lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

BAHASUL KARIJUL FIKHU 27 RABIU AWWAL 1441 H, CIKIN MAS’ALAR WANDA YA KASANCE YANA DA WATA MATSALA A HARSHENSA DA BA ZAI IYA FURTA KALMOMI

 

Wuri: cibiyar Muntada Jabalul Amil Islami-tare da Samahatus Assayid Adil-Alawi (H) karfe 8 na safe.

Mas’ala 30: idna ya zamana akwai wani ciwo a kan harshensa da zai hana shi furta kalmomi sai ya yi karatun a cikin zuciyarsa, ko da kuwa cikin wahami amma abin da yafi zama ihtiyadi shi ne ya dinga motsa harshensa cikin abin da yake wahamtawa.

Ina cewa: cigaba kan abin da ya gabata da fadadawa kansa daga wajabacin karatu cikin sallah cikin raka’o’in biyun farko idan ya zamana akwai wani ciwo kan harshensa. Tun lokacin da da aka haife shi yana fama da wannan ciwo da yake hana shi furta kalmomi tom menene hukuncinsa?

Mash’hur din malamai wand adaga cikinsu akwai mawallafin Allah ya tsarkake sirrinsa sun tafi kan cewa zai karanta cikin zuciyarsa ne koda ta hanyar wahamtawa da surantawa, duk da cewa ihtiyadi istihbabi ya motsa harshensa cikin abin da yake wahamtawa kamar misalin zancen zuciya da darsuwar abubuwa cikin zukata ko kuma misalin ilhamomi daga Allah matsarkaki ko wasiwasi daga Shaidanu.

Mas’alar tana da fuskoki:

Fuska ta farko: cikin kasantuwar mai sallah yana da iko kan ingantaccen karatu, lallai wajibi yin haka a kansa wannan yana daga abin da babu ishkali cikinsa.

Ta biyu:ya kasance ya gaza ya kasa ingantacce karatu daga kasantuwa ba zai iya furta haruffa daga mafitarsu ba kamar misalin idan zai furta harafin ra’un sai furta ya’un maimakonsa, ko kuma kasantuwarsa ba’ajame bai kyawunta harshen larabaci sia ka same shi yana furta harafin zayun maimakon zadun kuma ba zai iya koyo ba.

Ta uku: ya kasance ya gaza sakamakon wani shamaki da shinge da ya bijiro kamar misalin rashin lafiya haka misalin wanda yake da wata matsala kan harshensa.

Ta hudu: ya kasance ya gaza tun daga lokacin da aka haife shi kamar yanda yake cikin wanda bai ya Magana (Bebe).

Amma fuska ta farko: hukunci shi ne wajabcin ingantaccen karatu a kansa.

Fuska ta biyu: wajibi kansa ya kawo iya abin da zai iya daga abin da ya saukaka gareshi daga karatu, wannan karatunsa yana daga Allah bai dorawa rai face abin da ya yalwaceta, kamar Muwassakatu Assakuni ta ke ishara zuwa ga hakan:

موثقة السكوني عن أبي عبد الله عليه السلام قال: قال النبي صلى الله عليه وآله وسلم: إن الرّجل الأعجمي من أمّتي ليقرء القرآن بعجميته، فترفعه الملائكة على عربيته([1]).

Daga Abu Abdullah amincin Allah ya kara tabbata a gareshi ya ce: Annabi (s.a.w) ya ce: lallai mutumin da yake ba balarabe ba daga al’ummata ya karanta kur’ani tare da ajamancinsa sai Mala’iku su daukaka karatun kan larabacinsa.

Fuskar kafa hujja: bayan ingantar isnadi lallai Assakuni da Naufali duk da cewa dukkaninsu ba daga shi’a suke ba suna daga gurbatacciyar mazhaba sai dai cewa su suna daga Sikatu (mutanen da aka aminta da su)kasantuwar marawaicin daga Sikatu ya wadatar cikin aiki da hadisin sabani matafiyar Shahid Awwal da Sani da wanda ya kasance kan matafiyarsu da cewa maraiwacin da ya kasance kan gurbatacciyar mazhaba ba a daukar maganarsa, sannan zahirin riwaya ba’ajame idan bai iya samun ikon koyo ba ko da kuwa zuw aga karshen lokaci to iya abin da ya sani ya wadatar da shi kuma za a karba daga gareshi lallai Mala’iku zasu tura shi kan larabcinsa.

Daga abin da ya karfafar haka ingantacciyar riwayar Mas’adatu Ibn Sadakatu 

معتبر مسعدة بن صدقة قال: سمعت جعفر بن محمد عليه السلام يقول: إنّك قد ترى من المحرم من العجم لا يراد منه ما يراد من العالم الفصيح، وكذلك الأخرس في القراءة في الصلاة والتشهد وما أشبه ذلك فهذا بمنزلة العجم، والمحرم لا يراد منه ما يراد من العاقل المتكلّم الفصيح([2]).

Ya ce: ba ji Jafar Ibn Muhammad amincin Allah ya tabbata a gareshi yana cewa: lallai kai kana iya ganin bakauyen ba’ajame daga gareshi ba a bukatar abin da ake bukata daga wurin malami mai fasaha, haka ma Bebe cikin karatun sallah da zaman tahiya da abin da yayi kama da haka wannan yana matsayin Ajamawa, bakauyen daga gareshi ba a neman abin da ake nema daga mai hankali mai Magana da fasaha.

Fuska kafa hujja: bayan lafiyar isnadin riwayar abin da nufi daga Almuhram bakauye shi ne wanda bai cudanya da zamantakewar birni kamar yanda ake ake cewa bakauyen balarabe: ya bushe bai cudanya da wayewa da birni ba (Akrabul mawarid juz 1 sh 185).

Amma fuska ta uku: shi ne abin da mawallafin ya bijira kansa cikin wannan mas’ala lallai shi ya tafi kan cewa a irin wannan hali zai yi karatun ne cikin zuciyarsa ko da kuwa da wahamtawa ne kamar sururi da surutun da yake a ransa da darsuwar abubuwa cikinsa.

Wannan Kenan duk da cewa kebantaccen nassi bai zo cikinsa ba sai dai mai littafin Jawahir Allah ya tsarkake ransa ya karkata zuwa ga wannan ra’ayi ya kuma kafa hujja kansa, da farko: da abin da ya zo daga wanda tsoro ya hana shi yin karatu, na biyu: da Sahihiyar riwayar Aliyu Ibn Jafar (a.s)

 سألته عن الرّجل هل يصلح له أن يقرء في صلاته ويحرك لسانه بالقراءة في سهواته ـ فضاء فمه ـ من غير أن يسمع نفسه؟ قال عليه السلام: لا بأس أن لا يحرك لسانه يتوهم توهماً([3]).

 

Na tambaye shi dangane da wani mutum shin ya inganta gareshi cikin sallarsa yayi karatu ta hanyar motsa harshensa cikin farfajira bakinsa ba tare da shi kansa ya ji mai yake karantawa ba?

Sai amincin Allah ya kara tabbata a gareshi ya ce: babu laifi kada ya motsa harshensa ya wahamta wahami.

Hakika wannan hadisi mai daraja ya gabata da dukkanin ishkalan da suke bijira a kan kafa hujja da shi, da cewa bai da alaka da bahasinmu, sabida zahirinsa wanda ya kasance cikin zabi yana aikatawa, wannan ya sabawa Kur’ani da sunna sabida makomarsa na komawa ne ga la’akari da karatu cikin sallah wanda hakan yana sabawa fadinsa madaukaki:

﴿فَاقْرَءُوا مَا تَيَسَّرَ مِنْ الْقُرْآنِ﴾ (المزمل: 20)

Ku karanta abin da ya saukaka daga Kur’ani.

Haka zalika ya sabawa tarin hadisai wadanda suke umarni da karanta Fatiha cikin sallah ko kuma karanta Fatiha tare da surori daga Kur’ani.

Daidai wannan lokaci ya zama dole ko dai ayi watsi da ita bisa gini kan cewa hadisin ya sabawa Kur’ani zuki tamalli ne gurbatacce bamu fade shi ba, ko kuma dai mu komar da iliminsa zuwa ga Imam amincin Allah ya tabbata a garsehi kamar yanda ya zo cikin Jumla daga hadisai ko kuma mu dora shi kan abin da Shaik Dusi ya dora shi da cewa ya kebanta da wanda yake sallah a bayan mabiya mazhabar da ba ta Ahlil-baiti ba bisa takiyya, don gudun watsi da riwayar kai tsaye.

Na uku: hadisin Ibn Jafar wanda ya zo cikin littafin Kurbul Isnad4 sai dai cewa kuma hadisin rarrauna ne sakamakon samun Abdullahi Ibn Hassan cikin Isnadinsa kamar yanda ya kansance bai da mashiga cikin mahallin bahasinmu.

Na hudu: Mursalatu Muhammad Ibn Abi Hamza:

بمرسلة محمد بن أبي حمزة قال: يجزيك من القراءة معهم مثل حديث النفس([5]).

Ya ce: ya isar maka daga karatu tare da su misalin sururi da surutu cikin rai.

Anyi ishkali kansa: da farko dai isnadinsa rarrauna ne na biyu akwai irsali sannan ita wannan riwaya kamar tana nuni ne karara cikin yin sallah bayan mabiyan wata mazhaba sakamakon fadinsa (a.s): (tare da su) sai wannan riwaya ta zamanto bakuwa  daga abin da muke bahasi ciki.

Babu abind aya rage face kasancewa hukuncinsa daidai da hukuncin Bebe-kamar yanda zai zo- sai ya yi riko da idlakin abin da ya zo cikin hadisin Assakuni daga Imam Sadik (a.s)

 (تلبية الأخرس وتشهدُه وقراءتهُ القرآن في الصلاة تحريك لسانه وإشارته بأصبعه) ([6]).

Talbiyar Bebe da zaman tahiyarsa da karatunsa cikin sallah shi ne motsa harshensa da nuninsa da yatsunsa.

Fuskar dalili: daga babin tanasubul hukumu ma’al maudu’ maudu’in mas’alar ko dia ya kasance daya daga misdakan Bebe sai ya zamana kamar Bebe a hukunci ko da kuwa bai kasance maudu’i ba, ko kuma dais hi ya kasance daya daga daidaikun abin da aka nufa daga Bebe a maudu’an dora hadisin kan wanin Bebe da kuma cewa shi dayan wanin mafhumi ne na daban bai kasance daga zahiri ba, ta yiwu fuska daga ihtiyadin mawallafin shi ne motsa harshensa misalin Bebe daga wannan babi duk da cewa ihtiyadi shi yafi dacewa daga jingina masa yin ishara da da yatsu sakamakon abin da ya zo daga hadisi, sai hukuncin Bebe ya gudana kansa cikin mukamin, maganar a dunkule shi ne: lallai babu nassi kebance cikin fuska ta uku da za dogara da ita, ko dai mu tafi kan cewa ya tattaro Bebe a mafhumance da misdaki, sannan abin da ake nufi da Bebe shi ne wanda bai iya koyo mudlakan babu banbanci a kankin zatinsa ko kuma da bijirowa sai hukuncin ya tattaro da shi kasantuwarsa daya daga misdakansa, ta yiwu ace ma’anar Bebe ta karkata zuwa ga wanda bai da Katanga da shinge daga yin Magana a zatance kamar misalin misalin Makaho da ak haife shi da makanta, lallai baya gasgatuwa kan wanda baya gani a take cikin wannan hali saboda shi makanta a wajensa ciwo ce da zata iya karbar magani, hakama dayar, lallai yana karkata zuwa ga wanda rashin ikon kan Magana ya bijira kansa saboda shima wannan larura tana iya kaucewa ta hanyar magani, sai manufar ta zama ta fita daga maudu'in dayar sai dai cewa yana cikinsa a hukunci sakamakon munasabar hukunci da maudu’i, lallai wannan da cewa tana hukunta cewa Bebe bai da wata hususiya kadai dai anyi riko da shi ne cikin harshen dalili bisa la’akari da kasancewarsa ba zai iya Magana ba, wnanan shi ne maudu’in a hakikance amma dayan lallai shi yana daga daidaikun misdakai, sai hukuncinsa ya zama irin hukuncin Bebe sai dai cewa Ihtiyadi ya hada da zancen zuci ko da kuwa da wahami ne kamar misalin cewa ya dinga motsa harshensa da abin da yake wahamtawa kamar yanda wasu adadi daga malamai suka tafi akan haka, haka ya dinga ishara da yatsunsa kan abin da yake wahamtawa da surantawa sakamakon abin da ya zo a riwaya kamar yanda wannan shi ne ra’ayin da muka zabi muka fifita.

Amma dangane fuska ta hudu da hukuncin Bebe yana daga cikin bahasinmu na nan gaba da yardar Allah ta’ala

 

Tura tambaya