lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

MENE NE YA SANYA AKA HAIFI ALI (AS) A CIKIN DAKIN KA’ABA

عناوين

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Akwai wata tambaya da take bijiro da kanta shine cewa: ta kaka zamu fassara kebantuwar Imam Ali (as) da haihuwarsa a cikin dakin ka’aba koma bayan Manzon Allah (s.a.w)?! ... cigaba

IMAM HASSAN ASKARI DA TALAKAWA

Muhammad bn Ali yace: halin tattalin arzikinmu ya munana ta yanda rayuwarmu ta wayi gari cikin matukar tsanani, sai mahaifina yace mini mu je wajen Imam Askari (as) hakika naji labari cewa yana taimakon talakawa, sai nace masa shin ka san shine? Sai yace: a’a ban san shi ba. ... cigaba

MALAMAI MAGADA ANNABAWA_TARIHIN SHAIK JAFAR TUSTARI.


An haifi Ayatullah Shaik Jafar Tustari a shekara ta 1230 hijiri a birnin Tustar wanda ake kiransa da Shushtar, a farko-farkon rayuwarsa ya raka da babansa Shaik Husaini Wa’izi cikin safararsa zuwa Iraki, sai ya zauna a can garin Kazimiya Nahru Dajala arewacin Bagadaza, ta yanda maida hankali kan darasi a wannan gari, sannan ya daga ya koma birnin Najaf wacce ta kasance babbar cibiyar ilimin Ahlil-baiti, a biranen guda biyu yayi dalibta a hannun manya-manyan malamai, daga cikinsu akwai: Shaik Murtada Ansari, da Shaik Muhammad Hassan Najafi mawallafin littafin (Jawahir Kalam) da Shaik Ali bn Shaik Jafar Kashiful Gida`, hakama yayi dalibta hannun dan’uwansa Shaik Hassan kashiful Gida`, da Shaik Radi Najafi, da Shaik Shariful Ulama’u Mazandarani.
A shekara ta 1255 hijri Shaik Tustari ya dawo mahaifarsa domin yin ayyukan ilimi da zamantakewa a wannan lokaci ya kasance yana da shekara 25, bayan cikin karatun sa a Njafar ya kai ga cimma martabar yin Ijtihad cikin fikhu , a garin Tustari ya kasance babban Marja’i ga mutane cikin bayar da fatawa cikin abinda ya shafe dgaa kaziyoyi da batutuwa, ya gina Husainiya a wannan gari wacce ta zama babbar cibiyar zaman makokin ta’aziyyar Imam Husain ibn Ali (as) kuma mahallin yin tablig da jagorantar sallolin jam’i.
... cigaba

Arziki da ni'ima_tareda Alkalamin Assayid Ali bn Husaini Alawi

Arziki da fari ciki sababin samuwarsu na da tarin yawa; shi arziki wani hali ne na nafsu da yake samuwarsa suka kammmala, daga cikin mafi muhimmancin sabubban samuwarsa akwai abinda ya zo daga hadisi mai daraja, (ya Allah ka azurta mu). ... cigaba

Ili yasin cikin kur’ani_tareda Assayid Muhammad Alawi



Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Me ake nufi da (Ili yasin) da ya zo cikin kur’ani mai girma?
Hakika Allah cikin kur’ani mai girma cikin suratul Safat ya ambaci Nuhu (as) ya ce: (amincin Allah ya tabbata a gareshi cikin talikai) bayansa kuma ya kawo Ibrahim (as) ya ce: (amincin Allah ya tabbata ga Ibrahim) bayansa ya kawo Musa da Haruna (as) ya ce: (amincin Allah ya tabbata ga Musa da Haruna) bayansu sai Ambato Iliyas (as) ya ce: sai suka karyata shi, bayan haka sai ya ce: (amincin Allah ya tabbata ga Iliyasin) bayansa ya ce: lallai shi, wanda lamirin da yazo mufradi ne na mutum daya rak.
... cigaba

Sai nayi na so abu kaza, sai muka so abu kaza niyya, sai ubangiji ya nufi abu kaza


Sai nayi na so abu kaza, sai muka so abu kaza niyya, sai ubangiji ya nufi abu kaza
Mene ne sababin sassabawa cikin wadannan kalmomi da suka zo cikin wadannan ayoyi?
... cigaba

Wata yar takaitacciyar kissa da a gaske ta faru

a Zamanin da ya shude anyi wani tsoho da ya kasance yana zaunawa tareda `dansa, wata rana suna cikin tattaunawa kwatsam sai suka ji ana kwankwasa kofa, sai matashin `dansa ya tashi ya je ya bude kofar, bude kofar ke da wuya sai ya ga wani mutum bako yana kokarin shogowa gidan ba tareda yin sallama ba yana mai nufar zuwa wajen wannan tsoho, yana cewa tsohon ka ji tsoran Allah ka biya bashin da yake kanka na yi hakuri fiye da haddin da ya dace yanzu kam hakurina ya rigaya ya kare ... cigaba

Kin cigaba da kiran sallah da Bilal Habashi yayi

Bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) Bilal Y daina kiran sallah, yace: ba zan yiwa kowa kiran sallah ba bayan Manzon Allah (s.a.w). ... cigaba

Daga kowanne malami akwai hikima



Hikimomi da bayanai da maganganu suna da yawan gaske ya kamata mu yi riko da su saboda suna nuna mana ingantacciyar hanya wacce magaba suka bi ta, na umarceku da riko da maganganun malamai da hikimominsu da za su zo cikin wannan makalar tawa:

... cigaba

Yanzu ba zaku yi duba zuwa ga Rakumi ba yaya aka halicce shi_ ina fuskar kamanceceniya



Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
(أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ * وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ * وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ * وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ)
Yanzu ba zaku yi duba ya zuwa rakumi ba yaya aka halicce shi* ya zuwa duwatsu yaya aka kafa su* ya zuwa kasa yaya aka shimfida ta.
Ina ne fuskara kamanceceniyar da rakumi?
Me ya sanya Allah yake son mu kalli rakumi ta fuskar iyakancewa a wannan aya mai albarka?
... cigaba

Tura tambaya