MUKAMI NA FARKO: CIKIN ZARGIN FUSHI DAGA LITTAFIN ALLAH DA SUNNA

1-Allah madaukaki ya ce:

{إِذْ جَعَلَ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي قُلُوبِهِمُ الْحَمِيَّةَ حَمِيَّةَ الْجَاهِلِيَّةِ فَأَنْزَلَ اللَّهُ سَكِينَتَهُ عَلَى رَسُولِهِ وَعَلَى الْمُؤْمِنِينَ وَأَلْزَمَهُمْ كَلِمَةَ التَّقْوَى وَكَانُوا أَحَقَّ بِهَا وَأَهْلَهَا وَكَانَ اللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍعَلِيماً} سورة الفتح:26 .

Yayin da wadanda suka kafirce suka sanya kabilanci irin na jahiliya a cikin zukatan su  sai Allah ya saukar da nutsuwarsa kan Manzonsa da muminai ya lazimta musu Kalmar takawa sun kasance mafi cancantuwa da ita kuma ahalinta Allah ya kasance masanin komai.

Hananar kabilanci na nufin daga hanci da fushim hakika Allah ya zargi kafirai daga abind aya gangaro daga garesu daga hananar kabilancin jahiliya da ya gangaro daga fushi gurbatacce da jin izza da sabo, da daga hanci daga karbar gaskiya, ya kuma yabawa muminai daga abin da ya ni’imta su da shi daga nutsuwa wacce ya saukar kan manzonsa da muminai daga mabiyansa da sahabban sa.