lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Tauhidin jikkanta Allah (Attauhidul Jismani)

Da sunansa madaukaki

Abu na farko farko cikin gamammun akidun wahabiyawa na bata shi ne ra'ayinsu cikin tauhidi wanda ake kidaya shi asali daga asalai da kuma kasantuwarsa asasin addini.

1- hakika wahabiyawa sun tafi kan surantawa da jikkanta Allah da siffanta shi da cewa Allah matsarkaki shi jiki ne amma ba kamar ragowar jikkuna ba, yana da dukkanin abin da mai jiki yake da shi tun daga fuska hannaye kafafuwa, lallai shi yana dasurar shagirin saurayi wanda gashing emu bai tofo a fuskarsa, gashin kansa a warwatse yake ba tare da tajewa ba, kamar yadda yana da yanayi irin na mutane daga zaunawa da kwanciya kan gadon bayansa da dora kafarsa daya kan daya, sanya takalmin zinariya da dai sauransu.

Ya yinda ya tabbata cewa shi Allah matsarkaki babu wani abu da yake misalinsa, sai suka ce shi jiki ne amma ba kamar ragowar jikkuna ba, yana da yanayi ba irin yanayin ragowar mutane ba, bari dai da abin da ya kebantu da zatinsa na ubangijintaka.

 

2- kamar yadda Allah yana da karaga daga bangaren sama lallai shi yana saman halittunsa[1]

Lallai shi Allah ya na saukowa daga karagarsa kamar yadda mai huduba ke sauka daga kan mimbarinsa, hakan na faruwa ne ranar juma'a daga kwanakin karshe sati, yana zama tare da annabawansa kan karaga, bayan kammala zama sai ya kara komawa kan karagarsa.[2] 

3-Lallai al'amarin yadda yake shi ne za a ga Allah mai girma da daukaka ranar kiyama gani na kwayar ido karara[3]

Suna kafa dalili kan baki dayan hakan da cewa duk abin da ya kasance mafi cika da kammaluwa shi ne mafi cancata da a ganshi da idaniya, to tunda shi Allah ya kasance mafi kammala cikin samuwa to shi ya fi cancanta da a ganshi da kwayar ido[4]

4- sannan suna cewa lallai Allah yana da kwauri da kafa yana kuma sanya takalmin zinariya, lallai shi yana saukowa cikin kowanne dare daga kan karagar al'arshinsa ya zuwa sama ta daya, lallai shi a daren Arafat yana kusantowa daga kasa har ya dinga amsa addu'o'in bayin sa, lallai shi yana tambayar jahannama (shin kin cika) sai ta ce (shin akwai kari ne) sai Allah ya sanya kafarsa a cikin wuta sai wuta ta dinga cewa kat kat, ma'ana ta cika, da dai makamantan wadannan daga gurbatattu akidu batattu  cikin dayanta Allah matsarkaki madaukaki.

 



[1] Kuna iya komawa littafin minhajul sunna na ibn taimiyya bugun misra bugu na shekarar 1321 mu 1 sh 137 hakam ma majmu'u fatawa m 5 shy 137. Da tauzihul makasid na ibn kayyumu aljauzi bugu na uku bairut m 1 sh 234.  Sharh tauhid na sualaiminu ibn Abdullah ibn mohd ibn abdul-wahab m 1 sh 659 da sauransu.

[2] Kuna komawa cikin littafin ibn taimiya mai sauna ijtima'I juyush islamiya bugun bairut darul kutub ilmiyya m 1 sh 51 ; majumu'u fatawa m 5 sh 55. Ko kuma ibn kayyum akjauzi cikin zdul ma'ad bugun bairut mu'assatau darul risala. 399- 11407

[3] Kuna komawa minhajus sunna  bugun mu'asssatu kurdaba  bugun na farko 1406

[4] Minhajus sunna: m 1 sh 341

Tura tambaya