sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
 • Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
 • Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
 • MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
 • Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
 • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
 • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
 • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
 • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
 • Shahadar Fatima Azzahra A.S
 • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
 • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
 • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
 • sababun labare

  Labarun da ba tsammani

  Fatima zahara madubin kyawun Allah girmansa ya girmama

   

  Fatima zahara Sirri daga sirrikan Allah kasha na biyu- tareda alkalamin sayyid adil alawi

  Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah makagin sammai da kassai masnin gaibu  da bayyane tsira da aminci su tabbata ga mafi darajar halittu muhammadu da iyalansa tsarkaka, ubangiji ka buda bakina da shiriya ka kimsa mini  tsoranka: ya zo cikin ingantaccen hadisi mutawatiri daga bangare biyu cewa manzon Allah(s.a.w)  wanda bai fadin  son zuciya bai fadin kaoami face abinda akai wahayi gareshi yace: ya Fatima  lalle Allah yana fushi da fushinki yana kuma yarda da yardarki. Daga ckin tabbatun abubuwa da kur’ani da yakini suke nuni zuwa gareshi shine cewa lalle so shine(karkatar zuciya zuwa ga wanda take so) sannan kiyayya na kishiyantar hakan, lalle su biyu (so da kiyayya) suna daga cikin ayyukan zukata masaukinsu da mahallinsu iata ce zuciya sannan tasirinsu na bayyana kan gabbai dan adam koda kuwa ya bayyana ko ya boye ta karfi da yaji,

  Sannan kiyayya da soyayya sun kasu zuwa kasha hudu ta fuskanin dogaro da hakikaninsu.

  Na farko zuciya mai biyewa shaidani: lalle iblis da rundunarsa  akamr misalin mai waswasi da mai buya suna sace zukatan dan adam sai suyi sai maida zuciayar dan adam shekarsu da za suyi kwai da kyankyasa  kamar yadda sarkin muminai yayi ishara gameda hakan cikin litttafin sharhin  nahjul balaga huduba ta 7

  Manzon Allah(s.a.w) yace: (wani zamani zai zowa mutane fuskarsu fuskar dana dam amma zukatansa zukatan shaidanu.

  Allah matsarkaki  cikin kur’ani mai girma yana cewa:

  (هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَى مَن تَنَزَّلُ الشَّيَاطِينُ تَنَزَّلُ عَلَى كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ).

  Shin in baku labara a kan wadanne mutane shaidanu ke sauka suna sauka kan dukkanin makaryaci mai sabo.

  Maisalin wannan zuciya makaryaciya  mai yawaita sabo to tana yin matsananciyar soyayya shaidanci, kamar yadda take yin matsananciyar kiyayya da ma’aunan shaidanci. Allah ka tsare mu

  Ta biyu kuma itace zuciyar dabbobi: iatace wadda son rai ke galaba cikinta wanda ya bubbugo daga fushi da sha’awa sai ya dinga biye ma sha’awe sha’awe ya dinga yin fushi biye da karkatarsa ta sha’awa  da fushi da son mutanensa  Allah madaukakin sarki na cewa:

   (وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ الَّذِيَ آتَيْنَاهُ آيَاتِنَا فَانسَلَخَ مِنْهَا فَأَتْبَعَهُ الشَّيْطَانُ فَكَانَ مِنَ الْغَاوِينَ * وَلَوْ شِئْنَا لَرَفَعْنَاهُ بِهَا وَلَكِنَّهُ أَخْلَدَ إِلَى الأَرْضِ وَاتَّبَعَ هَوَاهُ فَمَثَلُهُ كَمَثَلِ الْكَلْبِ).

  Ka karanta musu labarin wanda muka bashi ayarmu sai ya fita daga gareta shaidani ya bishi  ya kasnce daga halakakku* da munso da mun daukaka shi da ita  sai dai cewa shi ya dawwama a ban kasa ya biy ma son ransa misalinsa kamar misalign kare ne.

  (يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجاً).

  Ranar da za ai busa cikin kaho ai ku zo jama’a jama’a.

  Zuciya ta uku iatce zuciyar hankali: lalle shi hankali yana daga ni’imomin Allah  amsu girman gaskiya kan dan adam, abinda ake nufi da shi  wajen annabawa shine wanda ake kira da (wanda aka bauta wa ubangiji da shi aka kuma samu aljanna ta hanyarsa) lalle lada da ukuba suna kewaya da shi  da duk inda ya kewaya.

  Lokacin da aka yabi wani mutum cikin sallarsa da ibadarsa  a gaban imam sadik(as) sai yayi tambaya gameda hankalinsa yace yaya hankalinsa yake. Manzon Allah(s.a.w) ya cewa sarkin mumina ali(as) idan mutnae suka nemi kuasnci zuwa ga mahaliccinsu da kyautatawa to kai ka kusnce da hankali zaka gabacesu.

  Misalign wadannan mutane masu hankali ma’abota lura da basira hakika soyayyarsu da kiyayyarsu  suna damfare da lafiyayyen hankali suna kewayawa tareda shi da dukkanin martabobinsa  da ma’anoninsa.

  Na hudu zuciyar irfani(masaniyar ubangiji): lalle tushen soyayyar arifi  masanin Allah  shine yardar Allah matsarkaki ma’ana yana soyayya da kiyayya saboda Allah, lalle mutane sun kasu kashi uku cikin karkatarsu ta zuciya kamar yada kan wannan ne suaratu bakara tayi ishara cikin fadinsa madaukaki:   

  -1(فَمِنَ النَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا وَمَا لَهُ فِي الآخِرَةِ مِنْ خَلاَقٍ).

  Daga cikin mutane akwai maicewa ya ubangijina ka bamu a cikin duniya, shi wannan bai da rabo a lahira.

   

  2 ـ (وِمِنْهُم مَّن يَقُولُ رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الآخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ).

  Daga cikinsu akwai mai cewa ya ubangjinmu ka bamu kyakkyawa cikin duniya ka bamu kyakkyawa  cikin lahira  ka tsare daga azabar wuta.

  3 ـ (وَمِنَ النَّاسِ مَن يَشْرِي نَفْسَهُ ابْتِغَاء مَرْضَاتِ اللّهِ وَاللّهُ رَؤُوفٌ بِالْعِبَادِ).

  Daga mutane akwai mai sai da ransa domin neman yardar Allah  shi Allah mai tausayi ne ga bayi.

  Kashi na uku  suna daga cikin mutanen da suke sayar da ransu domin Allah matsarkaki , sai su samu kusantarsa saboda bayyanarwa  da kamewa ba tareda boye boye cikin lamarinsu ba har sai su kasance kamar da kamar m,isalin tattacccen daddada zuciyarshi ta kasance haramin Allah ar’ashinsa. Addu’a  ga ilimin Allah da sirrikansa, wata rana wani mutum yayi ta’addanci kan kambar hadimin sarkin muminai ali(as)  sai kambar yayi yunkurin yi rama irin abinda yayi masa sai iama ali(as) ya hana shi yace masa (idan kayi hakuri zaka samu yardar Allah ka kuma fusata shaidan) babu shakka duk wanda manufar ayyukansa ta kasance domin neman yaradar Allah babu makawa Allah zai katange shi ya shiryar da shi hanya abar yabawa.

  (يَهْدِي بِهِ اللّهُ مَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَهُ سُبُلَ السَّلاَمِ).

  Allah yana shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa hanyoyin aminci.

  Soyayya da kiyayya wani lokaci sune biiye da halakar shaidan, wani lokacin kuma son zuciya da ke yawan umarni da mummuna, a karo na uku kuma takan bin hankali lafiyayye karo na hudu kuma shine soyayya da kiyayya da ke biye da neman yardar Allah mai girma da daukaka.

  Ko dai yardar Fatima shugabar matan aljanna da fushinta domin ita wasu lokuta ta kan yarda wani lokacin kuma ta kanyi fushi da abinda Allah ke fushi da shi da yarda da dukkanin abinda Allah ke yarda shi, idan Allah ya yi fushi to ita ma Fatima take take yin fushi, domin ita Fatima dukkanin iradarta ta riga ta narke cikin iradar Allah a wannan lokaci sai ta zamanto fuskar Allah madubinsa sonsa da yardarsa da fushinsa sannan bai buya cewa ta hanyar fuska ake sanin kowanne abu kamar yadda ana sanin kowanne mutum daga fuskarsa a wannan ne zamu san cewa kadai dai ana sanin badini da sirri idan ansan zahiri da bayyana, ya zama dole ya kasance ka san mutum ta fuskarsa.

  Hadisi ya zo daga littafin uyunu akbarul rida  daga majibancin lamarinmu imam rida(as)  yana cewa:   

  «من قال لا إله إلاّ الله أعطى له ثواب من ينظر إلى وجه الله، فقيل يا ابن رسول الله : فما معنى ذلك؟ قال  ×: وجه الله الأنبياء ورسل الله» فالنظر اليهم من النظر إلى وجه الله سبحانه. وفي الحديث عن عيسى بن مريم لـمّا سأله الحواريّون: يا روح الله من نعاشر؟ قال: «من يذكّر كم الله رؤيته».

  Duk wanda yace: babu abun bautawa da gaskiya sai Allah* Allah zai bashi ladan wanda ya kalli fusakar Allah, sai aka tambaye shi ya dan manzon Allah(s.a.w) menene ma’anar hakan? Sai yace: ma’ana fuskar annabawa da manzanni, lalle kallonsu yana daga cikin kallon fuskar Allah matsarkaki. Yazo cikin wani hadisi daga isa (as) lokacinda hawariyawa suka tambaye shi suka ce masa ya ruhin Allah da wane mutum zamuyi mu’amala sai yace musu: wanda ganinsa zai tunatar da ku Allah.

  Lalle bawa yana samun kusanci zuwa ga Allah da yin nafilfili  har Allah ya so shi sai Allah ya zamanto jinsa ganinsa, kamar yadda yake kusantarsa ta hanyar sauke sallolin wajibi sai bawa ya zamanto jin Allah da ganinsa wannan shine abinda arifan gidan ahlul baiti  suke kira da (mukamin kusanci da farillai) kamar yadda suka kira na farko da (mukamin kusanci da nafilfili) majibanciyar lamarinmu  mahaifiyarmu Fatima fuskar Allah ce da kyawunsa, lalle shahidi yana kallon fuskar Allah hakama `yan aljanna  suma suna kallon fuskar Allah ludufinsa bai buya ba.

  Ya zo cikin hadisin annabi mai daraja manzon Allah(s.a.w) yace: ya salmanu duk wanda ya so diyata Fatima lalle yana cikin aljanna tareda ni, duk wanda ya ki ta yana cikin wuta. Misalin wannan soyayya da kiyayya sune biye da son Allah da kinsa, kadai dai hakan na nuni da isma ta zati  ko ta aiki, lalle Allah yana son biyayya yana kin sabo  duk wanda ya so abinda Allah yake so babu shakka zai kasance mai biyayya bamai sabo, wannan na daga cikin isma ta kamewa daga sabo, girma iya girma  cikin Fatima shi ne kasantuwar ta zarce mukamin ma’asumanci  domin ita Allah yana yarda da yardarta yana fushi da fushinta wannan  ya kasance ta hanyar samuwarta ta malakutiyya, kamar yadda yardarta ga yardar Allah na daga sirri daga sirrikan Allah babu masu tsinkayarsa sai masu zurfafawa cikin ilimin gidan manzon Allah (s.a.w) da iyalansa tsarkaka, salmanu ya samu babban matsayi ta yadda annabi yake ce masa salmanu daga garemu yake ahlul baiti(as) sannan daga cikin tabbatun abubuwa  cikin akidarmu ta gaskiya cewa Allah madaukaki  wanda ke aikata abinda yake so  a hannunsa komai yake  cikin duniyar al’amari da halitta idan ya so al’amari take yake ce masa kasance sai ya kasance, lalle shi ya halicci sammai  cikin kwanaki shida, na farko daga duniyar al’amari  na biyu daga duniyar halitta. Ma’sumai muhammadu da iyalansa(as)  kadai dai sune tsani da gada zuwa ga rahamar Allah mayalwaciya da izininsa  matsarkaki domin kwararar fairar Allah mafi tsarkaka , lalle su imamai Allah ya basu iko kan wilayarsa ta takwiniyya wadda take basu ikon tasarrufi cikin duniyar halittu da izinin ubangijinsu, ya zama dole a wannan lokaci mu sansu ko suwaye mu san matsayinsu madaukaki da abinda ke bayansa daga sirrrika, kamar yadda arzikin duniya da lahira na tabbatuwa cikin riko da wilayarsu da aiki da tafarkinsu madaidaici da sanin gaskiaya da banbance ta daga karya, lalle Allah ranar kiyama zai tambayi bayinsa kan wilayarsu         

  (وَقِفُوهُمْ إِنَّهُم مَّسْئُولُونَ)

  Ku dakatar da su lalle su ababen tambaye ne.

  Babu shakka da kokwanto cikin kasantuwar yardarsu yardar Allah ce fushinsa fushinsu, biyayyarsu biyayyar Allah ce saba musu saba masa, lalle su suna samun wani matsayi madaukaki na tushe da sasi ciin tsarin Zubin tsarin duniyar halittu. Majibanciyar lamarinmu Fatima `yar manzon Allah(s.a.w) muhamadu musdafa, kuma matar aliyu almurtada mahaifiyar imamai zababbu iatace kadai da manzon Allah(s.a.w) kan sha’aninta ke cewa: lalle Allah yana yarda da yardarta yana fushi da fushinta.

  Wannan hadisi tareda ma’anarsa mai girma yana shiryar damu zuwa ga matsayin zahara wanda ya shallake matsayin ma’asumanci, lalle iatace mafi girman isma.

  Karshen maganarmu muna godiya ga Allah ubangijin talikai