lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

IMAM HASSAN ASKARI DA TALAKAWA

Muhammad bn Ali yace: halin tattalin arzikinmu ya munana ta yanda rayuwarmu ta wayi gari cikin matukar tsanani, sai mahaifina yace mini mu je wajen Imam Askari (as) hakika naji labari cewa yana taimakon talakawa, sai nace masa shin ka san shine? Sai yace: a’a ban san shi ba.

Sai muka tafi wajensa sai babana a kan hanya yace mini: ina bukatar dirhami dari biyar inama ace Imam (as) ya bani wannan abinda da nake bukata domin in sayi kaya da dirhami dari biyu in sayi gari da dirhami dari biyu ragowar kuma in sayi kayan bukata da sauran.

Muhammad bn Ali yana cewa: sai cikin raina nace: inama Imam (as) nima ya bani dirhami dari uku in sayi jakin dirhami dari daya in sayi kayan bukatu da dirhami dari daya, ragowar in yi tafiya zuwa Jabal yankuna duwatsu a Iran Hamdan da Kazwin, lokacin da muka isa gidan Imam (as) sai wani yaro ya fito wurinmu sai yace: Aliyu bn Ibrahim da `dansa su shigo, sai muka shiga, Imam (as) ya cewa mahaifina: me ya sa baka zuwa wurina ya zuwa yanzu?

Sai mahaifina yace: ya shugabana ina jin kunya ne in ganka ina cikin wannan hali, bayan mun juya mun tafi daga hallarar Imam (as) sai wannan yaro ya biyo mu ya mikawa mahaifina wata dan karamin kulli wanda yake kunshe da dirhami dari biyar, ya cewa mahaifina ka dirhami dari biyar nan kaje ka sayi tufafin dari biyu daga kudin sannan ka sayi kayan bukatu da sauran kudaden, daga karshe ya cewa mahaifina kada kayi tafiya zuwa Iran maimakon haka ka tafi Suri (wani yanki a Iraki cikin Bagadaza).

Sai Muhammad bn Aliyu ya tafi yayi aure a can, kowacce rana yana samun shigar dirhami dubi biyu, sai dai kuma tareda haka bai canja baya wanzu kan akidarsa ta (wakifiya) wakifanci tsayama kan Imami na bakwai (as)

Tura tambaya