مِنَ النَّاسِ مَنْ يَشْرِي نَفْسَهُ ابْتِغَاءَ مَرْضَاةِ اللَّهِ)

Daga cikin mutane akwai wanda yake sayar da kansa don neman yardar Allah.

 

Na da ma’anar cewa Allah yana da irada kai ma kana da taka iradar, sabida saye da sayarwa yana kasancewa ne daga bangare biyu bangaren mai sayar da kaya da mai sayensu, sannan a marhala ta uku marhalar wakilci tana nufin cewa kai kana da jimillar kaya sai dai cewa ka sanya Allah wakilinka cikin wannan dukiya taka, cikin sayar da su da sayensu da tasarrufi cikinsu wannan abin yana cikin amfanin ka, kamar yanda Allah yake cewa:

 (وَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ وَكِيلًا)،

Ka dogara da Allah ya isar zaman Allah wakili.

 

Sannan marhala yta uku wacce itace marhalar wilaya, da ma’anar cewa kana da haja kaya sai dai cewa ka shingantu dag tasarrufi cikinsu, sakamakon kai kana daga cikin wadanda basu da cancantuwar yin tasarrufi cikin dukiyarsu suna bukatuwa zuwa ga waliyi da wilaya, kamar misalin mai rashin fama da larurar tabin hankali da karamin yaro da wawa dole da abinda yayi kama da haka, kamar yanda madaukakin Sarki yake cewa:

 

 (اللَّهُ وَلِيُّ الَّذينَ آمَنوا يُخرِجُهُم مِنَ الظُّلُماتِ إِلَى النّورِ)

Allah shine majibancin al’amarin wadanda suka yi Imani yana fitar da su daga duffai zuwa haske.

 

Wadannan marhaloli uku Kidir (as) yayi bayaninsu cikin maganarsa da fadin sai muka nufi, sannan marhalar karshe ta biyar shine tsantsar talauci na zati cikin hallarar Allah matsarkaki, da ma’anar cewa kai baka da komai dukkanin abinda yake cikin samuwa da abinda yake gareka mallakin Allah ne girmansa ya girmama, kai tsantsar talaka ne Allah ne mawadaci tsantsa.

 

 ( يَآ أَيُّهَا النَّاسُ أَنْتُمُ الْفُقَرَآءُ إِلَى اللَّهِ وَاللَّهُ هُوَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ)،

Yaku mutane ko mabukata ne zuwa ga Allah Allah shine mawadaci godadde.

 

Kamar yanda Kidir (as) daga karshen dawafi yake cewa (sai Allah ya nufa).

 

Daga cikin fuskoki Allah ne masani akwai: cewa halaye ne daban-daban ga Kidir (as) da suke bayyanar da sirarsa da narkearsa zuwa ga Allah Azza wa Jalla da hadewa tareda shi cikin irada da aiki cikin karshen al’amari daga babin ittihad da tajalli bawai wahadatul wujudul zati ba sakamakon gurbatarsa, yayin da yayi aiki na kwarai cikin marhalar farko sai ya danganta shi zuwa ga iradarsa sai dai cewa ya nemi kusanci da shi zuwa ga Allah da yanayin da zia ga iradarsa gefan iradar Allah sai ya danganta iradar gareshi da kuma ga ubangijinsa cikin sairin su’udi da mi’irajinsa yana ganin Allah shi kadai babu kowa cikin guda da samuwa sai Allah sai ya danganta iradar zuwa ga Allah matsarkaki saboda haka ne ma yace Allah ya nufa (sairi su’udi da kusance ga mukamin Allah) wannan na nufin tsakaninmu da Allah akwai taku guda biyu kadai taku na uku kadai na kasancewa cikin hallarar Allah hakan bai yiwuwa face da aiki na kwarai.

 

Daga ciki akwai: ina cewa fuskar karshe Allah ne masani shine cewa iata iradar mutane ta yiwu ta jawo sharri na zahiri ko da kuwa daga bayansa akwai alheri, amma iradar mutum tareda ta Allah na jawo alheri daga wani bangare sai dai cewa ta wani bangaren akwai sharri cikinta, amma iradar Allah tsantsa ita alheri ce tsantsa tsura babu mis, wajibi ga bawa ya nema daga Allah kadai, kada ya nufi wani abu face wanda Allah ya nufa yake so, wannan shine abinda ake kira da mukamin fana’i cikin Allah, ma’ana iradar Allah tana kore dukkanin iradar bawa, babu abinda zai so sai abinda Allah mastarkakin Sarki yake so.

 

Akwai wasu fuskokin sai dai cewa dukkanin su suna daga istihsanar da zace-zacen ko kuma abubuwan da suka zo daga zantukan sufaye da zauki da kashafi da shuhudi, cikin kowacce dole a kawo dalili daga riwaya ko karina haliya ko kuma ingantaccen shuhudin irfani.  

Tura tambaya